𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Ƙabarin
da aka haka sai aka ga ya cika da ruwa. Sai da aka kwashe ruwan sannan aka iya
kwantar da mamacin. To wai wannan alamar Rahama ce?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa
Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
Malamai sun bibiyi Hadisai Sahihai sun gano
alamomin da suke nuna kyakkyawan cikawa ga musulmi kamar haka:
1. Furuci da Kalmar Shahada a lokacin mutuwa.
2. Mutuwa da zufan goshi.
3. Mutuwa a daren Jumma’a ko yinin Jumma’a.
4. Mutuwar shahada a filin daga na yaƙin
Musulunci.
5. Mutuwa a kan hanyar Allaah.
6. Mutuwa a cikin annoba.
7. Mutuwa saboda ciwon ciki.
8. Mutuwa ta nutsewa a cikin ruwa.
9. Mutuwa a cikin rushewar gini.
10. Mutuwa a cikin gobara.
11. Mutuwa saboda cutar ‘bulala’.
12. Mutuwa a cikin naƙuda.
13. Wanda aka kashe shi yana kare dukiyarsa.
14. Wanda aka kashe shi yana kare iyalinsa.
15. Wanda aka kashe shi yana kare addininsa.
16. Wanda aka kashe shi yana yare kansa.
17. Wanda aka kashe shi yana hana mai zaluntarsa.
18. Mutuwa da cutar tarin huka.
19. Mutuwa
a halin yana yin gadin garin musulmi.
20. Mutuwa a kan wani aiki na-gari.
21. Yabon mutanen kirki gare shi a bayan
mutuwarsa.
(Ahkaamul
Janaa’iz, shafi: 287-298 na Al-Qahtaaniy).
Kamar yadda muka gani, duk a ciki waɗannan bai ambaci maganar yanayin ƙabarin
da za a saka mamacin a cikinsa ba, kamar cewa ƙasar mai taushi ce, ko
kuwa an samu ɓullowar
idon ruwa a cikinsa, ko kuwa tsirowar wata ciyawa ko tsiri ko dai wata fulawa
da sauransu.
A taƙaice dai, a iyakan ɗan abin da na sani, samun ɓullar idon ruwa a cikin ƙabari
ba shi daga cikin alamomin samun Rahama ga mamaci. Duk kuwa da kasancewar
mutane sun daɗe suna
ambaton haka.
As-Shaikh Ibn Baaz (Rahimahul Laah) ya amsa wata
fatawa a kan tsirowar itaciya a kan ƙabari: Ko wannan yana nuna wata daraja ko
matsayi na mamacin ne? Sai ya nuna cewa: Tsirowar bishiya ko ciyawa a kan ƙabari
ba ya nuna salaha ko nagartar mamaci. Zaton hakan kuma zaton banza ne kawai,
domin sanannen abu ne cewa ciyayi da bishiyoyi suna tsirowa a ƙabarin
mutumin kirki da mutumin banza ma. (Fataawaa Al-Muhimmah, shafi: 443 na
As-Shaikh Al-Imaam Ibn Baaz).
Allaah ya shiryar da mu.
WALLAHU
A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.