A Wacce Rana Aka Haifi Annabi Saw?

    TAMBAYA (28)

    MAlam tambayata biyu ce daya privet daya public. Bayani nakeso kaimana a kan ranar da aka haifi fiyayyan halitta ankoyan asiri ranar litinin amman yanxu dana lissafa sainaga zaikama laraba Kuma meyadace ayi ranar

    AMSA

    Musulmai dayawa suna kafa hujjar haihuwar Annabi Muhammad SAW a ranar 12 ga watan Rabi'ul Awwal wanda yayi daidai da 570CE wasu kuma sunce 13 ne wasu ma 15 sukace saidai babu wani sahihin hadisi da ya tabbatarda hakan a gaba daya cikin kutubus sittah (Bukhari, Muslim, Abu Dawud, Imam at-Tirmidhi, Imam an-Nasa'i da Ibn Majah)

    To amman mafi qaulin rinjaye shi ne an haifeshi ne a ranar litinin saboda shi da kansa ya fada a lokacinda sahabbai suka tambayeshi dalilin dayasa yake azumtar ranar ta litinin

    (Jami'i at-Tirmidhi littafi na 9 lambata 101)

    Shi kuma azumin Alhamis yana yin sa ne SAW saboda a ranar ne ake tattara ayyukan bayi a kaiwa Allah SWT

    An karbo daga Abu Hurairah, Ibn Abbas, Nana Aisha da Abdurrahman Ibn Abi Bakrah (RA), Annabi SAW ya ce "Tabbas, ayyukan bayi ana bijirar dasu ga Allah SWT a ranar litinin da alhamis, nafison a bijiro da ayyukana yayinda nake azumi"

    (Sunan Ibn Majah littafi na 10 lambata 1656)

    Waɗanda suka inganta Hadisin sun hada da Ibn Hajar al-Asqalani, Imam ad-Dhahabi, al-Hafiz Ibn Khathir (Allah yayi musu rahama baki daya)

    A tarihance abinda ya tabbata shi ne: Annabi SAW ya koma ga Allah ne a ranar litinin 12 ga watan Rabi' al-Awwal, 11 AH wanda yayi daidai da 8 ga watan June, 632 CE. Ya rasu ne bayan yan watanni kalilan da yin hajjin bankwana (Hajj al-Wada') a lokacin yana shekaru 63

    Bayan rasuwarsa kuma sai aka nada Sayyadina Abubakar RTA a matsayin khalifa wanda duk son da yakewa Annabi SAW amman ba a taba rawaitowa cewar yayi maulidin Annabi SAW ba. Sauran khalifofin ma duk basuyi ba. Hakama Nana Aisha RTA, saida tayi shekaru 48 bayan wafatin Ma'aiki SAW alhalin bata auri kowa ba saboda son kasancewar daya daga cikin matan Annabi a cikin Aljannah to amman dukda wannan soyayya ba'a taba cewa Nana Aisha RTA tayi maulidi ga Manzon Allah SAW ba

    A shawarce bai kamata Musulmai su dinga daga jijiyar wuya a kan wannan sabanin ba

    Wasu ma musu a kan wannan mas'alar kan kaisu ga tsananin gabar da zata rusa alaqar mu'amalarsu wanda harma hakan yake shafar addininsu wanda anan shaidan yayi nasara kam. Don haka a shawarce kuma a sunnance an so musulmi ko musulma suyi koyi da sunnar da Ma'aiki SAW yake a wannan ranar da aka haifeshi wato azumtar ranar. Wannan ita ce sunnah Mu'akkhada da ya kamata mu Dabbaqa a maimakon tuno haihuwarsa duk bayan kwanaki 360 wanda Sahabbai, Tabi'ai da Tabi'uttabi'un basu taba hakan ba. Har yanzu banga hujjar da akace sunyi Maulidi ba haka kuma ko a Akhdari, Ishmawy, Iziyya, Risala babu wani babi na Maulidin Annabi SAW

    Bai kamata a muyi kwaikwayo da nasara ba wanda suke murnar haihuwar Annabi Isah A.S a kowacce shekara, ranar 25 na kowanne watan December wanda shima din bai ingantaba kamar yanda binciken malaman tarihi ya tabbatarda hakan. Wannan yana daya daga cikin dalilan da yasa Annabi SAW ya ce kada ku dinga kaini matsayin da ban kai ba kamar yanda mutanen Dan Maryam (Isah AS) suke allantardashi. Ku kirani Abdallah kuma Rasulullah. Kamar Annabi SAW ya san hakan zata faru la'akarida yanda zakaga a wajen maulidin ana kai shi matsayin Allah SWT wasuma suna cewa yana halartar wajen maulidin. Wanda da zai bayyana a zahiri to da tun a lokacin sahabbai ya bayyana ya sasanta rigimar cikin gida da ta wakana tsakanin Sayyadina Aliyu RA da Mu'awiya RA a lokacin khilafa. To amman Idan Allah SWT ya fahimtarda mutum addini to ya huta kam. Kamar yanda hadisin Ibn Majah ya tabbatarda hakan

    (Ibn Majah littafina 3 lambata 3606)

    Muna roqon Allah SWT ya rabamu da qirqiro bidi'ah, domin kuwa dukkan bidi'ah batace kuma dukkan bata zai kai mutum zuwa wutane. Wannan hadisine wanda Abu Hazim (Muhammad bin Hazim) ya rawaito daga Abu Hurairah shi kuma yaji daga bakin Ma'aiki SAW

    (Musnad Imam Ahmad hadisi mai lambata 219). Dukda dai malamai sunce da'ifin hadisi ne saboda raunin Abu Hazim a bangaren ruwaya amman ma'anar hadisin (matn) haka yake saboda hadisai mutawatirai sun tabbatarda Annabi SAW yana cewa "Dukkan bidi'ah batace dukkan bata zaikai mutum zuwa wuta" a kowacce Khutbatul Haja da zaiyi

    Amman tabbas mutum ya qwaqwule gini da yan yatsunsa shi ne yafi sauqi a kan son zuciyarsa domin kuwa muma mun taba maulidi a dacan kafin musan matsayinsa a addini

    Abinda ya dace ayi shi ne abinda Annabi SAW yakeyi wato azumtar ranar haihuwarsa. Shin munayi ?

    Wallahu ta'ala a'alam

    Amsawa:

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

    Questions And Answers According To Qur'an And Sunnah. Join Us...

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RQbbrzgW

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.