𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Game da yarinyar da ba ta fara haila ba amma ta
fara kirgan-dangi, kuma da yaron da bai yi mafarki ba amma ya fara warin
hammata, shin za su rama azumin Ramadan da suka sha ko ba za su rama ba?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Masana sun ce: Alamun balaga a wurin yaro su ne:
1. Fitar maniyyi daga gare shi a cikin barci ko a
farke.
2. Tsirar gashi mai ƙarfi mai duhu a mararsa
da hammatarsa.
3. Fitowar gashin gemu da saje da gashin baki a
fuskarsa.
4. Buɗewar
muryarsa.
5. Bayyanar waɗansu ƙurajen pimples a
fuskarsa.
6. Samun warin jikinsa (warin balaga).
A wurin yarinya kuwa alamun su ne:
1. Samuwar jinin haila daga gare ta.
2. Bayyanar nono a ƙirjinta, wanda kuma yake
cigaba da girma kaɗan-kaɗan.
3. Tsirowar gashi mai ƙarfi mai duhu a
hammatarta da mararta.
4. Bayyanar waɗansu ƙurajen Pimples a
fuskarta.
5. Sauyi a cikin gashin kanta, ta yadda yakan ƙara
zama mani’imci
mai santsi da laushi.
6. Samuwar warin jiki (watau: Warin Balaga).
7. Ƙarin faɗin ƙugunta.
8. Fitar maniyyi a cikin barci ko a farke.
Don haka, duk wanda ya ga ɗaya daga cikin waɗannan alamomin sai ya kara kulawa da
addininsa sosai.
Kodayake wasu Malamai sun nuna cewa babbar alamar
balaga a wurin namiji ita ce fitar maniyyi, a wurin mace kuma fitar haila ce,
amma dai abu mafi-kyau shi ne su rama duk azumin Ramadan da suka sha kawai,
domin fita daga matsala a Lahira.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RQbbrzgW
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.