𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Shin Annabi Isah zai dawo ko ba zai dawo ba, kuma
menene ban-banci tsakanin ayata (158) cikin suratul nisa'i da ayata (117) cikin
suratul ma'idah, domin ɗaya tace an daukeshi sannan ɗaya kuma tace (lokacinda ka karɓi raina)?.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
الحمد لله.
Hakika ya tabbata Annabi Isah ( Alaihissalamu) zai sakko akarshen
zamani yakashe dujal ya karya Abun da kiristoci suke riyawa cewa da shi ne
aka sokeshi yayinda Allah yadaukeshi zuwa sama, zaikashe aladu ba zai karɓi wani addini ba inba Musulunci ba, Hakika
nassoshi daka Alqur'ani da sunnah Sun nuna hakan, Allah madaukakin Sarki ya ce:
ﻭَﺇِﻧَّﻪُ ﻟَﻌِﻠْﻢٌ ﻟِّﻠﺴَّﺎﻋَﺔِ ﻓَﻠَﺎ ﺗَﻤْﺘَﺮُﻥَّ ﺑِﻬَﺎ ﻭَﺍﺗَّﺒِﻌُﻮﻥِ ﻫَﺬَﺍ ﺻِﺮَﺍﻁٌ ﻣُّﺴْﺘَﻘِﻴﻢٌ ١٦
Lallai Sakkowar Annabi Isah (Alaihussalamu) ilmi
ne na tabbas Alkiyama zata tsaya, kada ku ruɗu da duniya, kubini (Ni manzan Allah
sallallahu Alaihi wasallam) wannan ita ce hanyata mikakkiya. (Suratul
zukhruf:61)
Ibnu kaseer rahimahullahu ya ce: Lamirin Sunan
yana komawane zuwaga Annabi Isah Alaihissalamu domin maganar tazo acikin
jerangiyar Anbatonsa, sannan Abun da ake nufi shi ne sakkowarsa zuwa duniya
kafin tashin Alkiyama, Kamar yanda Allah maɗaukakin Sarki ya ce:
ﻭَﺇِﻥ ﻣِّﻦْ ﺃَﻫْﻞِ ﺍﻟْﻜِﺘَﺎﺏِ ﺇِﻟَّﺎ ﻟَﻴُﺆْﻣِﻨَﻦَّ ﺑِﻪِ ﻗَﺒْﻞَ ﻣَﻮْﺗِﻪِ
Lallai tabbas daka cikin kiristoci za a samu waɗanda za suyi imani da shi kafin mutuwarsa.
وَﻳَﻮْﻡَ ﺍﻟْﻘِﻴَﺎﻣَﺔِ ﻳَﻜُﻮﻥُ ﻋَﻠَﻴْﻬِﻢْ ﺷَﻬِﻴﺪًﺍ.
Sannan ranar Alkiyama za su kasance masu bada
shaida akansa.
Abun da ke karfafar wannan cikin dalilai na dawowar Annabi Isah kAlaihissalamu) shi ne
faɗin Allah maɗaukakin Sarki awata kira'ar daban:
وَإِنَّهٌ لَعَلَمٌ ﻟِّﻠﺴَّﺎﻋَﺔِ
dayiwa (Ainun da lamun fataha) Wato tabbas
Sakkowar Annabi Isah (Alaihissalamu) Alamace tazuwan Alkiyama...
Kamar yanda Aka ruwaito daka (Abu huraira da Ibnu
Abbas da Abul Ããliyah, da Abiy Malik da ikrimah da hasan dasauran Malaman
tafsiri)
Hakika hadisai wanda sahabbai Samada saba'in suka
ruwaita daka Annabi (Sallallahu Alaihi wasallam) wanda Malaman hadisi suke
kirada (Mutawatiri) Sun tabbatar da yafada Annabi Isah (Alaihissalamu) zaidawo
duniya Akarshen zamani. amatsayin jagora adali Mai hukunci da gaskiya .
Duba tafsirin Ibnu kaseer (7/23) da fat-hul bããry
( 6/568)- ( 6/439..
Kamar yanda hadisin Bukhari ( 448) da Muslim (
155) Wanda Abu huraira yaruwato ya nuna.
Wannan malamai Sun haɗu babu kokwanto ko jayayya a kan Annabi
Isah (Alaihissalamu) Bai mutuba kuma ba'a sokeshi ba, Allah yadaukeshi zuwa
sama dajikinsa daruhinsa, kuma tabbas Zai sakko daka sama zuwa Duniya Dab da
tashin Alkiyama, wannan babu Saɓani
akai.
Malamai Sunyi saɓani ne a kan wafatin dayazo acikin ayar
datake cikin *suratul Ma'idah ayata (117):
ﺇِﺫْ ﻗَﺎﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻳَﺎ ﻋِﻴﺴَﻰ ﺇِﻧِّﻲ ﻣُﺘَﻮَﻓِّﻴﻚَ ﻭَﺭَﺍﻓِﻌُﻚَ ﺇِﻟَﻲَّ.
Lokacinda Allah ya ce: Ya Annabi Isah zan maka
wafati indaukeka zuwa gareni.
Abisa zantuka masu yawa Nafarko daka cikinsu: Yana
nufin wafatin mutuwa, domin shi ne zahirin ayar gawanda bai lura dasauran
dalilai ba, saboda kuma hakan ya mai-maitu acikin Alqur'ani da irin wannan
ma'anar misali faɗin
Allah maɗaukakin
Sarki:
ﻗُﻞْ ﻳَﺘَﻮَﻓَّﺎﻛُﻢْ ﻣَﻠَﻚُﺍﻟْﻤَﻮْﺕِ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻭُﻛِّﻞَ ﺑِﻜُﻢْ.
Kace Mala'ikan da'aka wakilta wajan zare rayukan
bayine yake dauke ranku
Awannan ayar an ambaci (wafati) da ma'anar Mutuwa.
Ma'ana ta biyu: Tana nufin ɗaukewa rikewa, ibnu jareerul dabary ya
ruwaito haka acikin tafsirinsa daka dayawa cikin magabata Nagari.
Magana ta
Uku:Ma'anar ayar datake cikin Suratul Ma'idah, Tana Nufin wafatin bacci,
nadaukeka daka cikin halittun duniya zuwa halittun sama, hakika dalilai sun
nuna cewa bai mutuba, saboda haka dole adora ma'anar ayar a kan cewa ba
(wafatin mutuwa ake nufi ba,) Ayar tana
nufin wafati na Bacci dan hada dalilan guri daya) Kamar fadin Allah madaukakin
Sarki;
ﻭَﻫُﻮَ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻳَﺘَﻮَﻓَّﺎﻛُﻢْ ﺑِﺎﻟﻠَّﻴْﻞِ.
Allah shi ne wanda yake karɓar rayukanku cikin bacci da daddare.
dafadinsa Madaukakin Sarki:
ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻳَﺘَﻮَﻓَّﻰ ﺍﻟْﺄَﻧْﻔُﺲَ ﺣِﻴﻦَ ﻣَﻮْﺗِﻬَﺎ ﻭَﺍﻟَّﺘِﻲ ﻟَﻢْ ﺗَﻤُﺖْ ﻓِﻲ ﻣَﻨَﺎﻣِﻬَﺎ ﻓَﻴُﻤْﺴِﻚُ ﺍﻟَّﺘِﻲ ﻗَﻀَﻰ ﻋَﻠَﻴْﻬَﺎ ﺍﻟْﻤَﻮْﺕَ ﻭَﻳُﺮْﺳِﻞُ ﺍﻟْﺄُﺧْﺮَﻯ ﺇِﻟَﻰ ﺃَﺟَﻞٍ ﻣُﺴَﻤًّﻰ.
Allah shi ne yake karɓar rai lokacin mutuwarta, dawacce bata
mutuba acikin barcinta, wacce ajalinta yacika acikin barci sai arike ran baza'a
dawo mata dashiba, wacce kuma ajalinta baizoba sai akyale mata ran zuwa
lokacinda aka diba mata na mutuwarta.
Zantuka biyun karshe sunfi nafarko rinjaye.
Takowanne halidai gaskiyar datake tabbatacciya ita
ce Annabi Isah (Alaihissalamu) Allah yadaukeshi zuwa sama araye, kuma bai mutu
ba, Har gobe yana nan araye asama harzuwa randa Allah zai sakko da shi zuwa
duniya, zai tsayar dayin Abubuwanda Annabi (Sallallahu Alaihi wasallam) yabada
labarin zaiyi inya dawo,
Sannan sai ya Mutu mutuwar da Allah yawajabta
masa, dakanan za ka gane waɗanda
sukace wafatin dake cikin ayar suratul ma'ida yana nufin wafatin mutuwa zancene
rarrauna abun wurgarwa, idanma Ance dole wafatin mutuwa yake nufi, to abun nufi
da shi shi ne wafatinda zaiyi bayan yadawo duniya akarshen zamani, sai ya
kasance ambatonsa da'akai yana cikin babin fara gabatar dawani abu amma ana
nufin jinkirtuwarsa, domin (wawun din jerin zancen) bata nufin zuwan Abu ɗaya bayan ɗaya, wannan sannan wannan, Kamar yanda
malamai suka fadakar.
Ita kuma ayar suratul Nisa'i tana kore aqidar Kiristoci
ne dasuke qudurce cewa sokeshi akai yakai ya mutu, Allah yabasu amsa dacewa:
ﻭَﻣَﺎ ﻗَﺘَﻠُﻮﻩُ ﻭَﻣَﺎ ﺻَﻠَﺒُﻮﻩُ ﻭَﻟَﻜِﻦْ ﺷُﺒِّﻪَ ﻟَﻬُﻢْ ﻭَﺇِﻥَّ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺍﺧْﺘَﻠَﻔُﻮﺍ ﻓِﻴﻪِ ﻟَﻔِﻲ ﺷَﻚٍّ ﻣِﻨْﻪُ ﻣَﺎ ﻟَﻬُﻢْ ﺑِﻪِ ﻣِﻦْ ﻋِﻠْﻢٍ ﺇِﻻﺍﺗِّﺒَﺎﻉَ ﺍﻟﻈَّﻦِّ ﻭَﻣَﺎ ﻗَﺘَﻠُﻮﻩُ ﻳَﻘِﻴﻨًﺎ ٧٥١ ﺑَﻞْ ﺭَﻓَﻌَﻪُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺇِﻟَﻴْﻪِ ﻭَﻛَﺎﻥَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﺰِﻳﺰًﺍﺣَﻜِﻴﻤًﺎ ٨٥١
Basu kasheshi ba, basu sokeshiba, kawai rikitasu
akai aka aje musu wanda yake kama da Annabi Isah ɗin, Abun da sukai saɓani akansa suna cikin kokwantonsa, basuda
ilimi akai saibin zato, basuda dayakinin kashehi, Allah yadukeshi zuwa gareshi.
Dawannan bayani za ka gane duk wanda ya ce Annabi
isah ba zai dawo ba, ko kuma yayi hijira zuwa kishmeer ne sannan ya mutu mutuwa
irinta dabi'ah, ko kuma ansokeshi ya mutu ko wanine mai kama da shi zaizo
akarshen zamani.
Hakika yakirkirawa Allah karya yajingina masa,
kuma tantagaryar makaryacine, kuma duk wanda yaiwa Allah da Manzonsa karya
yakafirta, wajibine masu faɗin
irin waɗannan
zantuka su tuba sudawo musulunci, akuma dunga bayyana musu dalilai daka
Alqur'ani dasunnah ingantattu waɗanda
suka nuna cewa Annabi Isah zai dawo, idan yatuba sai akarbi tubansa idan yaki
kuma za a kasheshi kafiri.
Saboda dalilai masu yawa dasuka tabbatar da
dawowar Annabi Isah.
Duk Wanda kaji yana cewa hadisan da suke nuni da
dawowar Annabi Isah hadisaine Ahããd wanda basa zama hujjah akaran kansu ko basu
ingantaba babu shakka ɓataccene
kanisanceshi zaisa maka ruɗu
acikin aqidarka, kuma lallai Bamu'utazilene kodan jahamiyyah.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.