𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Malam, wata
matsala ce ta sha min kai: Ko yana yiwuwa kuɗaɗe su riƙa ɓacewa a cikin gida ba tare da wani mutum ya ɗauke su ba?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa
Barakaatuh.
Masana sun ce zai iya yiwuwa kaya ko kuɗi su riƙa ɓacewa a inda mutane suka ajiye su, ko da
wani daga cikinsu bai ɗauka
ba. Domin ai ba mutane ne kaɗai
suke rayuwa a duniyar nan ba. Akwai aljanu mutanen ɓoye waɗanda suke ganinmu ta inda mu ba mu ganin
su.
Idan dai har sheɗanin aljani zai iya shiga masallacin
Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a cikin surar wani tsoho kuma
har ya riƙa ƙoƙarin sace kayan abincin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)
ya bai wa Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu) a matsayin gadi, to a wane wuri ne
a cikin gida za a ce sauran danginsa ba za su iya shiga, su ɗebo kaya ko kuɗaɗe ba.
Maganin irin wannan dai in shã Allahu shi ne a riƙa
ajiye kaya da kuɗaɗe a ɓoyayyen wuri tare da faɗin Bismillaah a lokacin ajiyewa da
kullewa. Domin Annanbi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya tabbatar da
cewa sheɗanu ba
sa buɗe ƙofar
da aka rufe da Bismillaah.
Sannan kafin a fara tunanin jingina batun satar ga
ɓoyayyun aljanu, a
tabbatar an tsananta bincike a cikin mutane tukun.
A dogara ga Allaah a yi istirjaa’i, a nemi sakayya
da samun musanye daga Allaah Ubangijin Halittu a lokacin da aka gano aukuwar
satar. Kar a tsananta wurin zargin wani mahaluki ba da cikakkiyar hujja ba, mai
kai wa ga aukuwar fitina. Galibi abin da sheɗanun aljanun suke neman aukuwarsa kenan a
tsakanin musulmi.
Allaah ya ƙara mana kariya.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.