Zayyana

     Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Bara da wasu waÆ™oÆ™in bara a Æ™asar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    Zayyana

    Wannan salo shi ne wanda mawaƙi kan tsaro bayanin faruwar wani ko yadda zai faru a cikin waƙa ta har yadda mai saurare zai ji kamar ga abin nan a gabansa yana faruwa. Wato bayanin da mawaƙin ya yi ya sa idanun zuciyar mai saurare na ganin yadda abin ke gudana. Misali:

     Almajiri tsuntsu ne,

     Da ya ji motsin tsaba,

     Sai ya yi hiringi da kunne,

     Kama da mataccen kusu,

     (Almajiri Tsuntsu ne)

    Duk lokacin da mai sauraro ya ji wannan ɗa , a daidai waɗannan layuka na uku da na huɗu sai ya ji kamar yana ganin yadda almajirin ya sifantu da wannan sifa sakamakon motsin tsaba da ya ji. Zayyana masa hiringi da kunne da dubin yadda kunnen mataccen kusu yake zama ƙyam ba motsaawa shi ke sa ya ji kamar yana ganin abin da ke faruwa ga almajirin. Sai ya gani a ransa kamar ga wani tsuntsu nan an watsa tsaba shi kuma ya kashe kunnensa ko dai don nufinsa na ya samu abincin da ya daɗe yana nema ko kuma don ya fake ne kar a gane shi yana cin tsabar a kore shi, sai wannan kashe kunne da ya yi ta mayar da shi kama da mataccen kusu (ɓera).

    A wani misalin ana cewa:

    Jagora : Annabi ya hito da haske da kyawo,

     Amshi : To

     Jagora : Kowa ya gane shi ya É—ora murna,

     Amshi : To

     Jagora : Ke ko kin gane shi kin É—ora kuka,

     Amshi : To

     Jagora : Ba kukan rashin É—iya niy da shi ba,

     Amshi : To

     Jagora : Don Æ™amnar Rasulu Manzo fiyayye,

     Amshi : To

    (Yabon Annabi)

    A cikin waÉ—annan É—iyan waÆ™ar da na kawo a sama, akwai hoto a cikin bayani wanda shi ake kira zayyana, domin mai saurare waÆ™ar kan iya riya yadda Annabi kuma ya gani a zuciyarsa irin hasken da aka ce ya siffantu da shi. Zai iya ganin sa a zuci a matsayin mai cikakken kyau wadda kowa da komai ke murnar gani a lokacin da ya fito. Sai aka kawo wata kaza tana kuka ga kuma wani mutum yana tambayar ta dalilin É“acin ranta bayan kowa na cikin murnar ganin Annabi. Daga Æ™arshe sai ta nuna cewa son Annabin ne ya sa ta kuka ba wai don ‘ya’yanta da shaho ya cinye ba.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.