𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum, ya Shaikh. Allaah ya saka maka da alkhairi a kan faɗakar da jama’a da kake yi. Malam, don Allaah wasu shubuhohi (rikice-rikice) ne ke damu na, waɗanda kuma nake so don Allaah, ka taimake ni ka warware mini da irin ilimin da Allaah ya ba ka. Shubohohin nan su ne: A kan cika gemu da kuma ɗage wando. Shin malam wajibi ne ko kuma dai
Sunnah ne?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatu
Da farko, ma’anar kalmar: ‘WAJIBI’ a wurin malaman
Usuul ita ce: Abin da Shari’a ta nemi a aikata nema mai ƙarfi, ta yadda duk
musulmin da ya aikata shi yana da lada, idan kuma bai aikata ba yana da alƙawarin
azaba ko uƙuba a Lahira.
A ƙasa da Wajibi kuma akwai ‘MANDUBI’, watau abin da aka nemi a aikata amma
nema mara-ƙarfi, ta yadda duk wanda ya aikata yana da lada, wanda kuma bai aikata ba,
ba za a ce yana da alƙawarin wata azaba ko uƙuba ba, sai dai kawai ya
yi asarar wannan ladan.
A wurin waɗansu malaman kuma sun ƙara da: ‘SUNNAH’ a tsakanin WAJIBI da MANDUBI, wadda suka
raba ta gida biyu: ‘SUNNAH MU’AKKADA’ wadda suka ce ta yi kusa da WAJIBI, da
kuma ‘SUNNAH MUSTAHABBIYA’ wacce ta yi kusa ko daidai da MANDUBI.
Akwai lokutan da Malamai suke amfani da kalmar
‘SUNNAH’ da wata ma’anar da ba wannan ba, kamar inda suke cewa: ‘Aure Sunnah
ne’, ko ‘Aje gemu Sunnah ne’, ko ‘Sunnah ne ɗage wando sama da idon-sawu’, da sauransu.
Abin nufi da Sunnah a irin wannan wurin shi ne:
Abin da Annabi (Sallal Laahu AlaihiWa Alihi Wa Sallam) ya gudana a kansa wurin
karantarwa da fassara saƙon addinin da Allaah ya aiko shi da shi. Don haka,
a irin wannan wurin ba ana nufin bayyana hukuncin shari’a ba ne. illa dai kawai
bayani a kan cewa, wannan abin yana daga cikin koyarwar addinin Annabi (Sallal
Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam).
Ana gane hukuncin abu cewa wajibi ne daga irin
yadda Shari’a ta ɗauke
shi, kamar idan Allaah (Subhaanahu Wa Ta’aala) ko Annabi (Sallal Laahu Alaihi
Wa Alihi Wa Sallam) ya yi umurni da aikata shi, in dai ba an samu wani dalili
ne da ya mayar da umurnin ya koma na mustahabbi ba, kamar inda Allaah ya ce:
وَأَقِيمُوا الصَّلَاةَ وَءَاتُوا الزَّكَاةَ
Kuma ku tsai da Sallah kuma ku ba da Zakkah
Kamar haka, aka gano hukuncin ‘Cika Gemu’ cewa
Wajibi ne, ba Sunnah ko Mandubi ba daga maganganun da Manzon Allaah (Sallal
Laahu AlaihiWa Alihi Wa Sallam) ya yi a kansa, kamar inda ya ce:
خَالَفُوا الْمُشْرِكِينَ، أَعْفُوا اللِّحَى، وَأَعْفُوا الشَّوَارِبَ
Ku saɓa wa
mushirikai: Ku cika gemu, kuma ku rage gashin-baki.
A nan, dayake ba a samu wani dalili sahihi kuma
sarihi da ya rage wa wannan umurni na cika-gemu ƙarfi, ya mayar da shi na
mustahabbi ba, kuma dayake ba a samu shi kansa Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa
Alihi Wa Sallam) ko wani daga cikin Sahabbansa _(Radiyal Laahu Anhum) ya aske,
ko ya sassabe gemunsa irin yadda waɗansu musulmai suke yi a yau ba. Shi ya sa Malamai
suka ɗauke
shi a matsayinsa na asali, watau Wajibi, ba Sunnah ko Mustahabbi ba.
Shi kuwa ɗage wando sama da idon-sawu ya zama wajibi ne
saboda hanin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi a kan
sakin wandon zuwa ƙasa da idon-sawu a cikin hadisai sahihai sarihai,
kamar maganarsa:
مَا أَسْفَلَ مِنَ الْكَعَبَيْنِ مِنَ الْعَزَارِ فَفِي النَّارِ
Duk abin da ya yi ƙasa da idon-sawu na tufa
yana cikin wuta.
A nan, tun da ya yi alƙawarin shiga wuta a kan
sakin tufa ƙasa da idon-sawu wannan
nuna aikata
hakan haram ne. Kuma abu ne sananne cewa nisantar aikata haram wajibi ne, ba
Sunnah ko Mustahabbi ba.
Wannan ya sa manyan Malamai suka ce: Tsawaita
kowace irin tufa ta namiji musulmi, kamar wando ko riga ko alkyabba ko rawani
da sauransu zuwa ƙasa da idon-sawu yana cikin manyan kaba’irai, kamar yadda Al-Imaam Al-Haafiz
Shamsuddeen Az-Zahabiy (Rahimahul Laah) ya yi a cikin Littafinsa: Al-Kabaa’ir.
Amma fa wannan ga maza ne kawai. Su kuwa mata
wajibinsu shi ne: Su rufe dukkan ƙafafunsu da zannuwa ko riguna da sauransu, har sai
sun sauka a kan ƙasa. Kai! Har ma sai sun ja su a kan ƙasar,
kamar yadda Hadisai Sahihai suka bayyana.
WALLAHU
A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.