Basakkwaciya

    Ya ke Basakkwaciya!
    Saurari kalmomi daga zuciya.

    Don ke zan taka tun daga Zariya,
    In tsallake tekun Bahru Maliya.

    Duk wata soyayya in ba taki ba,
    Daidai ta ke da cin ganyen tumfafiya.

    Ke na ke hange a cikin idanuwa
    Ba ruwana da wata baturiya, ko Æ´ar Italiya.

    Kafin soyayyarki, zuciyata zindir ta ke,
    Sai kaunar ki ta lulluɓe ta da jallabiya.

    Ke ce tauraruwa ta tilo ƙwarai,
    A can faÉ—in sararin samaniya.

    A can cikin taskar mata masu tsada,
    Ke ce dai kaÉ—ai kyakyawar zinariya.

    Kar ku cece ni ko da kun ga zan nutse,
    Domin soyayyarki ita ce ambaliya.

    Kan ki ba batun Naira ko Fam na Ingila,
    Gare ki zan iya kashe miliyoyin gangaliya!

    Taka lafiya a sannu-sannu Sahibah.
    Dole in miki kirari ya ke Sarauniya

    Zan iya daina barci har abada,
    Don in dunga tashin ki sallar safiya.

    Dubin zubin nata na zuciya, sam ita babu hayaniya.
    Ko dan na samu salama dole na bi ki babu ƙiriniya.

    Aure da ke ba shi dan a kanki sai na yi mamaya.
    Kin kira ni, Jamil na Buthaina, fatana ki zame min halaliya

    Jiƙon ƙauna kin ba ni, to taya ya zan miki zamiya?
    DaÉ—i da ba daÉ—i mu zauna, in kin ji yunwa zan baki kunu na tsamiya

    Son ki ya shige zuciya ba sauran ƙafiyya
    Sai dai in yi addu'a Allah Ya ƙara miki lafiya

    Na san zaku murmushi wasu ko dariya
    Domin kun É—auka cewa ina ta hauragiya!

    Hauragiya na ga wanda bai san zaƙi,
    Da zafin da soyayya ke da shi ba a gaskiya.

    ©Potter

    26/09/2023.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.