Abubuwa 7 Da Ya Kamata A Ce Kana Yi In Ka Hau Yanar Gizo

Intanet da dandalolin sada zumunta ko soshal midiya a Turance wasu ƙafofi ne dake bawa kowa namiji ko mace yaro ko babba ƙungiya ko ɗaiɗaikun mutane, cibiyoyi ko majalisu kai har gwamnatoci da ƙasashe dabandaban a faɗin duniya damar furta albarkacin bakinsu a kan komai kuma a kan kowa.

Waɗannan kafafe sun kasu kashikashi dangane da irin buƙata ko saƙon da mutum ko jama'a ke son isarwa ga al'umar duniya. Idan  jan hankali da nuna fahimta kake so akwai Facebook. In yaɗa labari ko tura bidiyo ne ya fi baka sha'awa to Whatsapp ne naka. Ga masu son sharholiya kuwa TikTok ne nasu.

Yaɗawa da kallon gajejjerun bidiyo na tsakure don nishaɗi a nemi Instagram. Baiyana ra'ayin ƙashin kai da na ƙungiyoyi da gwamnatoci a takaice wato a sigar kanun labarai Twitter ce inda kowa ke baje kolinsa. In kuma aka ce za a kalli bidiyo ne na tsawon lokaci to mai sha'awar yin hakan ya je YouTube.

Akwai tarin wasu shafuka kalakala da suke biyawa ma'abota hawa yanar gizo da dama bukatarsu. Abin dai ya danganci me suke so. To, koma dai mene ne burin masu ziyartar kafofi da dandalolin a yanar gizo ya kamata mutum ya san cewa akwai abubuwa guda 7 da ya kamace shi yi don gudun tafka mummunar asara.

Tabbas asara ma babba kuwa, in dai a matsayinka na Musulmi, ɗan Arewa, Bahaushe, Mai Ilimi (Boko da Islama), Mai hankali da son ci gaban al'umarka da dai sauransu in baka tabbatar da cimma waɗannan manufofi har guda bakwai ba a duk sanda ka samu kanka ko kika samu kanki a duniyar intanet to a gaskiya da sake. Shin waɗanne ne abubuwa 7 nan?

Ga su kamar haka:

1. Neman Lada

Saboda rayuwar duniya cin kasuwa ce kuma ribarta ita ce mutum ya yi ajiya don maganin wata rana, sannan tunda lokaci wucewa yake yi ala ayya halin to ya kamata kowa ya yi la'akari da cewa duk aiyukansa/ta a doron ƙasa wata tijara ce. Sakamakon hakan zai yi masa/mata tasiri ne a rana gobe kiyama. Don haka hankali shi ne mutum ya shuka alkhairi.

2. Nemi Ilimi

Kasance ɗalibi a jami'ar 6oye wato dandalin intanet ta yadda za ka zama ko da yaushe a cikin shiri na ɗaukar dukiyarka (ilimi) da ta 6ata duk inda ka tsince ta kamar yadda Annabi SAWS ya sanar da mu. Akwai tulinsa kuwa duk inda ma'abocin hawowa ya kurɗa a yanar gizo. Yayin da kake karance-karance to kasance mai ɗiban ilimi.

3. Kiyayi Neman Suna

Yaro bari murnan karenka ya kama zaki in ji masu iya magana. Sau da yawa wasu na hawa intanet ne don yaɗa manufa don kuma a sansu a san harkarsu. Sai dai a ƙoƙarin ɗabbaƙa wannan manufa tasu akwai waɗanda suke yin abubuwan da ba shike nan ba don kawai su yi suna kuma sunan da tashen ya ɗore har ta kai su kunyata su kuma tafka gagarumar asara.

4. Kasance Bishiya

Duk sanda ka tsinci kanka a wani dandalin sada zumunta to ku ɗauki kanku tamkar wata bishiya ce mai ganye kore shar ga inuwa ga y'ay'a nunannu ga magani ga ƙaruwa a tattare da komai nata tun daga ganyenta har saiwarta. Bi ma'ana ku zama masu amfanar da al'uma daga alkhairin da Allaah SWT Ya baku na sani fahimta da zurfafa tunani.

5. Jakada Nagari

Ka zama mai amfani da damar da ka samu na faɗa duniya ta ji wajen kare addininka (Islam), al'umarka, 6angarenka (Arewa), ƙwatar y'ancinka, koyar da dabi'u da halaye nagari, jan hankalin mutane don sanin abubuwan ci gaba da inda duniya ta sa gaba. Don akwai buƙatar ka koyi salon rubutu irin na duniyar midiyar yanar gizo saboda cimma waɗannan buruka.

6. Gina Kai/Ɗaukaka Darajar Kai

Kowa ya sani cewa yanzu fa manya-manyan kamfanoni na duniya da masana'antu da ma wasu hamshaƙan masu kuɗi sun daina damuwa da sakamakon karatun mutum na Jami'a. Buƙatarsu kawai me ka iya me za ka iya yi? Maimakon su kalli satifiket ɗinka na'ura za a ba ka a ce ka sarrafa wani ƙalubale a gani.

In ka iya ba ka da matsala in kuwa aka samu akasi duk karatunka to fa da sauranka. Shi yasa matasa masu wayo a cikinmu suke hawa yanar gizo su shiga koyon ilimin yin aiyukan zamani iri-iri daga jami'o'i dake ƙasashe dabandaban ta hanyar amfani da kwamfuyuta ko wayar hannunsu su kuma samu shaidar kammala karatun. Amma kai fa?

7. Neman Kuɗin Shiga

Sai na ƙarshe - Sana'o'i, aiyuka, ƙodago da ire-irensu da yawa da aka sani a da kuma ake amfani da su wajen samun kuɗin shiga duk sun soma sauyawa. Wasu sun kau sabbi sun wanzu. Aiki yanzu ba lallai ba ne a ce kullum sai ka fita da safe ka dawo da yamma da sunan wai ka tafi aiki ba. Namiji ko mace yanzu kowa zai iya yin aikinsa kai tsaye daga gida daga ɗakinsa.

Saboda samuwar fasahar sadarwa ta yanar gizo yanzu da yawa ana samun aiki yi daga ko'ina a duniya ba sai ɗan ƙasa ko jiha ko ɗan ƙaramar hukumar mutum ba. A kuma biya mutum albashi a kowace rana, duk sati ko duk wata. Kuɗin kuma su shigo asusun ma'aikacin ta sigar kashles! Ba kuma a nau'in Naira ba a'a da kuɗin kasashen waje wato dalar Amurka $$$.

Abin yi kawai don samun tabbatar da kasancewar hakan shi ne al'umarmu musamman matasanmu mazansu da matansu su san abubuwan da ake buƙata don gudanar da wannan harkar wanda sanin makaman aiki yana daga ciki. Dole ne mu tashi tsaye wajen wayewa da wayar da kan al'umarmu mu zurfafa bincike mu nemi hanyar da ake bi a yi.

Shi ya sa yanzu sai ka ji ana tambayar "Wai me wane to wacce suke yi ne? Kullum suna gida a ɗakunansu amma ba sa rabo da kuɗin kashewa?" To ku sani ba fa y'an Yahoo Yahoo ba ne kuma ba 419 suke yi ba. A'a wani sabon salon yin aiki ne da zamani ya zo da shi inda za kanyi amfani da wayar hannunka e ita ɗin dai da da yawa suke shirmensu da ita.

Kun ga yanzu mutum zai iya kasancewa yana ɗan Kano kuma mazaunin Kano nan amma ya zama ma'aikacin Google, Amazon, Apple, Facebook da dai makamantansu in har ya iya allonsa. Kuma ba ta ko'ina zai samu wannan matsayin ba illa ta sanin yadda zai yi amfani da wayarsa da e-mail da e-payment da e-learning.

Muhimmiyar tambaya anan ita ce: Shin me kake yi da wayarka in ka hau yanar gizo? In dai ba abubuwa bakwan nan da na lissafo kake yi da ita ba to a gaskiya sharholiya kawai kake yi kuma 6ata lokacinka da asara kuɗin sayan data kawai kake yi. E gayawa kowa ka ce inji ni Tijjani Muhammad Musa... 😆

Abubuwa 7 Da Ya Kamata A Ce Kana Yi In Ka Hau Yanar Gizo

Post a Comment

0 Comments