Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.
Haɗa Kalmomi
36. Ba ita ke baba,
birni, buzaye,
Bar bakalin biri yana bin ganyaye,
Bobo ba ruwansa sabgar
bokaye,
Ba,
bi,
bo da bu, da be kwai bebaye,
Borin
beguwa ƙaya taka harbowa.
37. Ɗauko
‘ca’ mu
yo misalai kyawawa,
Ca ita ke da caca, ciwo, cutarwa,
Ce kaca, carafke, cacuma ga
gocewa,
Cinnaka, cida, kucaki, ciza
da ƙucewa,
Mai cin Cera ba
ya burge Hausawa.
38. Dawa, dankali,
akai dogo, dubbai,
Dakali ya daɓe a dandali
can Dabai,
Dogon dogari ya sanya wando
baibai,
Dakaru dubu dukansu du ba
kibbai,
Ita ko, Dediya hatsi taka katsewa.
39. Fara mara fuka-fukin
ba ta firka ba,
Duba daɗin misalai idan ba ka gane ba,
Fafe duma farat guda ba aiki ba,
Fati fito ki kai fura zauren
baba,
Ka da
ki bari a feƙe ƙwaryar damawa.
40. Gangara gangaren Bala geben Suru,
Gagare ga shi yanzu ya gagari taru,
Gabada, gada, gida, goro da guru,
Ga gara, gira, gumi,
ga kuma goru,
Mai gemu ya zanka aiki na yabawa.
41. A misalai
‘h’ idan zan zanowa,
Hauka, hankali ka magance taɓewa,
Yanzu mu lura ga su jumla ka biyowa,
Na ga Habu ga hira shi ke holewa,
Hura wuta cikin dawa sai herewa.
42. Yanzu mu ɗauki ‘j’ mu jera
misalinshi,
Jaji Hajjo juyi,
jeji duka sa shi,
Ga wata jumla a zan kula
zan gane shi,
Jakin Jika jori na son
huda shi,
Juraha ɗan Baduku manyan jemewa.
43. “K(a)” na nan ga sautuka bari in jero,
Kaki, koko, kuka, rakke sa koro,
Ga jimla ƙasa misalan zan ƙaro,
Kakaki kira yakai Allah koro,
Kukuma amonta shi ke godewa.
44. “L(a)” sautin amonta tamkar dai lalo,
Lale marhaba da ‘yan wasan ƙwallo,
Ga wata jimla cikinta
“l(a) ta sha lilo,
Liman Bawa shi ka limancin Lolo,
Lura da lokaci ake iya lelawa.
45. Matar Manu na ga ta aiki su Kande-
Mamman, Mode har da Mani
sa Mande,
Mai damun fura a nemo
mata ludde,
Matan Minjibir suna neman Mode,
Mai musu munduwa
da buzun jemewa.
46. A kalmomi ‘n’ takan fito in kun yarda,
Nana, niƙa da naniya ga kuma hoda,
Idan mun sa a jimla ‘n’ kan
bayar da:
Nana ka son ni’imta nono
ya yi tsada,
Kwara ruwa gare shi nan
muka
ganewa.
47. Raggo bai da rangwame dutsen Dala,
Rigar ragguwa da dauɗa ɗan kalla,
Ra
ke raraka a kalmomi kalla,
Ragon Rigu ya yi rero madalla!
Dussa ga ruwa ya sha ba renawa.
48. ‘S’ ma na zuwa a kalmomi jere,
Sara, samfuri, sukar sa
sassare,
Sura, safiya, sigari ga
sure,
Sambo, Sirajo sun ka sha romon sure,
Sososo ka shan miya bai suɗewa.
49. Tattara kalma da ke da
“t” malam jero,
Teku tana da tambuwa ga kuma toro,
Telan Tumba tambaɗaɗɗe mai tsoro,
Tasar Titi an ka sa toshin
Mairo,
Ta turo akwati tebur
na azawa.
50. Ga misalin w cikin kalamai an kawo,
Waƙa, wuƙa, wuya, kuwwa, dawo,
Wayon waiwaya yana can bisa gawo,
Wawa mun ganai da wiwi bisa gawo,
Ya wuce ƙa’ida a nan sai ɗaurewa.
51. Yaro bai yini a ɗaki mai yoyo,
In ko ka ganai ka san ba
shi da wayo,
Bai zarce a ɗau zani ai mai
goyo,
Wayo
na ga yara manya wuce goyo
Gayu, wa ka
bar su baya ga wayewa?
52. Zakari da Zoro
yau wurin zikiri za su,
Zazzage-zazzagen gaba
babu irinsu,
Zabure-zaburensu ya wuce sa’arsu,
Zanka zumuɗi zuwa ga tasu
ibadarsu,
Zuci ka ambaton Ilahi da dacewa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.