Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.
Haɗuwar Baƙi da Wasula
25. A karatu na Hausa ai sai da baƙaƙe,
Yanzu mu je ga yadda ke
yi
masu sarƙe,
An yi baƙi, akwai wasal nan ya tuƙaƙe,
Sa natsuwa a yanzu zan ɗauko baƙaƙe,
Mu yi wasali gare su domin furtawa.
26. A, i, o, u, da
e(n) ga dai mun gane su,
Yanzu baƙi na ‘b’ a ɗauko mu kasa su,
Ba, bi, bo, da bu, da be, ka ji ajinsu,
Haka “c” za a sa ta bi
su a tsarinsu,
Ca, ci, co, da cu, da ce, dinga kulawa.
27. “D” na nan mu ɗora sautim wasulan nan,
Da, di, do, da du, da de, daidai ke nan,
To a riƙe rubuce har furucin
wannan,
Shi kuwa ‘f’ idan ya goyo wasulan nan,
Fa, fi, fo, da fu, da fe, sai ferewa.
28. Kun ga akwai baƙi na ‘g’ in mun
waiga,
In dai munka sa wasullanmu ga shi g(a),
Ga, gi, go, da gu, da ge, gara hakan ga,
“H” ke bin baƙi na “g” gun tsarin ga,
Ha, hi, ho, da hu, da he, iya zanawa.
29. Kallamu, kaka, kakalen kolon keke,
Ka, ki, ko da ku, da ke, ba kekeke,
Labari ya zo garan yau
nan take-
Labbo da Ladi yanzu sun zo da
azakke,
La, li, lo, da lu, da le, sai lulawa.
30. Sa wasula guda biyar kan sautin “j(a)”
Ja, ji, jo, da ju, da je, ba ja-in-ja,
Jaji, a can nag ga soja
jere da aiki ja,
Maye mai kwaɗai da idonsa kamar
manja
Ma, mi, mo, da mu, da
me, ba damewa.
31. Kan tsarin ga yanzu in dai kun lura,
An tsara baƙi akwai wasulan kara,
Na, ni, no, da nu, da ne, Nana a lura,
“R” na nan gabanta sa
wasali tura,
Ra, ri, ro da ru, da re, sai rerawa.
32. Tsarin nan a nau gani mun yo sabo,
Za mu sako baƙi na ‘s’ mu ga nasa
rabo,
Sa, si, so, da su, da se,
sai mai sabo,
Sautin “t” ya bi su ga
daɗin tarbo,
Ta, ti, to, da tu, da te, sai tarawa.
33. Wawa da wawiya ba wayewa,
Gun wauta da ɗimuwa sai zurmawa.
Wa, wi, wo, da wu, da we, ba wahalarwa,
Yaro ya yi yunƙuri don miƙewa,
Ya, yi, yo da yu, da ye, aka yayowa.
34. Zanka kula a ko’ina za ka yi zage,
In ka ga an sako baƙaƙe, to rege,
Saitin za ya zo a ƙarshe bari hange.
Za, zi, zo, da zu, da ze, zabura zage-
Dantse don ka hardace
ba wahalarwa.
35. Ka ga haɗin baƙi, wasulla ga
zubinsu,
Baƙaƙe Ƙi-jima ne a kai ta
misalinsu,
Sai wasulla da sunka
ciccika sautinsu,
Kalma ba ta zaunuwa sai in ga su,
Daɗa sai yunƙurin haɗawa, zanawa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.