Ticker

Dalilin Da Yasa Ake Neman Ilimi

TAMBAYA (16)

Dan Allah inada tambaya akan ayar datake magana aakan dalilin dayasa ake neman ilimi aha ko hadisi ngd

AMSA:

Neman ilimi fardu ayn ne ba fardu kifaya ba bi ma'ana ya zama dolene wani daya daukewa wani, shiyasa ba'a gadon ilimi saidai mamaci ya tafi da abinshi. A takaicedai yakamata musa a ranmu cewar:

(طلب العلم فريضة علي كل مسلم  ومسلمة)

Hujjar dalilin neman ilimi tana cikin ayar da Allah SWT ya turo Mala'ika Jibrilu AS wadda aka cirota daga Lauhul Mahfuz zuwa Baitul Izza (Ka'aba dake sama ta daya) wadda itace aka fara saukarwa zuwaga Annabi SAW wato Suratul Alaq aya ta farko:

( اقْرَأْ بِاسْمِ رَبِّكَ الَّذِي خَلَقَ )

 

العلق (1) Al-Alaq

Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta.

Hujja ta biyu kuma, itace wata aya: a lokacin da ake yiwa Annabi SAW wahayin Qur'ani ya kasance idan Mala'ika Jibrilu AS ya karantardashi sai ya dinga karantawa da sauri don gudun kada ya manta sai Allah SWT ya saukarda wannan ayar:

( فَتَعَالَى اللَّهُ الْمَلِكُ الْحَقُّ ۗ وَلَا تَعْجَلْ بِالْقُرْآنِ مِن قَبْلِ أَن يُقْضَىٰ إِلَيْكَ وَحْيُهُ ۖ وَقُل رَّبِّ زِدْنِي عِلْمًا )

طـه (114) Taa-Haa

Sa'an nan Allah Mamallaki, Tabbatacce Yã ɗaukaka. Kuma kada ka yi gaggãwa da Alƙur'ãni a gabãnin a ƙãre wahayinsa zuwa gare ka. Kuma ka ce: "Yã Ubangiji! Ka ƙãra mini ilmi."

Iya wannan ayar kadai ta isa kafa hujja da neman ilimi ga kowanne musulmi. Akwai kuma hujja ta uku, wato: ayata 25 har zuwa ta 28 (a cikin dai Sura ta 20 din) inda Annabi Musa AS yake roqon Allah ya buda masa kirjinsa (da ilimi)

( قَالَ رَبِّ اشْرَحْ لِي صَدْرِي )

طـه (25) Taa-Haa

Ya ce: "Ya Ubangiji! Ka buɗa mini, ƙirjĩna.

Haka kuma akwai sahihin hadisi wanda Annabi SAW ya ce: "Neman ilimi wajibi ne ga kowanne musulmi"

Tirmidhi Chapter 10 Hadisi mai lambata 2614

Sannan hadisin yazo a cikin Sunan na Ibn Majah da kuma Musnad na Imam Ahmad

Shi ilimi baya buya haka ma jahilci baya buya. Misali: Ibn Sina (Rahimahullah) ya kasance shahararren masanin lafiya wanda akewa laqabi da Yariman likitoci (Prince of Physicians) kuma har yanzu jami'o'in duniya suna kafa hujja da littafinsa mai suna Littafin Likitanci (The Book of Medicines) wanda Lorry Dowsing ya ce "Duk wanda yaje asibiti ya amshi magani ya warke to ya zama tilas yayi addu'a ga Avecina (Yana nufin Ibn Sina) kuma a cikin Qanun na Ibn Sina shi dai Lowry Dowsing din ya fitarda mujalladi (Volume) na littafinsa ya kawo sunan Ibn Sina a matsayin abin kafa hujja. Da neman ilimi ba abune mai muhimmanci ba da kafirin likitancan bazai kafa hujja da littafin musulmin likita ba

Irinsu ibn al-Haitham balaraben da ya kirkiro camera ta daukan hoto mawallafin littafin Kitabul Manazir (Book of Optics), irinsu al-Khawarizimi dan kasar Persia wanda ya kirkiro concept din linear da quadratic equation da  kuma Algebra, ga al-Kindi wanda ya kirkiro sufuri (zero:0), ga irinsu al-Idrisi balaraben da ya fara fitarda taswira (map) din duniya, shine ya wallafa littafi Tabula Rogerina (Book of Roger) littafin da Sarkin Norman Roger II ya sahale fitarsa mai daukeda taswirai 70 da suka kunshi geography climates dakuma dabi'un al'umma daban daban, irinsu Abu Abdullah Muhammad Ibn Batuta dan kasar Morocco wanda ya share wajen shekaru 30 yana zagaye kasashen duniya dayawa tareda tattaro ilimin da ya samu ya wallafa littafi mai suna "Rihla" ma'ana tafiye-tafiye (travels)

Abbas Ibn Firnas, likita, mawaqi, engineer kasar  dan Andalusia, shine engineer na farko wanda ya fara gwaji akan yiwuwar mutum zai iya shawagi a sama kamar tsuntsu, wanda yayi wasu yan hikimomi (ya daure jikinsa da wasu sassan ressan bishiya kamardai fuka-fukai) ya hau saman gini ya fado sai gashi yana shawagi a sama kamar tsuntsu wanda silar hakan aka bude kofar binciken da har aka kirkiro jirgin sama. Shine ya kirkiro agogon ruwa dakuma alhariri a jikin garaya ta dinga fitarda sauti (guitar). Ibn Firnas yayi tadabburine da ayoyin Qur'ani kamar irinsu aya ta 19 dake cikin Suratul Mulk inda Allah SWT ya ce:

( أَوَلَمْ يَرَوْا إِلَى الطَّيْرِ فَوْقَهُمْ صَافَّاتٍ وَيَقْبِضْنَ ۚ مَا يُمْسِكُهُنَّ إِلَّا الرَّحْمَٰنُ ۚ إِنَّهُ بِكُلِّ شَيْءٍ بَصِيرٌ )

الملك (19) Al-Mulk

Bã zã su yi dũbi ba zuwa ga tsuntsãye a kansu, mãsu sanwã, kuma suna fiffikãwa, bãbu mai riƙe da su sai (Allah), Mairahama? Lalle shi Mai gani ne ga dukan kõme.

Hatta mata ma ba'a barsu a baya ba, irinsu Zaynab bint al-Kamal, yar Baghdad dake kasar Iraq, tayi rayuwa a karni na sha uku (13th century) itace mace ta farko da ta zamo likita mai lasisi kuma itace ta gina asibiti mai suna Dar al-Shifa (house of healing) bi ma'ana "Gidan waraka" wanda har yanzu ana amfana dashi. Likitar (Zainab) ta wallafa littattafai na lafiya kuma ta shiga tarihin wadanda suka bada gudunmawa a duniyar ilimin lafiya, an girmamata a zamaninta silar bude kofar neman ilimi ga mata. Kalubale ga matan wannan zamanin wanda a maimakon a nemi ilimi ayi aiki da shi saidai a share awanni anata kallon fina-finai da sauraren kade-kade wadanda bazasu amfanar da su anan duniyarba ballantana acan lahira

Dukkan wadannan bayin Allah wadanda kusan shekara duba da ta wuce sun duqufane wajen neman ilimi da kuma yadashi. Indai muma zamu duqufa muyi da ikhlasi mu cire riya to tabbas wataran sai sunanmu ya shiga tarihin masana

Ya Allah ka bamu ilimi mai amfani wanda zai zamo sadaqatul jariya

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa:

Usman D. Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments