Haji Ummaru Ɗan Habu Getso

Kai Yara kuzo mu tai Getso..... 
Hajji Dan Habu Getso... 
Amshi.. 
Ku shirya zamutai Getso,  gun Umaru dan Habu Getso..... 
Amshi.. 
Allan daya ba shi ya gode......
Amshi...
Allah ya baka ka gode, Hajj Umaru dan Habu Getso..... 
Amshi.. 
Na Auwalu dan uwan Yaro,  Umaru dan Habu Getso... 
Amshi.. 
Getso randa na koma,  ta tabbata baka zama kauye dan mararrabar mu tai Getso..... 
Amshi.. 
Duk iya mutunen dake Getso, ko da ya zam bakauye kaf, banda Umaru dan Habu Getso.... 
Amshi.. 
Banda Umaru dan Habu Getso... 
Amshi.. 
Ga Mota tahi dubu Legas, wasu nan a Kanon Dabo, ga wasu Funtua birninmu,  duk na Umaru dan Habu Getso.......
Amshi.. 
Ina na Yaro Uban Shehu,  kamar shima in san naune.... 
Amshi... 
Alhaji Umaru dan Habu Getso... 
Amshi...
Nasan Attajiran Birni,  nasan Attajiran Kauye....
Amshi.. 
Nasan Almajiran birni,  nasan Almajirin kauye.... 
Amshi... 
Nagane ma'aikan Birni,  nagane ma'aikatan Kauye.... 
Amshi.. 
A cikin ukku wanda duk na fadi ba kamatai dan Habu Getso.... 
Amshi.. 
Ka ganshi gida yana baka, ya ganka gidanka ya baka, sai Umaru dan Habu Getso.... 
Amshi.. 
Sunan tsoho nai Abu Getso... 
Amshi.. 
Wani Yaro nata son tsoho wani kau naji yaki Babanshi... 
Amshi..
Ga wani yaro na ta son tsoho wani kau naji yaki Babanshi... 
Amshi.. 
Shi Umaru dan Habu Getso,  ya zai ki fadin Habu Getson....
Amshi.. 
Marayar gwarzo Habu Getso... 
Amshi..

RUBUTAWA:
MUBARAK JAMILU KATSINA (SCORER)

Hussaini dogo
Sarkin Yaƙi

Post a Comment

0 Comments