Zubairun Mailalle

    Citation: BunguÉ—u, U.H. (2022). WaÆ™oÆ™in Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Amali  Sububu

    Zubairun Mailalle

    Zubairu na garin Mailalle manomi ne sosai, garin Mailalle yana can yamma ga Sabonbirni ta jihar Sakkwato. Amali ya yi masa waƙa shi ma saboda shahararsa ga noma.

     

    G/Waƙa : Na taho in buga[1] mai ƙwarya,

      : Zubairu manyan manoman gero.

     

         Jagora: Na taho in buga mai Æ™warya,

      : Zubairu manyan manoman gero.

    ‘Y/Amshi: Na taho in buga mai Æ™warya,

      : Zubairu manyan manoman gero.

     

         Jagora: Ni mai lalle can za ni in kwan,

    ‘Y/Amshi: Tun da Zubairu an ce yana nema na.

     

         Jagora: Ni Mailalle can za ni in kwana,

    ‘Y/Amshi: Tun da Zubairu an ce yana nema na.

     

         Jagora: Tun da Zubairu an ce yana nema na.

    ‘Y/Amshi: Tun da Zubairu an ce yana nema na.

      : Na taho in buga mai Æ™warya,

      : Zubairu manyan manoman gero.

     

         Jagora: In mutum ya ji kainai,

      : Lalle in mutum ya ji kainai,

      : Yat tara geron dakawa,

      : Gami da kuÉ—É—in kashewa,

      : Yat tara mata na wari[2],

      : Yanzu kiÉ—inmu shi za shi Æ™auna,

      : In dai ba kare za shi wa wanka ba.

    ‘Y/Amshi: In dai ba kare za shi wa wanka ba.

      : Na taho in buga mai Æ™warya,

      : Zubairu manyan manoman gero.

     

    Jagora: Jatau in mutum ya ji kai nai[3],

      : Yat tara geron dakawa,

    : Yat tara kuÉ—É—in kashewa,

      : Yas sami mata na wari,

      : Yanzu kiÉ—inmu shi za shi Æ™auna,

      : In dai ba kare za a wa wanka ba.

    ‘Y/Amshi: In dai ba kare za ya wa wanka ba[4].

    : Na taho in buga mai ƙwarya,

      : Zubairu manyan manoman gero.

         Jagora: Na leÆ™a Æ™asat Kwantagora,

      : Can ma na ga manyan manoma.

    ‘Y/Amshi: Amma ba su aikin mutanen farko.

     

         Jagora: Na leÆ™a ta sashen Ilori,

      : Can ma na ga manyan manoma,

    ‘Y/Amshi: Amma ba su aikin manoman farko.

     

         Jagora: Na leÆ™a Æ™asat Kwantagora,

      : Can ma na ga manyan manoma.

    ‘Y/Amshi: Amma ba su aikin mutanen farko.

     

         Jagora: Jatau in mutum ya ji kai nai,

      : Yat tara geron dakawa,

    : Yas sami kuÉ—É—in kashewa,

      : Yat tara mata na wari,

      : Yanzu kiÉ—inmu shi za shi Æ™auna,

      : In dai ba kare za a wa wanka ba.

    ‘Y/Amshi: In dai ba kare za ya wa wanka ba.

    : Na taho in buga mai ƙwarya,

      : Zubairu manyan manoman gero.

     

    Jagora: Na leƙa ƙasat Kwantagora,

      : Can ma na ga manyan manoma.

    ‘Y/Amshi: Amma ba su aikin mutanen Hausa[5].

     

         Jagora: Na leÆ™a ta sashen Ilori,

      : Can ma na ga manyan manoma.

    ‘Y/Amshi: Amma basu aikin manoman Hausa.

     

    Jagora: Na leƙa ta sashen Ibadun,

      : Can ma na ga manyan manoman gero.

    ‘Y/Amshi: Amma ba su aikin mutanen Hausa.

     

         Jagora: Na leÆ™a ta sashen Ilori,

      : Can ma na ga manyan manoma.

    ‘Y/Amshi: Amma basu aikin manoman Hausa.

     

    Jagora: Na yi Kano da waƙa da yara,

      : Can ma na ga manyan mutanena.

    ‘Y/Amshi: Amma ba su aikin mutanen Hausa.

     

         Jagora: Birnin Bauchi na kwana roÆ™o,

      : Can ma na ga manyan manoma.

    ‘Y/Amshi: Amma ba su aikin mutanen Hausa.

     

    Jagora: Na Gwambe na kwana wasa,

      : Can ma na ga manyan manoma.

    ‘Y/Amshi: Amma ba su aikin manoman Hausa.

     

         Jagora: Na je Borno na kwana wasa,

      : Can ma na ga manyan mazaizai[6].

    ‘Y/Amshi: Amma ba su aikin mutanen Hausa.

     

         Jagora: Na Koma ta sashen Arewa,

      : Can ma na ga manyan manoma.

    ‘Y/Amshi: Amma ba su aikin manoman Hausa.

     

    Jagora: Lalle ba su aikin manoman Hausa,

    ‘Y/Amshi: Lalle  ba su aikin mutanen Hausa.

     

         Jagora: Na Rabi da Rabi manyan manoman Hausa,

    ‘Y/Amshi: Na Rabi da Rabi manyan manoman Hausa,

     

         Jagora: Na Abu da Abu manyan mazaizan Hausa

    ‘Y/Amshi: Na Abu da Abu manyan mazaizan Hausa,

    : Sarkin daji sai in yaba mai hwama.

        

         Jagora: Ka ban zawara ‘yag garin ga,

    ‘Y/Amshi: Sarkin daji Mamman shina ban kwana.

      : Na taho in buga mai Æ™warya,

      : Zubairu manyan manoman gero.

     

         Jagora: Amali kiÉ—inmu sai mai iyawa,

      : KiÉ—inmu sai mai na kai nai,

      : KiÉ—inmu sai mai riÆ™onmu,

      : Ba ni matce ma Æ™ato yanai man Æ™arya.

    ‘Y/Amshi: Ba ni matce ma Æ™ato yanai man Æ™arya,

      : Na taho in buga mai Æ™warya,

      : Zubairu manyan manoman gero.

     

         Jagora: Ba ni matce ma Æ™ato yana É—angwanno[7],

    ‘Y/Amshi: Ba ni matce ma Æ™ato yanai man Æ™arya,

      : Na taho in buga mai Æ™warya,

      : Zubairu manyan manoman gero.

     

         Jagora: Na taho in buga mai Æ™warya,

      : Zubairu manyan manoman gero.

    ‘Y/Amshi: Na taho in buga mai Æ™warya,

      : Zubairu manyan manoman gero.

     

         Jagora: Birnin Mailalle can za ni wasa,

    ‘Y/Amshi: Tunda Zubairu an ce yana nema na.

      : Na taho in buga mai Æ™warya,

      : Zubairu manyan manoman gero.

     

         Jagora: Na taho in buga mai Æ™warya,

      : Zubairu manyan manoman gero.



    [1]  KiÉ—a.

    [2]  Sa’a/ ‘yan shekara ko Æ™arfi ko tashi É—aya.

    [3] In mutum ya isa.

    [4]  Aikin banza.

    [5]  Ƙasar Sakkwato.

    [6]  Mazaje/manoma/gwaraza

    [7]  Sata Musamman ta hatsi/Ƙwalto/ kala.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.