𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Malam, na
kasance idan wasanni sun auku a tsakanina da mijiina ko kuma idan tunani ya
kama ni, sai wani ruwa mai yauƙi ya riƙa fito mini, to wai sai na yi wankan
tsarki idan hakan ya faru?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa
Barakaatuh.
Abin da kike gani ɗaya ne daga cikin abubuwan da suke janyo
hadasi ga mutane idan sun fito musu:
[1] Akwai masu fitowa daga kowane irin mutum
namiji ko mace, kuma babba ko ƙaramin yaro, su ne: Tusa da kashi da suke fitowa
ta dubura. Fitsari wanda ke fitowa ta gaba. Hukuncinsu: Kowannensu najasa ne.
Dole ne a wanke inda suka fito kawai, a sake alwala. Wurin da suka shafa kuma
dole sai an wanke shi da ruwa mai tsarki mai tsarkakewa. Sai dai fitsarin
jariri a kan tufa, shi ba sai an wanke ba. Idan aka jiƙa tufar da ruwa kawai ya
wadatar.
[2] Sai kuma waɗanda suke fitowa daga manyan mutanen da
suka balaga, su ne: Wadiyyi da maziyyi da maniyyi.
WADIYYI: Ruwa ne fari mai kauri da yake fitowa
yawanci a ƙarshen fitsari. Kuma yana fitowa yawanci daga tsofaffi ne. Hukuncinsa iri ɗaya da na fitsari ne: A wanke inda ya fito
da inda ya taɓa
kawai, a sake alwala.
MAZIYYI: Ruwa ne tsararo mai yauƙi,
yana fitowa a lokacin ƙaramar sha’awa, kamar a lokacin tunani a kan sha’anin jima’i, ko
kallon sha’awa ga
al’aurori, ko wasannin sha’awa a tsakanin miji da mata. Ba ya tunkuɗar juna wurin fitowarsa, yawanci ba a ma
ji ko sanin fitowarsa sai dai a ga jiƙewa kawai. Hukuncinsa shi ne: Shi najasa
ne, don haka sai a wanke duk inda ya shafa da dukkan al’aurar da ya fito daga
cikinta, sannan kuma a sake alwala. Idan ya shafi tufafin matasa an yi sassauci
cewa a jiƙa wurin da ruwa kawai maimakon wankewa.
MANIYYI: Ruwa ne fari mai kauri (a wurin namiji),
yana tunkuɗar
juna a lokacin fitowarsa, kuma yana janyo sakewar jiki bayan fitowarsa. Yana
fitowa ne a lokacin babbar sha’awa, kamar a lokacin saduwar jima’i, ko wasa da
gaba (istimna’i). Yakan fito a cikin barci kamar yadda yake fitowa a farke.
Hukuncinsa: Ba najasa ba ne a maganar da ta fi ƙarfi a wurin malamai.
Amma kuma yana wajabta yin wankan da ake kira wankan janaba a bayan fitowarsa.
[3] Akwai kuma waɗanda suke fitowa ta gaban manyan mata kaɗai su ne: Haila da nafasi da kuma
istihala.
HAILA: Jini ne da yakan fita daga gaban mace a
lokacin da ta balaga, ba don wani dalili na rashin lafiya ko wata larura ba.
Jini ne na al’ada, wanda ba shi da wani iyakantaccen adadi ta fuska yawa ko
kwanaki. Yana maimaita fitowa yawanci a kowane wata guda ne. Hukuncinsa: Mai
haila ba za ta yi sallah ba, ba za ta yi azumi ba, ba za ta yi ɗawafi ba, ba za a sadu da ita ba, kuma ba
za a sake ta ba. Bayan ɗaukewarsa
wajibi ne ta yi wankan da ake kira wankan haila. Tana rama azumman da ba ta yi
ba a lokacinsa, amma ba za ta rama sallolin ba.
NIFASI: Jini ne da ke fitowa saboda dalilin
haihuwa, Mafi yawan kwanakinsa kwana arba’in ne saboda hadisi sahihi da ya zo a
kan haka. Don haka, idan ya kai kwana arba’in sai mace ta yi wanka, ta cigaba
da sallah, da sauran ayyukan ibada. Haka ma idan ya ɗauke kafin cikan kwanaki arba’in ɗin. Hukuncinsa daidai da haila ne.
ISTIHAALA: Jini ne da yakan fita a dalilin wata
matsala ta rashin lafiya a cikin mace. Yakan zama ya karu a kan adadin
kwanankin haila a wurin mace. Hukuncinsa: Ba ya hana komai daga cikin abubuwan
da haila ko nifasi ke hanawa. Sai dai dole ne mai Istihaala ta sake alwala ga
kowace sallah. Kuma tana iya yin wanka ta haɗa salloli biyu da suka haɗa lokaci: Azahar da La’asar ko Maghriba da
Isha’.
[4] Daga cikin waɗannan matsalolin, duk wanda ya janyo wanka
kafin a samu tsarki, kamar fitar maniyyi ko haila ko nifasi, shi ne ake kira:
Babban
kuma Wanda kuma ya janyo alwala, kamar fitar
fitsari ko kashi ko maziyyi da sauransu shi ne: Ƙaramin Hadasi.
[5] Kuma waɗannan abubuwa suna zama hadasi ne kaɗai idan sun fito ta fuskar lafiya ta
hanyar da aka saba, amma duk lokacin da suka fito ta fuskar rashin lafiya,
kamar idan suka wuce iyaka a wurin yawa da lokacin fitarsu, to sun zama larura.
Kuma ba za su hana komai ba na sallah ko azumi ko ɗawafi da sauransu.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.