Gajeruwar Wakekeniya Daga Zauren Makaɗa Da Mawaka

Gajeruwar Waƙeƙeniya Daga Zauren Makaɗa Da Mawaƙa

Babu shakka Yan'uwana,

An raba min hankalina,

Na yi dukkan bincikena,

Kuma na rasa Wanda za na zaba.


Zogale da kuli-kulinsa,

Har da danyar albasarsa,

Ga timatir ja cikinsa,

Ba a mar kwauron abin hadi ba.


Can a gefe kwa ga dajaja,

An gasa ta jikinta yai ja,

Ta ji yaji har da manja,

Kila har magi ba a rasa ba!


Malamai Kuma sun bayani,

Sun kwadaitar sun yi nuni,

Zogale a bisa yakini,

Kaza ba ta kai shi fa'ida ba.


Shi ya sanya duk na rude,

Shin in dau ganyen in tande,

Ko ko kazar za na bude,

Na ci ba sai na bi ka'ida ba?!


Yan'uwa da maza da mata,

Shawararku na ke bukata,

Kar fa in biye zuciyata,

Nai hukumci ba a kan sani ba!

Abubakar Alkantamawy Nakowa 
08022581902

***

Malama Halima Mansur Kurawa:

In za ka bi shawara ta,

Ɗauki ganyen nan kwaɗanta,

Ita kazar nan ka bar ta,

Domin ba ta kai shi fa'ida ba. 

***

Gamarali:

Minyi daidaito a zaɓi

Zogalan shi zani ɗauka

Ita ko kazar in barta

Tunda dai bata fishi faida ba🤣🤣

***

Malam Musa Abubakar Kurawa:

Gaskiya ni shawarata,

Ɗauki zogalan na fahimta,

Don kazar ba ta kai shi fa'ida ba.


Don nai kallo na ƙurlla,

Na ga kaza ce ta gwamna,

Babu komai jikinta,

Kemikal ne suka kumbura ta.


Don haka ɗauki ɗan asalin halitta,

Wanda ba cushe cikinsa,

Kar kai gamo da cutar nan ta kansa.

Post a Comment

0 Comments