Hausa

    Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin WaÆ™aƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

    About Tahamisin WaÆ™aƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

    Hausa

    8.  Hausa tana cikin harasan magabata,

     Cikin tsaranta Rabbu shi ne ya É—aga ta,

    Ya sauƙaƙa laffuza da tsarin harufanta,

    Kalmominta har da tsarin jimlarta,

      Ba tamka gare ta sauÆ™in ganewa.

     

    9.  Don haka nan Afirka ta zam shakundun,

     Ta haÉ“É“aka tai kama da teku ruwa kundun,

     Wasu ‘yan harsuna, su faÉ—a ciki tsundum,

     Ta yo mamaya ta zamto shakundun,

      In an ambace ta ba mai motsawa.

     

    10. Ta bunƙasa ta zamo harshe babba,

     Wannan nahiya kusan ba wani babba,

     Ba lungun da Hausa ba ta kutsa ba,

     Kai har Chana yanzu ni ban É—ebe ba,

      Ta shiga duniya ga tsarin sadarwa.

     

    11. Gun nazari ku lura nan taf fi fitowa,

     An yo digiri cikinta sun wuce Æ™irgawa,

     Ana nazarinta har Æ™asashen Turawa,

     Ga ta da maluma suna ilmantarwa,

    Masana sun yaba da Hausa ga koyarwa.

     

    12. Masana harsuna tuni sun ka amince,

     Sun daddale ta har sun Æ™wanÆ™wance,

     Sun yarje ma Hausa ikon Allah ce,

     Ta haÉ“É“aka duniya abin ai ta kwatance,

      Babu kamar ta yaÉ—uwa mai dogewa.

     

    13. Ga ta da hanƙurin wuya ga kutsawa,

     Al’adunta na da tsarin burgewa,

     Gun adabinta nan ake ilimantarwa,

     Ga harshenta na da sauÆ™in kamawa,

      In aka zo fagen aro ta fi Æ™warewa.

     

    14. Ta dai mamaye Afirka da gefenta,

     Kai ka ce wutar da daji taka rurinta,

     Haka taka mamayar harasan gefenta,

     Har ma Æ™etare tana baje kolinta,

      Ta yi barazana ga harshen Turawa.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.