𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Malam, tambayata ita ce: Ina
aikin gwamnati ne sai mijina ya ce bai yarda ko ‘maggi’ in saya a gidansa ba.
In na saya kuma to, Allaah ya isa! Alhali kuwa ba ya bayar da kuɗin da zai isa. To, idan na saya na yi
laifi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.
Akwai sarƙaƙiya a cikin wannan tambayar:
Abu ne sananne cewa, mace ba ta da ikon fita daga
gidan mijinta zuwa aikin Gwamnati ko na wata Hukuma sai da izini kuma da yardar
mijinta. To, ta yaya kuma zai ce bai yarda ya yi amfani da wani abu komai ƙanƙantansa
da ta kawo a cikin gidansa ba?!
Sannan kuma ya ce wai: Bai yarda ta sayi wani abu
ta ƙara a cikin abincin gidansa ba, alhali kuma shi bai bayar da abin da zai
isa ba, wannan kuma wace irin doka ce haka?! Lallai kam akwai kwantanciyar
matsala a ɓoye a
nan.
Amma ko menene dai, abin da ya fi a irin wannan
halin sai kawai a nemi zama da waɗanda
suka ɗaura
auren da farko, domin a tattauna matsalar a cikin ruwan-sanyi da fahimta tare
da manufar yin sulhu a tsakaninsu. Wannan shi ne ya fi, in Shã Allãh.
Allaah ya ce:
وَإِنْ خِفْتُمْ شِقَاقَ بَيْنِهِمَا فَابْعَثُوا حَكَمًا مِنْ أَهْلِهِ وَحَكَمًا مِنْ أَهْلِهَا إِنْ يُرِيدَا إِصْلَاحًا يُوَفِّقِ اللَّهُ بَيْنَهُمَا إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلِيمًا خَبِيرًا
Kuma idan kuka ji tsoron aukuwar saɓani a tsakaninsu (ma’aurata) sai ku aika
da mai hukunci daga cikin danginta, da mai hukunci daga cikin danginta, idan
dai sulhu suke nufi, to Allaah kuwa zai datar a tsakaninsu, haƙiƙa
Allaah ya kasance masani ne, mai cikakken ilimi.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.