Ticker

Hukuncin Ɗaukar Hoto

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, Malam, don Allaah kar ka gaji: Hukuncin ɗaukar hoto nake tambaya a kansa.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatu

Tun tuni malamai suke ta maganganu da wallafe-wallafe a kan nau’ukan hotuna da matsayinsu da yanayinsu da sauran hukunce-hukuncensu.

Manyan malaman Ahlus-Sunnah Salafiyyah a wannan zamanin kamar su: As-Shaikh Al-Allaamah Ibn Baaz (Rahimahul Laah) da As-Shaikh Al-Faqeeh Ibn Uthaimeen (Rahimahul Laah) da makamantansu duk sun yi maganganu a cikin fatawoyinsu da darussansu kan wannan mas’alar da ta zama ruwan-dare a wannan zamanin. A nan bari in kawo taƙaitaccen bayanin da As-Shaikh Al-Mujaddid Al-Albaaniy (Rahimahul Laah) ya yi a kan haka, a ƙarƙashin wani hadisi sahihi marfui zuwa ga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) wanda ya ce:

أَتَانِي جِبْرِيلُ - عَلَيْهِ السَّلَامُ - فَقَالَ : إِنِّي كُنْتُ أَتَيْتُكَ اللَّيْلَةَ ، فَلَمْ يَمْنَعْنِي أَنْ أَدْخُلَ عَلَيْكَ الْبَيْتَ الَّذِي أَنْتَ فِيهِ ، إِلَّا أَنَّهُ كَانَ فِي الْبَيْتِ تِمْثَالُ رَجُل ، وَ كَانَ فِي الْبَيْتِ قِرَامٌ سِتْرٌ فِيهِ تَمَاثِيلُ ، فَمُرْ بِرَأْسِ التِّمْثَالِ يُقْطَعُ فَيَصِيرُ كَهَيْئَةِ الشَّجَرَةِ ، وَمُرْ بِالسِّتَرِ يُقْطَعُ .

وَفِي رِوَايَةٍ : إِنَّ فِي الْبَيْتِ سِتْراً فِي الْحَائِطِ فِيهِ تَمَاثِيلُ ، فَاقْطَعُوا رُءُوسَهَا فَاجْعَلُوهَا بِسَاطاً أَوْ وَسَائِدَ فَأَوْطِئُوهُ ، فَإِنَّا لَا نَدْخُلُ بَيْتاً فِيهِ تَمَاثِيلُ . فَيُجْعَلُ مِنْهُ وِسَادَتَانِ تُوطَآنِ ، وَمُرْ بِالْكَلْبِ فَيُخْرَجُ .

فَفَعَلَ - رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - وَإِذَا الْكَلْبُ جِرْوٌكَانَ لِلْحَسَنِ وَالْحُسَيْنِ - عَلَيْهِمَا السَّلَامُ - تَحْتَ نَضِدٍ لَهُمَا . قَالَ : وَمَا زَالَ يُوصِينِي بِالْجَارِحَتَّى ظَنَنْتُ أَوْ رَأَيْتُ أَنَّهُ سَيُورِثُهُ .

Mala’ika Jibril (Alaihis Salaam) ya zo mini, ya ce: Haƙiƙa! Na zo wurinka jiya da dare, amma babu abin da ya hana ni shiga cikin gidan da ka ke, sai dai kasantuwar akwai wani mutum-mutumi a cikin gidan, kuma a cikin gidan akwai labule mai hotuna a jikinsa! Don haka, ka yi umurni a yanke kan mutum-mutumin har ya zama kamar surar bishiya, haka kuma labulen shi ma a yanke shi.

A wata riwaya ya ce:

Haƙiƙa! A cikin gidan akwai labule a jikin bango mai ɗauke da hotuna a jikinsa, ku yanke kawunansu ku mayar da su shimfiɗu ko matasan-kai a riƙa takawa ko kwanciya a kansu. Domin mu ba mu shiga duk gidan da akwai hotuna a cikinsa. Sai aka mayar da shi matasan-kai guda biyu ana kwanciya ko kishingiɗa a kansu. Kuma ka yi umurni a fitar da karen.

Sai kuwa Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya aikata haka. Sai kuwa aka ga wani ɗan kwikuyo na su Hasan da Husain (Radiyal Lahu Anhumaa) a ƙarƙashin wani gadonsu. Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce: Kuma Jibril (Alaihis Salaam) bai gushe ba yana yi mini wasiyya game da maƙwabci har sai da na yi zato ko kuma na yi tsammanin zai sanya shi mai gado.  (Silsilah Saheehah: 356).

Bayan wannan sai shehun malami mujaddidin wannan zamanin ya bayyana irin ilimin fiqhun da ke cikin wannan hadisin:

[1] Ya nuna haramcin ajiye hotuna, domin su ne dalilin hana mala’iku shiga cikin gidaje. Kuma hadisai da suka zo a kan haka sun fi ƙarfin a lissafe su.

[2] Wannan haramcin ya haɗa da hotunan da ba su da jiki ko kuma marasa inuwa, saboda gamammen maganar Mala’ika Jibril (Alaihis Salaam) cewa: ‘Domin mu ba mu shiga duk gidan da akwai hotuna a cikinsa.’ Kuma abin da zai ƙara ƙarfafarsa shi ne: Hotunan da su ke jikin labulen ai ba su da inuwa!

[3] Kuma babu bambanci a cikin wannan ko ɗinka hoton da zare a ka yi a cikin tufar, ko kuwa zanawa ne aka yi a kan takarda, ko kuma an ɗauke shi ne da na’urar ɗaukan hoto na zamani. Domin dukkan wannan sunansu ɗaya: Hoto ne kuma yin hoto ne.

(Ta amfani da kyamara mara motsi da aka saba, ko kuma da kyamarar bidiyo, duk dai ɗaya ne).

[4] Sannan bambantawa a tsakanin hoton da aka zana da hannu da kuma wanda aka ɗauka da na’ura ɗaukan hoto, har a haramta na-farkon ban da na-biyun wannan wata sabuwar mazhabar Zahiriyyah ce, kuma daskarewa ne a kan abin da bai zama godadde ba.

[5] Wannan haramcin ya haɗa har da hoton da ake takawa ana wulaƙantawa, idan dai aka bar shi a kan halinsa ba tare da an sauya shi ta yage shi ko yanke shi ba. Wannan kuwa shi ne abin da Al-Haafiz a cikin Al-Fat-hu ya karkata gare shi.

[6] Maganarsa cewa: ‘har ya zama kamar surar bishiya’ dalili ne a kan cewa: Sauya suran hoton da ya ke halatta yin amfani da hoton ita ce sauyawar da ta shafi dukkan hoton, kuma ya sauya shi har ya koma wata surar abin da aka halatta, kamar bishiya.

[7] A ƙarƙashin wannan, bai halatta a yi amfani da hoto ba don kawai an mayar da shi wata surar da ba zai yiwu ya iya rayuwa ba ne in da a ƙaddara cewa rayayye ne, kamar yadda wasu malaman fiqhu suke faɗi. Domin dai har yanzu bai rabu da matsayinsa na hoto a suna da hakikaninsa ba, kamar dai cartoon da makamantansu.

[8] Ya dace ƙwarai da gaske ka san wannan, domin yana daga cikin muhimmin abin da musulmi yake son sanin hukuncinsa a wannan zamanin, wanda hotuna suka yawaita kuma suka game koina a cikinsa. Idan kana son ƙarin bayani da tattake wuri a kan wannan, sai ka koma littafin Adabuz Zifaaf Fee Sunnatil Mutahharah.  

[9] A cikin wannan hadisin akwai nuni ga cewa: Idan hoto ya zama na abubuwa marasa rai ne to ya halatta, kuma ba ya hana mala’iku shiga gida, saboda maganarsa: ‘Kamar surar bishiya.’ Domin in da yin hoton bishiya haram ne kamar hotunan abubuwa masu rai to da mala’ika Jibril (Alaihis Salaam) bai yi umurni da a mayar da hotan zuwa da surar bishiya ba. Wannan dai a fili ya ke. Kuma hadisin Ibn Abbas (Radiyal Laahu Anhumaa) zai ƙarfafe shi, inda ya ce:

وَإِنْ كُنْتَ لَا بُدَّ فَاعِلاً ،  فَاصْنَعِ الشَّجَرَةَ ، وَمَا لَا نَفْسَ لَهُ

Kuma idan ya zama maka dole, to sai ka yi hoton bishiya ko duk wani abin da ba shi da rai.

 (Muslim da Ahmad suka riwaito shi)

[10] Haka kuma hoto idan ya zama na-halal to shi ma dai ba ya hana mala’iku shiga gida, saboda ga A’ishah (Radiyal Laahu Anhaa) ta kasance tana da ’yar bebinta na wasa, tana wasa da su tare da ƙawayenta a kan idon Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) kuma bai hana ta ba, kamar yadda ya tabbata a cikin Sahih Al-Bukhaariy da sauransu. In da wannan irin hoton yana hana malaiku shiga, to da kuwa bai tabbatar da ita a kan hakan ba. Wallahu A'alam

[11] Sannan a ƙarshen bayaninsa a kan wannan masalar a cikin Adabuz Zifaaf (shafi: 194) ya nuna cewa: Ko da muka ɗauki mazhabar cewa hoto da dukkan nau’ukansa haram ne kuma muka kafe a kan haka, to sai dai fa ba mu ganin laifin yin hotunan da suka zama suna da wata fa’ida tabbatacciya, wadda babu wata cutarwa da ke tattare da ita, kuma wadda wannan fa’idar ba za ta samu ta wata hanyar da asalinta ya ke halal ba. Misali a nan kamar hotunan da ake buƙatarsu a fannin likitanci ko a wasu fannonin ilimi a makarantu, ko wanda ake amfani da su don a iya kamo masu laifi, ko a tsoratar da jamaa a kansu.

(Haka kuma hotunan da ake amfani da su wurin karantar da ɗalibai a cikin azuzuwa ko a cikin littaffai da kalandun da ake ratayawa a bangaye, masu motsi da marasa motsi. Kamar kuma hotunan passport don shiga ƙasashe da wuraren ayyuka iri-iri, da katin zama ɗan-ƙasa da na buɗe asusun ajiya a bankuna, da lasin mallakan gidaje ko filaye ko abubuwan hawa da sauransu, da katin zaɓe da na asibiti da sauran irinsu, duk sun halatta saboda fa’idojinsu da kuma abin da rashin yin su zai haifar na wahalhalu da ƙunci a cikin rayuwar musulmi).

[12] Kai amfani da wasu nau’ukan hotuna ma kan iya zama wajibi a wasu lokutan. Kamar hadisin wasan da A’ishah Ummul-Mu’mineen take yi da ’yar bebinta. Fa’idar wannan don manufar koyon aikin reno da tarbiyyar ’ya’ya ne wanda yake wajaba a kan mace bayan ta girma, shi ne shari’a ta amince ta fara koyon wannan tun tana ƙarama.

(Wannan hadisi ma’anarsa a fili ya ke, in shã Allãh. Ƙananan yaran mata ne suke wasanni da irin waɗannan kayan wasannin da suka haɗa da hotunan abubuwa masu rai, kamar ’yan jarirai da sauransu. Amma irin abin da ake gani yanzu yadda wasu manya mata baligai suke kwana da teddy a gadajensu, wannan ba shi da wata fa’ida, koyi ne kawai da waɗanda ba musulmi ba. Sai a kiyaye.

Sannan a nan wasu malamai ke ganin halaccin ɗaukar hotunan bidiyo na manyan malamai domin manufar yaɗa karantarwa da koyar da ilimi a cikin al’umma na-kusa da na-nesa. Wasu malaman kuma suna ganin rashin halaccin hakan saboda wasu dalilan da suka dogara a kansu. Amma abu ne sananne a wurin kusan kowa, ba wai masana kaɗai ba cewa: Amfani da hotuna tsayayyu da masu motsi a wurin koyarwa ya fi sauƙi kuma ya fi saurin isar da saƙo ga ɗalibai, in shã Allãh ).

[13] Amma hotunan da ba su da wata fa’ida a addinance ko a duniyance, sai dai kawai koyi da kafirai masu bautar gumaka, waɗannan irin hotunan suna nan a matsayinsu na haramci, kamar hotunan shehunnai da shugabanni da manyan mutane, da abokai da makamantansu.

(Haka kuma kamar hotunan da ake ɗauka a wurin bukukuwan ɗaurin aure da zanen suna da na ƙarin girma ko na cin zaɓe da sauran bukukuwan fasiƙanci da saɓon Allaah, da hotunan wasanni da fima-fiman barkwanci da soyayya da yaudara da kaɗe-kaɗe da raye-raye da waƙe-waƙe da sace-sace da faɗace-faɗace da sihirce-sihirce da sauransu, duk waɗannan suna nan a asalinsu na haramci. Duk kuwa da da’awar da masu yinsu suke yi kullum cewa wai suna ƙoƙarin faɗakarwa ko wayarwa ko fahimtarwa ne.

Allaah ya kyauta). 

Domin neman ƙarin bayani da mayar da martani da waɗanda suka zame ko suka kauce wa ƙaida a wannan babin sai a duba: Adabuz Zifaaf, shafi: 161-165, 175-179.

Allaah ya ƙara mana dacewa a cikin ilimi da magana da aiki.

 WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments