Takardar da aka gabatar domin taya Farfesa Muhammad Ahmad Sabon Birni samun kujerar Farfesa a fannin Paediatrics a Makarantar Ilmukan Kiyon Lafiya (College of Health Science), Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato ranar Lahadi 29/1/2023 a Giginya Hotel,Sakkwato da ƙarfe 11:00am na safe
Aliyu Muhammad
Bunza
Sashen
Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar
Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
Waya: 0803 431 6508
Ƙibɗau: mabunza @yahoo.com
Tsakure
Hausawa na cewa: “Kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi.” Kowace irin al’umma magabatanta ke jawo mata girma ko akasinsa. Na tabbata taron ƙasa-da-ƙasa da Jami’ar Sakkwato ta yi kan Daular Gobir 2021 masana ba su raga wata babbar kafa da ɗalibai irinmu za su leƙa ba. Don haka, na ɗan hango wani bagire da ya shafi uban tafiyar kansa wato Sarkin Gobir Malam Sheikh Umar Bawa Jangwarzo. Na yi amfani da tattaunawa da Gobirawa da Fulani da Katsinawa da Kabawa, kuma na ratsi ayyuka wallafaffu da waɗanda ba a wallafa ba kan Gobir da Gobirawa da Sarkin Gobir Umar Bawa. Na amfana da ayyukan da suke cikin google na kuma ratsi kundin tarihin Daular Gobir da Jami’ar Usman Ɗanfodiyo ta wallafa (2021). Na gano ba a samu wani fitaccen aiki da aka yi a kan sunan Sarkin Gobir Malam Sheikh Umar Bawa Jangwarzo ba. Daga cikin Sarakunan Gobir fiye da (300) babu wanda sunansa ya kere na Sarki Umar Bawa. Na yi duba cikin natsuwa kan sunan BAWA a Hausance, kana na warga ga muhallin ‘jan” launi a adabi da al’ada. Na kwakkwafe bayanina a kan kalmar “gwarzo”. Binciken an gina shi kan fasula (13) haɗa da gabatarwa da naɗewa. Nazarin ya gano sunan da sarautarsa da kasancewarsa mai martaba uku, ɗan sarauta, sarki, malami, da gawurtaccen jarumi, su suka ba shi muƙamin da ba basaraken da ke da shi a Gobir da ƙasashen da ke kewaye da ita, wato JANGWARZO. Kirarin “Gobir gidan faɗa” ta daɗe da shi, amma zamanin Sarkin Gobir Malam Umar Bawa aka yi wa kirarin ƙari da cewa: “Gobir Ta Bawa Gidan Faɗa”.Yaƙe-yaƙen Gobirawa shi ya ba su ‘yancin cin moriyar ƙasarsu ta kasance wani gambu da katangar ƙarfe ga sauran ƙasashen Hausa. Hasashen bincikena, ina kyautata zaton ranar LARBA aka haifi Sarki Bawa, saboda sanin jumu’ar da ke albarka tun ranar Larba ake ganewa; bisa ga kirarin Bahaushe na, Larba ta Bawa ranar samu kowa ya samu gare ki, sai ya ƙara. Allah Masani.
Gabatarwa
Al’adar bincike ita ce,
samar da wata ‘yar gudunmuwa ga abin da ya gabata domin ƙara rage
zango. Gobirawa da tarihin kakaninsu sananne ne a adabin baka da rubuce-rubucen tarihi cikin Ibrahimiyanci (Hebrew) da Girkanci, da Larabci, da
Ingilishi da sauran harsunan Afirka. Wannan takarda ɗan tsokaci za ta yi ga ɗan
wani bagire da bai sha lugude sosai daga masana ba. Irin yadda Gobirawa suka
mamaye duniyar baƙar
fata ko’ina sun kafa sansanin gari ko tunga. Sarautunsu suka kai wuraren da faɗin ƙasarsu
bai kai ba. Yaƙe-yaƙensu suka kai nesa ga kadadar ƙasashen da suke iko. Famarsu ta mamaye
su nan magabatansu da mabiya bayansu a tarihi ka ce, babu wata zuriya daga
cikin zuriyar mazauna Sudaniyya in ba Gobirawa ba. Babban abin mamaki sunan
Sarkinsu BAWA ya
mamaye tarihin sarakunan Sudaniyya, ka ce duk daulolin Sudaniyya ƙarƙashin ikon Sarki Bawa suke. Maƙasudin wannan ‘yar takarda kallon sunan sarki Bawa da
abubuwan da sunansa ya ƙunsa,
tare da fayyace amsa amon sunansa “JAN GWARZO” cikin biyar diddigin adabi,
al’ada, da nahawu.
Fashin
Baƙin Matashiya
Kalmar da ta limanci
matashiyarmu ita ce “Gobir”. Masana da dama sun tofa albarkacin bakinsu a kan ta.
A ganin Gobirawa daga GUBUR take wato tsohon wurin da suka baro suka yo hijira.
Wasu masana na ganin daga kalmar “Kobir” ko “Kubir” ne mai ma’anar “Tagulla”
(Coper). Idan ma aka ce daga kalmar “Coper” ce ta Ingilishi akwai abin cewa a
ciki a nahawun tarihi. Masu danganta ta da daɗaɗɗiyar
ginan nan ta Katsina wato “Gobarau” ba jifa cikin tudu suka yi ba. Na daɗe ina tunanin, anya! Hausawa ba daga bakin
Adarawa
ko Azbinawan Agades suka ji furucin suka ara ba? A Bahaushen tunani na tarihin tarihi ya
kamata mu fara jinjina
nauyin wasu kalmomi masu alaƙa da
sunan irin su: Gobara, goriba, gurbi, da sauransu. Yanki na biyu shi ne, “Ta
Bawa” Ba Bawa ne
Sarkin Gobir na farko ba, ficensa da kere da ya yi wa sauran sarakunan Gobir
aka danganta ƙasar
gaba ɗaya da sunansa”.”Ta Bawa”. A nahawu, samun harafin “ta” gabanin suna yana
tabbatar da kasancewar sunan na jinsin “mace” ne, ba a haɗe su da “Bawa”, in an yi sai ya ba da sunan mace “Tabawa”. A gargajiyance gambu shi ne tsaro
ga gari,
da gida, da ɗaki, in babu shamakin gambo babu tsaro
ga muhalli. Gobir ita ce, tsaro ga ƙasar Hausa.
Daga gangan na kawo kirarin
Gobirawa na fama da ake yi musu: “Kurya Gangar Mutuwa”. Kurya turun kiɗa ne da ake haɗawa
da duma wajen kiɗin yaƙi da artabu da tayar da maza daga barcin raggwanci. Kurya ta
fi duma murya mai shiga zuciya da yamutse rayuwa da gigita gwaraje da
gawurtattu. Kurya ba ta barin maza su mazaya sai dai a mutu har liman tare da
mai kiɗin da kuryarsa duka. Da wuya a ji muryar
kurya babu gawa kwance domin muryarta cewa take yi:
: Komi taka zama ta zama!
: Komi taka zama ta daɗe!
Haka Gobirawa suke a fagen daga in nasara, in mutuwa. Dubi
yadda askarawan Satiru
na ƙasar Ɗancaɗi ta
Boɗinga Gobirawa (Wazirin Boɗinga: 2023) ke atisayen yaƙi da Turawan Biritaniya a (1906) suke cewa:
Ku sa kiɗi mazaizai mu gani,
Ko can gida faɗa mun ka sani,
Ba mu san gudu ba sai dai a mutu.
Idan fagen artabu ya yi cin alewar kuturu, kurya ake
jefawa tsakanin maƙiya
mazaje su je su karɓo ta mai rabon ganin baɗi shi gani (Kwatantagora: 1999). Haka idan an rufe birni an
hana abokan gaba shiga, makaɗin kurya yake jefawa
tsallaken ƙyauren ƙofar birni ta je can ta tarar da abokan gaba, su kuwa dakarun
gaba sai tsallakar ƙyaure
da ganuwar gari, a riski abokan gaba cikin garinsu a ce musu aljanna gafara
wuta salamu alaikum. Rashin tsoron Gobirawa da mayar da mutuwa tobashiyarsu, da
rungumar takaici domin kunya ta san in da dare ya yi mata, shi ya sa ake yi
musu kirari da “Kurya Gangar Mutuwa”.
Gurbin
Sunan
“Bawa” Cikin Sunayen Hausawa
Tunanina a wannan bincike in
tsaya kan sunan Sarki Bawa Jangwarzo a kadadar al’adar Bahaushe. A ƙasar Hausa, kalmar “bawa” tana da fassarori da dama. Daga cikin
fassarorin akwai:
1- Bawa daga cikin bayin sarki, ba dole sai bawa na haƙiƙa ba, a’a ha, mai cika wa sarki aiki, da ya ce, “a yi” an gama. Don haka ake ce wa
“dakarun yaƙi",
bayin sarki.
2- Akwai bawa kamamme da aka rinjaya fagen
artabu, ko aka sayo kasuwa, ko ya gaji bauta daga iyayensa, ko aka bautar da shi da ƙarfi-da-yaji a ƙabilance ko a yaudarance da sunan addini.
3- Akwai “bawan gona” wanda aka ba gona ya
noma a shekara ya biya “tirkici” in ya yi dami goma ya ba da ɗaya, in ya yi ɗari
ya ba da goma haka dai zuwa. A Sakkwato da Kabi ana ce da su “Runji”, muna da
“Runjin Sambo” a misali.
4- Akwai “bawan bashi” wanda ya sha ta fi
cikinsa, sai a riƙe
shi a matsayin bawa, ya dinga ƙwadago
ga mai bashi har sai wahalarsa ta biya murgunsa.
5- Akwai “Bawa” wanda ke bi wa mata ga
haihuwa a wasu wurare a ce da shi Gambo.
6- Akwai “Bawa” wanda aka haifa ranar
“Larba” ana sa masa suna “Bawa” domin neman albarkar ranar. Magabata sun ce, an
halicci kowane haske ranar Larba don haka ko karatun zaure ranar Larba ake
farawa, kuma akwai kuɗin bulala da ake biya ranar kowace
Larba. Dalilin Hausawa ke nan na yi mata kirari da:
Larba ta Bawa ranar samu,
Kowa ya samu gare ki sai ya ƙara.
7- Na ƙarshe akwai laƙabin da ake yi wa yara na neman ɗaukaka irin ta “Sarki Umar Bawa Jangwarzo” kowane Bagobir na son a samu Bawa gidansa. Haka
kuma kowane Bahaushe idan ya ji irin ɗaukakar
Bawa da tagomashinsa yakan so ya sa wa yaronsa Bawa domin takwara ga JANGWARZO.
A taƙaice za mu ce, Sarkin Gobir Bawa Jangwarzo sarki ne, ɗan sarki, jikan sarki, don haka hasashe da muka gabatar a
lambobi na (1-4) ba za su kusace shi ba. Ala tilas yana cikin hasashe na (5-6)
wanda shi ya haifar da hasashen na (7). Sunan Sarkin Gobir Umar Bawa Jangwarzo ya ɓace gaba ɗaya sai dai ka ji an ce: Bawa ko Malam
Bawa ko Jangwarzo, a Jamhuriyar Nijar in ba Malam Bawa ka ce ba, ba a gane da
Sarki Bawa kake domin Malami ne kuma Sarki ne gaba da baya, a ji sarki, a ga
sarki. Malam Bawa ya yi tasiri sosai a ƙasar Hausa ba ma ga Gobirawa kawai ba, a’a a tarihin ƙasar Hausa. Ga wasu misalai biyu don
tabbatarwa:
1- A Sakkwato hanyar zuwa mazaunin
din-din-din na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo
Sakkwato akwai Kantin magani gawurtacce sunansa JANGWRZO CH.
2- A Maraɗi
akwai Hotel babba sunansa JANGWARZO kundin PhD Hausa da aka fara yi a fannin waƙoƙin Addini a duniyar ƙasar Hausa, a Jami’ar SOAS Ingila, wanda Prof. M. Hisket ya
yi, (1975) da aka wallafa shi, waƙar Yabon Sarkin Gobir Malam Bawa Jangwarzo aka buga a
bangonsa.
Danganta
Bawa da Launin “Ja” a Bahaushen Tunani
Tunanin wannan bincike feɗe tunanin Gobirawa na saka wa Sarkin Gobir Malam Umar Bawa sunan JANGWARZO,
na ga ya fi kyau mu fara da kalmar “Ja” a Bahaushen tunani. Launin “Ja” kirari
ne ga zarumi saɓanin wasu launuka da ba shi ba. Me ya sa
ba su ce, fari ko kore ko shuɗi da sauransu? Dalili shi ne, fari na
shiga cikin yabo amma ba ya ɗaukar kirari, haka nan sauran launuka. Launin “baƙi" na ɗaukar kirari da yabo amma ba na ma’abota ɗaukaka da alfarma ba. Sauran launukan da muke da su duka ba
sa ɗaukar kirari da kambama ma’abota alfarma
kamar yadda “ja” yake yi a al’adance. Ma’aunin kalmar “ja” ko in ce launin “ja” a dubi ma’auninta:
1- Ja
2- Ja
3- Jajaye
4- Jajaja
5- Jajircewa
6- Jajirtacce
7- Jajirtattu
8- Jajir
9- Jajibiri
10-Jaji
-
Ai
Abubakar jan namiji ne.
-
Garba
ba wasa an ja ya ja.
-
Matan
Buba jajaye ne.
-
Ya
damu fuskarsa ta yi jajaja.
-
Mayaƙan masu jajircewa ne.
-
Bawa
jajirtaccen namiji ne.
-
Dakarun
jajirtattu ne ba wasa.
-
Dubi
idanun mutum kamar
maye jajir ba su da fari.
-
Kwananmu
bakwai ranar jajibirin kokuwar muka isa.
-
Fargar jaji
Bahaushe ya yi tunani mai zurfi wajen zaɓar launin “ja” saboda sabawarsa da ‘ya’yan ita ce da yake
ganin kai matuƙa ta
ninarsu ja suke yi daga
cikin su akwai:
-
Kaiwa
-
Goriba
-
Giginginya
-
Tonka
-
Gauta
-
Wake
-
Gyaɗa
-
Masara
-
Yalo
-
Janzakara
Idan aka kula, yadda duk launin “ja” ya
kasance ya kai
matuƙa ga
nunarsu, haka nan ake ganin kirari da launin ja shi ne matuƙa ga jarumi. Dubi yadda kalmar “ja” ta yi
naso a zantukan hikima da kirare-kiraren Bahaushe:
-
Jan
kara jan zaƙi
(in ji masu rake).
-
Jan
ido alamun namiji.
-
Kowane
gauta ja ne, sai
in ba ji zafin rana ba.
-
Jan
aiki.
-
Aiki
ja.
-
Jar
wuta ita ce danja.
A tunanin waɗannan zantukan hikima da karin magana launin ‘ja’ ba ƙaramar daraja yake da ita ba, musamman a fagen yi wa gwarzo kirarin da ya dace da ƙoƙarinsa. A kowanne daga cikinsu duk irin launin da aka sa ma’anar ba ta fitowa yadda za a
buƙace ta. A
adabin zaruntaka na kambama gwaraje da cicciɓa su, za mu ga launin “ja” na da tasiri ciki sosai, misali a dubi waɗannan zantuka:
-
Jini
da jini, janjan (mabuɗin karafkiya a goshin yaƙi)
-
Jarƙaniya (kalmar ƙundumbala)
-
Jannasuri
(Maciji gawurtacce na cikin suri)
Launin
“Ja” a Tatsuniya da Wasanni
Daga cikin daɗaɗɗun adabin gargajiya akwai tatsuniya da
wasannin yara. Tatsuniya da wasannin yara wasu makarantu ne da kowane ɗalibin ilmi ya
kamata ya ziyarta idan yana son biyan tushen diddigin kowane irin abu da ya
shafi al’adar ma’abotanta. Daga cikin tatsuniya muna da:
Ja ya faɗi, ja ya ɗauke
Giginya ta faɗi ɗan Bafulatani ya ɗauke.
Haka kuma a cikin wasannin yara akwai
wasar da ake yi:
Jagora: Jini da jini.
Amshi:
Janjan.
Jagora:
Rago da jini.
Amshi:
Janjan.
Jagora: Kifi da jini.
Amshi:
Janjan.
Jagora:
Masara da jini.
Amsa:
Yara za su yi tsit! Wanda ya ce jan jan sai duka.
Wasa ne na maza da maza, don haka aka ɗauki
launin ‘ja” na jini aka sarrafa, wanda duk ya yi kuskure zai sha duka sosai ba
mahani. A taƙaice,
jarunta ta yi amo cikin waƙe-waƙen yara da ake sarrafa launin “ja”. Dubi
wani
wasa na
nuna ƙwarewa ga
harshe da matasa ke sarrafa launin “ja” a ciki:
Kai jan mutumin can
Ka ɗauki jar sandar can
Ka kori jar naggen can
Mai cin jar dawar can
Ta jar gonar can
Ta jan mutumin can.
Tabbas! jar sanda da jar
nagge da jar dawa da jar
gona akwai abubuwan hangowa a ciki na nagarta. Jar sanda dole ta kasance kulki.
Jar nagge babu wai ga kasancewarta karsana. Jar dawa kuwa ko a magani mahaɗin maganin mazakuta ce.
Ficen “jan” Launi ga Mu’amular Tsaro da Buwaya
Gobirawa mayaƙa ne gaba da baya, kuma masana ne a kan
harkokin tsaro da dabarun yaƙi.
Saka launin “ja” cikin kirarin “Bawa” wani karatu ne babba. Idan muka yi nazari
za mu ga cewa:
1) Barkono ja ne, jajir da shi ga shi da tsananin yaji, hatta da tattasai da tarugu da suka zo da baya ba sa
ciyuwa idanu ba su yi hawaye
da ja ba. Nagartar namiji jan ido ya sa idanu kuka.
2) Jini na kowace irin haliita “ja” ne
rinjayen launinsa da an ga ya fito a kowane sashe na jikin mai rai razana za ta
shiga. Da yaro da babba babu wanda jini ba ya wa barazana. Haka ake son shugaba
tsakanin mabiya.
3) Wuta, belanta da farshinta da garwashinta duk jajaye ne, kuma
jajirtattu. Da mai hankali da maras hankali ba wanda wuta ba ta sa wa hankali ba. Gaskiyar Bahaushe da yake cewa, yaro bai san wuta ba sai ya dafa. Haka kuma ake
da karin maganar,
wuta ba ta da raggon doki.
4) Da belar wuta, da ruɓushinta, da gaushinta duk jajaye ne. Ko a wasan maƙera takin “kunkurun tama” ƙarfen da aka saka a wuta ya yi jajir sai maƙeran da suka tambayu. Don haka “ja” a
cikin suna nagarta da jarunta yake tabbatarwa.
5) A yi duba zuwa ga bindigoginmu da sojojimu ke amfani da su, a kowace bindiga
ƙarshenta
daidai wurin da balbalin bala’i ke tartsatsi sukan ɗaura ɗan ƙyalle ko tsumma “ja”. A gargajiyance suturar dogarai ‘yan ƙasa na sarakunanmu “ja” ne. Haka kuma,
rawunnan dogarai “ja” ne. Kuben kowane irin makamin Bahaushe za a ga “ja” ne da
aka yi da jemammiyar fata “ja”. Kai! hatta da jar dawa ɓawonta “ja” ne da shi ake yin sarrafa jan launi a waƙoƙi.
Yadda muka ga fasulan jan launi a daɗaɗɗun adabin baka haka nan adibban mawaƙa suka aro su suka sarrafa su a waƙoƙinsu a jigoginsu na yabo ta fuskar jaruntaka da ƙwazo da ƙwarjini. Ashe dai Gobirawa bisa kan hanya suke idan muka
kalli yadda ɗaya daga cikin mawaƙinsu Dr. Ibrahim Abdulƙadir Maidangwale Narambaɗa ya kambama ƙwarewa da adalci da ƙwazon Alƙali Abubakar, Alƙalin Moriki
a faɗarsa:
Jagora: Bilhaƙƙi amali na Jandamo,
Jagora: Abu hukumul ƙadil madhaa,
Yara
: In yai magana ta kwakkwahe.
Gindi
: Ya ɗau girma ya san yabo,
: Mu zo mu ga Alkali Abu.
Haka za mu ga a cikin waƙoƙin Amali Sububu yana koɗa taurararonsa “Aikau Jikan Tayawa”
gawurtaccen manomi da faɗar cewa:
Jagora: Ku dibi idanun mutum
kamar
maye.
Yara : Jajir ba su da fari.
Gindi: Ya riƙa aiki da gaskiyar Allah,
: Bai saba ba da zama,
: Aikau jikan Tayawa ɗan
Mamman Kunkelin fashin ƙasa.
Wannan ya tabbatar da faɗar Bahaushe na jan ido alamun namiji. Idan abu ya kankama ana
saka jan launi wajen yaba shi da ɗaukaka
shi. Da Shata na yabon Alhaji Garban Bici sai da ya sarrafa jan launi ga
yabonsa don ya hanzarta, ya ce:
Jagora: Kaka ta yi uban Nura,
Gyaɗa ta fara jar fata.
Gindi : Haji Garban Bici ɗan Shehu.
A taƙaice, mai yabon mazaje jarumai ba ya da makawa ga aron fasahar Gobiawa ta sa wa Sarkin
“Jangwarzo”. Bawa Ɗan’anace
a waƙarsa da
yabon Birgediya Hassan Usman Katsina yana cewa:
: “Dac can nag ga jan ido.”
A gai da Alhaji Aƙilu Aliyu Birnin Ƙaura Lailai Jega a cikin waƙarsa ta yabon Sojojin Nijeriya, da ta
cinye gasa, a wani baiti yana cewa:
Jar wuta ita ce danja,
Jar baƙar mutuwa soja.
Haƙiƙa sunan Sarki Malam Shekh
Umar Bawa Jangwarzo ya zanu
domin ya ci sunansa da sifanta shi da aka yi da “jan” launi, yanzu sai mu
fayyace abin da
ya biyo bayan jan launi mu gani.
Gwarzo
A mahangar Ƙamusun G.P. Bargery
An enegetic, capable worker;
a man of pluck and grit.
A ma’anar “grit” Ƙamusun Ingilishi ya ce:
Courage and resolve;
strength of character.
A ma’anar “pluck” Ƙamusun Ingilish ya ce:
Spirited and determiend
courege.
Ke nan za mu fassara ma’anar
gwarzo bisa ga waɗannan bayanai da cewa:
Nagartaccen zarumi
gawurtacce mai gaba gaƙi ga
abin da ya tunkara ko ya tinkaro shi mai zuciya sambai da fargaba ba ya yi mata
barazana.
Kalmar “gwarzo” kalma ce ta
nagara bayan an zama nagartacce a hau matsayin jaruntaka a zama jarumi. Idan
jarumi ya ƙasaita zai hau gadon gwarzantaka a kira shi “Gwarzo” kalmar
“Gwarzo” a cikin waƙoƙin saraua wata babbar fitila ce cikin
kalmomin yabo na waƙoƙin sarauta da yabon gwaraje, a ƙasar Hausa. Mu dubi gindin waƙar bakandamiyar Dr. Ibrahim Narambaɗa da ke cewa:
Gindi: Gwarzon Shamaki na
Malam toron
giwa,
: Baban Dodo ba a tamma da batun banza.
Wannan ita ce Bakandamiyar
Malamin waƙar ƙasar Hausa kuma da kalmar “gwarzo” ya yi
shamaki da ita a gindin waƙarsa.
Makaɗa Dandada ya yi tubali da ita a waƙarsa ta:
Gindi: Gwarzon Galadima ya
ci arna,
: Uban Yari baban Barga na farko.
Me ya sa Sarkin Gobir Bawa
ya keɓanta da kalmar “Gwarzo” a cikin
sarakunan ƙasar
Hausa? Babban dalili shi ne, saboda kasancewarsa jarumi a fagen yaƙi bisa ga yaƙe-yaƙen da ya gwabza ƙasa Hausa.
Ƙasaitar “Jangwarzo” Cikin Gwarajen
Sarakunan Sudan
Ƙasar Hausa wata irin makekiyar ƙasa ce da ta ƙunshi al’ummomi masu ɗimbin yawa. Ƙasa
ce da kowane sarki da ƙarfin
soje yake taƙama
da ɗiyaucin kare zuriyarsa. Babu zuriya daga
cikin zuriyoyin ƙasar
Hausa da ke da raggon suna. Kowace ƙasa da fitaccen sarkinta take tinƙaho da bugun gaba. Ga ƙunshiyar masarautun da zuriyarsu da kakaninsu.
|
Ƙasa |
Mutanenta |
Birininsu |
Kakaninsu |
Karin Harshensu |
1. |
Kano |
Kanawa |
Kano |
Bagauda |
Kananci |
2. |
Katsina |
Katsinawa |
Katsina |
Katsi |
Katsinanci |
3. |
Kabi |
Kabawa |
B/Kebbi/Argungu |
Kanta |
Kabanci |
4. |
Zamfara |
Zamfarawa |
Rawayya/Gusau |
‘Yargoje |
Zamfaranci |
5. |
Daura |
Daurawa |
Daura |
Daurama/Bayajida |
Dauranci |
6. |
Zazzau |
Zagezagi |
Zariya |
|
Zazzaganci |
7. |
Gobir |
Gobirawa |
Sabon Birni |
Jangwarzo |
Gobirarci |
8. |
Yawuri |
Yawurawa |
Birnin Yauri/Yauri |
Jarbana |
Yawuranci |
9. |
Maraɗi |
Maraɗawa |
Maradi |
Tcagarana |
Maraɗanci |
10. |
Damagaran |
Damagarawa |
Zinder |
|
Arabci |
11. |
Sakkwato |
Sakkwatawa |
Sokoto |
Danfodiyo |
Sakkwatanci |
Waɗannan gundumomi da daulolin ƙasar Husa manya da ƙananan sarakunansu fitattu ne kuma shahararru a tarihi amma babu
sunan da ya kai na Sarkin gobir Malam Shekh Umar Bawa Jangwarzo amo a cikinsu. Sunan
Sarki Bawa da ƙasarsa
wani gambu daga cikin gambunan rufe ƙofar fice da ɗaukaka a ƙasar Hausa, da an ce Gobir sunan Sarki Bawa Jangwarzo ke fara
faɗowa a zuciyar mai magana da mai
sauraronsa.
Kurya
Gangar Mutuwa
Daulolin nan na ƙasar Hausa da muka lissafa kowannensu na
da ɗan taken tarihi na jaruntaka da ake yi masa in an
ambace shi. Kowane kirari ko take yana da alaƙa da tarihin ƙasar
ko masarautarta ko sarakunanta ko sarkinta ko jama’ar ƙasarta. Ga ɗan abin da nake son in bayyana:
1.
Sakkwato:
Birnin Shehu ta Bello mai da ƙasari
zuma
2.
Kano:
Jalla babbar Hausa, Kano ba gari ba dajin Allah
3.
Argungu:
Na Kanta ba ku da raggo
4.
Katsina:
Dakin Kara
5.
Yawuri:
In ka san Yawuri ka san geshe?
6.
Gusau:
Ta Sambo dandin Hausa
7.
Zazzau:
Zazzau birnin ilmi na Turunku masu kaurin cinya a ba ku ci a ga aiki.
8.
Daura: Ta
Abdu tushen Hausa.
9.
Maraɗi:
10.
Damagaran:
11.
Gobir:
Uwar faɗa ko ta Bawa Uwar faɗa
A taƙaice babu ƙasa daga cikin ƙasashen nan (11) na Hausa da ake yi wa kirari na “faɗa/yaƙi"
in ba Gobir ba. Ashe Sarkinta ya ci sunansa “Jangwarzo” domin tsakanin sarakuna
(10) aka naɗa masa rawanin zama gwarzo a fagen yaƙi har ya ƙaura ba a karɓe tutar a hannunsa ba. Babu wata ƙasa ta Sudaniyya da ke tinƙaho da da dakaru da Gobir ba ta gwada
tsawo da ita ba. Gobirawa ba su taɓa
kunyata Jangwarzo har bayan ya ƙaura ba. Don haka mawaƙinsu ke cewa:
Jagora: Gobirawa kun sha
kunun baƙar
zuciya,
Yara : Nan gidan duniya babu inda ba a ji ku ba.
Gobir
Gambun Hausa
Lokacin da ƙasar Hausa take yau ciwo gobe lafiya a
kan yi wa manyan birane da gururuwa ganuwa a sa ƙyaure/gambu a rufe a naɗa
sarkin ƙofa.
Idan an yi haka, ba shiga, ba fita sai da yardar Sarkin ƙofa. Irin haka ne Gobir ta kasance wa ƙasar Hausa. Tsoron Gobirawa da ake yi a
fagen daga musamman zamanin Sarkin Gobir Malam Bawa Jangwarzo ya sa ƙasashe da yawa na jin tsoro kawo hari ƙasar Hausa. Bayan cin Alkalawa da masu
jihadi suka yi 1809, Gobirawa ba su tarwatse ba, domin wasu suka koma Tcibiri,
wasu suka bi Yariman Gobir Ɗanhalima
suka sake kafa Sabon Birnin Ɗanhalima
kusa da
Kogin Bunsuru (Gobir: 2021:5). A taƙaice Gobirawa sun yaƙi Kabi a ƙarni
na 18th, Zamfara ta rushe a ƙarni na 14th C, Katsina 1764. Don haka, da Katsina
da Zamfara da Kabi sun yi wa Gobir gambu babu mai ratso su shi kai mata hari, ita kuwa ta
yi musu gambu babu wanda zai tunkare ta da yaƙi, domin ya san suna tare (‘Yandaki: 2021:11). Bugu da ƙari Gobir ta gwabza da Azbin da Adar a ƙarni na 7th C, a nan ma ta yi
wa ƙasar Hausa
gambu ga masu ƙetaro
kashin giwa su ce su shigo ƙasar
Hausa. Gobirawa suka fara kafa dangantaka mai ƙarfi da ƙasashen
nesa ga ƙasar
Hausa irin su Yemen, Saudi Arabiya, Egypt, Sudan da Daular Borno, a tarihin ƙaurace-ƙauracensu duk suna da danganta da su, wanda ya ƙara wa ganuwar ƙasar Hausa da ƙyaurenta ƙarfi sosai.
Ja
da Baya ga Rago
Hausawa na cewa: “Ja da baya ga rago ba tsoro ba ne duk
cikin shirin yaƙi
ne.”
Babu gwarzon duniya da zai bugi ƙirjin cewa ba a taɓa
ribantarsa ba. Wurin da gizo ke saƙa shi ne, a karaya a gudu a tsere a yi hijira, a ce an tuba da faɗa wanda ba ya cikin kundin tarihin Gobirawa. Duk da haka, Gobirawa
sun yarda da a share jini a koma wasa, sai dai ba su yarda da faɗan da ya fi ƙarfinka
ka mai da shi wasa ba. Domin su a wajensu yaƙi shiga sojan Badakkare ne, in til, in ƙwal
rinin mahaukaciya. Yaƙe-yaƙensu ya ba su damar wasanni tsakaninsu
da Zamfarawa, Fulani, Yorubawa, Katsinawa da zumunta da Kabawa. Babu wai,
zancen a mazaya a mayar da iri gida ya yi naso a yaƙin Dutsen wake a ƙasar Kiyawa (Ibrahim: 2021:343) da yaƙin Ɗanƙasawa
zamanin Ummaru Dallaje (1807-1835) Gobir agaji ta bayar da yaƙin ci-kaji (1978) zamanin Sarkin Gobir
Ibrahim Shawai, agaji Gobir ta kai. Ga al’adar faɗa da
yaƙi da
jihadi, yaudara da salon ja da baya a sake shiri ba kasawa ba ne, cikin dabarun
fama ne da suke shiri.
Sakamakon
Bincike
Tunanin wannan bincike shi
ne duba zuwa ga jagoran Gobirawa da ya fi kowane sarki daga cikin sarakunan
Gobir fice da kere ga
suna. Abu na farko da na gano, Sarki Umaru Bawa Jangwarzo martaba uku yake da su da suka zama tsani ga ɗaukakarsa. Na farko Basarake ne gaba da baya. Na biyu,
Malamin addini ne, ko an ƙi a
faɗa don hasada. Na uku jarumi ne, jarumi uban gidan jarumai don haka aka
ba shi laƙabin
JANGWARZO. Irin tsayin dakar da Sarkin Gobir Malam Umar Bawa Jangwarzo ya yi na hanawa magabta ratsa ƙasarsa, da yi mata gambu da ƙasashen da ya yaƙa, da hana ta miƙa wuya da kasancewa ƙarƙashin kowace irin daula ta kowace irin jinsin
mutane ƙarƙashin kowane irin salo shi ne musabbabin
haɗin kan Gobirawa da ƙasaitarsu a farfajiyar Sudaniyya. Sarki
Bawa ya tsare wa Gobirawa ƙasarsu,
tarihinsu, addininsu, al’adunsu, da ɗiyaucinsu, ya girka wa Gobirawa kishin ƙasarsu a zukatansu wanda ya hana wa
Gobirawa ɗaga hamata ga kowace ƙabila da ke son ta yi musu shigar kutse. Na dai tabbata sunan JANGWARZO
ya cancanci Bawa domin ya mayar da ragon suna.
Naɗewa
Daga cikin zuriyar Hausawa
da ke zaune a ƙasar
Hausa babu zuriyar da ta fi ta Gobirawa haɗin
kai. Babu wani lungu daga cikin lungunan ƙasarmu Nijeriya da Gobirawa ba su yi sansani ba. A cikin
Afirka ta Yamma sun barbazu sosai da sana’o’i daban-daban. Gobirawa na daga
cikin zuriyar Hausawa da suka kiyaye dangin jininsu da sarautunsu da kadadar ƙasarsu. Tsagar fuskarsu ta daban ce, ba a yin ta ga duk wanda
ba ga uba ya gaji Gobarci ba, kuma ba su yarda da aron tsagar fuskar kowa ba.
Biyayyarsu ga shugabanci da gabaci ya sa, har gobe ba su daina yi wa ‘ya’yansu
laƙabi da
sunan Sarkin Gobir Malam Bawa Jangwarzo ba. Haka kuma babu basaraken da ya ari sunan “Jangwarzo” har yau.
Abin ban sha’awa na taɓa tambayar wani bakaniken motoci marsandi a Buzaye mai suna
Aliyu ma’anar Lambar SBN (Sabon Birni) ya ce: S. Shehu, B. Bello, N. Nana Asma’u. Allahu akbar! A share jini a koma wasa, lallai
sarkin Gobir Shekh Malam
Umar Bawa
Jangwarzo ya ci sunan SARKI ba Sarkin ƙaƙe
ba.
Manazarta
Ahmad, S. A. (2021) “Waiwayen Sarautun Mata Na
Daular Gobir da Yadda Za a Farfaɗo da Su.” Cikin Maishanu, I. M., Usman, M.T. da Gobir, A. Y.
(Editoci). Proceeding International Conference
on Transformations in Gobir Kingdom Past and Present,Pp.369-377. Published
By Faculty of Arts and Islamic Studies, Usmanu Danfodiyo
University, Sokoto. Kaduna: Amal Printing Press.
Aliyu,
A. “Waƙar
Yabon Sojojin Nijeriya.”
Ammani, M. (2021) “Gurbin Gaskiya a Bakin Makaɗan Gobir: Tarke Daga Waƙar
Alƙali Abu ta Ibrahim Narambaɗa.” Ciikin Maishanu, I.
M., Usman, M.T. da Gobir,
A. Y.(Editoci). Proceeding International
Conference on Transformations in
Gobir Kingdom Past and Present,
Pp.393-405. Published By Faculty of Arts and Islamic Studies,UsmanuDanfodiyo University, Sokoto. Kaduna: Amal Printing Press.
Augi, A. R. (1984) “The Gobir Factor in
the Social and Political History of the
Rima Basin” (Circa 1650-1808), PhD thesis, Zaria: Ahmadu Bello University Vol.1.
Bargery, G. P. (1993) A Hausa-English
Dictionary and English- Hausa Vocabulary
(Second Edition). Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.
Bunza, A.M. (2009) Narambaɗa, Ibrash, Lagos: Surulere.
Bunza, A. M., Sarkin Sudan, I. A., Usman, B. B. (2009) Daular Sakkwato(Fassarar
Sokoto Caliphate na Mury Last). Lagos: Ibrash Islamic Publication Centre Limited.
Bunza, A. M. (2021) “Ba a Wane Baki Banza (Gurbin Daular
Gobir da Gobirawa a Farfajiyar
Sudaniya.” Cikin Maishanu, I. M., Usman, M.T.
da Gobir,
A. Y. (Editoci). Proceeding International
Conference on Transformations in Gobir Kingdom Past and Present, Pp.242-259. Published By Faculty of Arts and
Islamic Studies, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto. Kaduna: Amal Printing Press.
Danmode, H. O. (2021) “Re-Enacting the Place and Position
of Gobir Kingdom Beyound the Confines
of Nigeria.” Cikin Maishanu, I. M., Usman, M.T. da
Gobir, A. Y.(Editoci). Proceeding
International Conference on Transformations
in Gobir Kingdom Past and Present,
P.7-10. Published By Faculty of Arts and Islamic Studies,Usmanu Danfodiyo
University, Sokoto. Kaduna: Amal Printing Press.
Furniss, G. (1996)
Poetry Prose and Popular Culture in Hausa. EU: Edinburgh.
Gobir, A. Y. (2016). “Gobir Wani Jigo a Ƙasar Hausa:
Waiwayen Tarihi da Diddigin
Masarautun Gobir.” A cikin Malumfashi, I. A., Yakasai, S. A., da Sarkin Sudan, I. A. (editoci). The Hausa People, Language and History:
Past Present and Future. Kaduna: Garkuwa Publishers.
Hisket, M. (1975)
A History of Hausa Islamic Verse. London: School of Oriental
and African Studies, (SOAS).
Ibrahim, A. (2021) “Hoton Yaƙe-yaƙen Gobirawa da Katsinawa Cikin Karin
Maganar “A Mazaya a Mai da Iri Gida.” Cikin Maishanu, I. M.,
Usman, M.T. da Gobir, A. Y. (Editoci). Proceeding International
Conference on Transformations in Gobir Kingdom Past and Present, Pp.334- 347. Published By Faculty of Arts and Islamic Studies, Usmanu Danfodiyo University,
Sokoto. Kaduna: Amal Printing Press.
Last, M. (1967) “Sokoto Caliphate.” PhD thesis, Ibadan: University of Ibadan.
Mamman, J. S. (2014) “A Literary
Analysis of the Themes and Imagery in Amali
Sububu’s Songs.” M.A Thesis, Sokoto: Department of Modern European Languages and Linguistics, Usmanu Danfodiyo University.
Sani, A., Gobir, A. Y. (2021) Wasanni a Ƙasar
Hausa.
Kaduna: Amal Printing Press.
Sarkin
Sudan, I. A. (2021) “Gobarci: Tsagar Gobirawa a Faifan Nazari.” Cikin Maishanu, I. M., Usman,
M.T. da Gobir, A. Y. (Editoci). Proceeding
International Conference on Transformatuions in Gobir Kingdom Past
and Present, Pp.384- 392. Published By Faculty of Arts and Islamic Studies,
Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.Kaduna:
Amal Printing Press.
Yandaki, A. I., Gusau, S. S., & Yandaki, U. A. (2021) “Gobir External Relations in the 18th Century.” Cikin Maishanu, I. M., Usman, M.T. da Gobir, A. Y. (Editoci). Proceeding International Conference on Transformatuions in Gobir Kingdom Past and Present, Pp.11- 24. Published By Faculty of Arts and Islamic Studies, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.Kaduna: Amal Printing Press.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.