𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalam Alaikun. Shin menene hukuncin maita a
musulunci naji ance babu maita se kanbun
baka. Kuma akwai hanyan da ake jinyan wannan matsala a musulunce? Domin wlh
wannan abu ya daure min kai. Sabida masu aikin jiyyan wadanda mayu suka kamasu
matsafa ne. Ko kuma dai nace bansan da me suke jinyan ba.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh
Da farko dai maita ba halitta bace, Tsafi ce.
Maita wani abune wanda yakeda alaƙa da bokanci da tsafi, domin abune musamman ake
zuwa ake samoshi a wajan bokaye wanda ake yin amfani da shi ana cutarda mutane
ana saka musu cuta ajikinsu ko wani nau'i na rashin lafiya, duk da cewa wasu
daga cikin malamai suna ganin cewa babu maita, amma zahirin gaskiya akwaita
kuma nau'ine na tsafi da bokanci.
Matsalar Kambun ido gaske ce ba Qarya ba. Domin
Manzon Allah ﷺ yayi
bayaninta Qarara acikin hadisai da dama. Har ma ya ce "BAYAN QADDARAR
ALLAH MAƊAUKAKIN SARKI, BABU ABIN DA YAFI HALLAKAR DA AL'UMMATA FIYE DA KAMBUN
IDO".
Kuma ya ce "DA ACE AKWAI ABIN DA KE RIGA
QADDARA AFKAWA KAN MUTUM, TO DA KAMBUN IDO YA RIGATA".
Abin da aka sani wanda mutane basa rabewa tsakanin
kambun baka da maita. shi kambun baka Allah yana halittar mutum dashi, wanda
shi kansa baisan ma yana da wannan halaittar ba, tayadda duk abunda suka kalla
idan basuyima wannan abun addu'a ba toh wani larura yana iya samun wannan abun
kamar idan yakalli wani mutum toh idan yanada kambun ido se kallon kawai ya iya
cutarda wannan mutumin. Inkuma kambun bakane toh idan ya yabi abu ba tareda
yayi addu'a ba toh hakan sekaga ya cutarda wancan mutumin.
Kambun ido idan ya afka ma mutum, ko guba (Poison)
bai fi shi saurin kisa ko lalata sha'anin mutum ba. Shi yasa da yawa zaka ga
mutane suna ta neman maganin karya sihiri, alhali basu san cewa kambun ido ne
ya afka musu ba.
Mai kambun ido zai iya yi maka akan dukiyarka ko
gidanka ko 'ya'yanka ko lafiyar jikinka, ko aikinka ko kasuwancinka, ko
muryarka, ko salon rubutunka, ko yanayin tafiyarka, ko kuma duk wani abu naka
wanda ya burgeshi, ko kuma ya jefa hassada acikin baqar zuciyarsa.
Kuma masu irin wannan cutar suna nan da yawa
acikin al'ummah. Watakila Akwaisu agidanku ko wajen aikinka, ko acikin abokanka
ko Ajin da kake karatu, etc. Sannan kuma akwaisu acikin Aljanu ma, wadanda ta
hanyar kallo suke iya cutar da mutum koda basu shiga jikinsa ba.
Yana daga cikin manyan hanyoyin Riga-kafi, mutum
ya yawaita addu'o'i da zikirorin safe da yamma da na kwanciya bacci da na shiga
gida da fitowa da sanya sutura da sauransu.
Ga wasu addu'o'i kariya daga dukkan sharri:
أَعُوْذُ بِكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّةِ مِنْ كُلِّ شَيْطَانٍ وَهَامَّةٍ وَمِنْ كُلِّ عَيْنٍ لاَمَّةٍ بِسْمِ اللَّهِ أَرْقِيكَ مِنْ كُلِّ شَيْءٍ يُؤْذِيكَ مِنْ شَرِّ كُلِّ نَفْسٍ أَوْ عَيْنِ حَاسِدٍ اللَّهُ يَشْفِيكَ بِسْمِ اللَّهِ أَرْقِيكَ بِسْمِ اللهِ لاَ يَضُرُّ مَعَ اسْمِهِ شَيْءٌ فِي اْلأَرْضِ وَلاَ فِي السَّمَاءِ وَهُوَ السَّمِيْعُ الْعَلِيْمُ
Idan kana
yawaita yin irin wadannan Addu'o'i, Allah zai tsareka, koda kuwa mai
maita da kambun baka ya aibantaka.
Allah ta'ala yasa mudace
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.