Abajada

    Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin WaÆ™aƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

    About Tahamisin WaÆ™aƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

    Abajada

    15. Gun harshe a yo rubutu tilas ne,

     A sanin Æ™a’idarsa kana farilla ne,

     Shi ko aro a raya harshe tsari ne,

     Hausa Æ™idan baÆ™inta a, b, c, d, ne,

      Haka nan ta aro shi can gun Turawa.

     

    16. Zan fara da sa baƙaƙe a kula su,

     A kiyaye su bi-da-bi kan tsarinsu,

     Akwai Æ™i-jima [1]ka ga nan ga tsarinsu,

     Su aka ce wa sauÆ™aÆ™a sai ka biya su,

    Su duka goma sha bakwai babu daÉ—awa.

     

    17. Sa mini /b/ da /c/ da /d/ ga /f/ ga /g/,

     Lissafin baÆ™i biyar ke nan har /g/,

     In ka lura tun da /b/ ya zuwa /g/,

     Æ˜ara kula yanzu bayan sautin /g/,

    Ga mu da /h/ da /k/ da /l/ /j/ ka biyowa.

     

    18. In ka lura ka gwane kan bitarsu,

     Sauti tara ne ka Æ™ara duba jimillarsu,

     /M/ na nan da /n/ da /r/, /s/ ke bin su,

     Nan Æ™asa ga waÉ—ansu sa su a jerinsu,

    /T/, /w/, /y/, da /z/ ga ƙarshen ƙirgawa.

     

    19. In ka lisafa su sun kammala daidai,

     SaÉ“anin hakan ga sai dai in ko dai,

     An yi kure na kama lisafin daidai,

     In ka gane su ka wucce Allah waddai,

    Sun zama sha bakwai baƙaƙen Hausawa.



    [1] Baƙaƙe ƙi-jima su ne baƙaƙen da suka kasance tilo kamar /b/ da /c/ da makamantansu, wato koma bayan masu goyo kamar /kw/ da /gy/ da makamantansu.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.