Ticker

Daular Haɓe a Ƙasar Zazzau

A cikin Lardinunan Arewa masu daɗaɗɗen tarihi akwai Lardin Zazzau,wanda ya yi fice wurin bunƙasa harkar kasuwanci da albarkatun ƙasa da kuma yake da kabilu iri-iri wanda suke zaune a yankunan ta. 

Kafin zuwan Musulunci,wanda suka fara mulki a farkon ta su ne Haɓe,kuma sun fara zama ne a wani gari mai suna Turunku.

Waɗannan Haɓe su ne ake kira da asalin Hausa a wani ƙaulin, kuma suna da al'adu da dabi'u daban-daban.

Baya ga Turunku, sun zauna a wasu wurare masu yawa kamar Madarkachi, Kufena, Tukur-tukur da sauran su.

Haka suna da alaƙa da wasu kabilu kamar Gbagyi,Kurama da kuma Kadara.da suka zauna a wuraren kufaina,har yanzu yankin na da ganuwa mai tsohon tarihi.

Tarihi ya nuna sarakunan Haɓe 60 aka yi lokacin da suke jagoranci kafin jihadin Shehu Usmanu Bin Fodiyo a shekarar 1804.

Ga sunayen su kamar haka:

-Gunguma -Matazu -Tumsa -Tamrasu -Suleiman-Nasau-Dan Zaki-Nayuga-Kauci-Nunaki-Mushalkwui-Kayau-Najida-Bushaikuri-Kirari-Jajunuku-Kana-Muhammadu-Ab-Gudumasu Kana-Tukira-Kunasu-Baka Turunku-Amina-Ibrahimu-Muhammadu Rabbu-Alu-Bako Ɗan Mowa-I'shaku-Buraimu Asha kuka-Bako Dankana-Muhammadu Uban Bawa-Muhammadu Ɗan Bawa-Muhammadu Ɗan Gabi-Muhammadu Gabi-Muhammadu Abu-Bawawa-Yunusa-Baku da Mutum Shehu -Aliyu-Muhammadu Maigamo-I'shaku Jatau-Makau.

Wadannan su ne jerin sunayen sarakunan Haɓe 60 da suka yi Sarautar Zazzau kafin jihadin Shehu Usmanu Bin Fodiyo.

Daga ciki akwai musulmi akwai kuma wanda ba musulmi ba,wato maguzawa ne 

Amma tun kafin jihadin Shehu Usmanu Sarkin Zazzau Muhammadu Jatau ke cikin musulunci kuma a dalilin kasancewar shi musulmi, baya jin daɗin maguzancin da ake a lokacin,ya kuma taimakawa Fulani masu bin addinin musulunci a wannan lokaci.

Lardin Zazzau shi ne mafi girma a duk lardunan ƙasar Hausa,kuma ɗaya daga cikin lardunan masu tarihi saboda yakeyaken da sarauniyar Zazzau Amina ta yi a wancan lokaci.

www.amsoshi.com

Daga:

muazu.abubakar011@gmail.com

Post a Comment

0 Comments