𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah.
Duk lokacin da na je yin sujada sai na ga mai shigowa daga bayana saboda bangon akwai tiles. To ko wannan ya yi kamar mai waiwaye a cikin sallah? Mene ne hukuncin sallata?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa
Barakaatuh.
Al-Imaam Al-Bukhaariy ya riwaito daga
Ummul-Mu’mineen A’ishah (Radiyal Laahu Anhaa) cewa: An tambayi Manzon Allaah
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a kan waiwaye a cikin sallah sai ya
ce:
هُوَ اخْتِلَاسٌ يَخْتَلِسُهُ الشَّيْطَانُ مِنْ صَلَاةِ الْعَبْدِ
Sata ce da sheɗan yake sacewa daga sallar bawa. (Sahih
Al-Bukhaariy: 709)
Wannan dalili ne a kan cewa waiwaye a cikin sallah
makaruhi ne, abin ƙyama tun da yana rage natsuwa da ƙanƙan-da-kai
ga Allaah. Haka ma kallon duk wani abin da ka iya ɗauke hankali daga cikin sallah, kamar
kallon hoton mai wucewa ko mai zuwa ta cikin madubi ko TV da sauransu.
Haka kuma Al-Bukhaariy ya sake riwaito hadisi daga
gare ta (Radiyal Laahu Anhaa) cewa: Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi
Wa Sallam) ya yi sallah a cikin wata riga mai alamu a jikinta, sai kuwa ya yi
kallo guda ga alamun, da ya yi sallama sai ya ce:
« اذْهَبُوا بِخَمِيصَتِى هَذِهِ إِلَى أَبِى جَهْمٍ وَائْتُونِى بِأَنْبِجَانِيَّةِ أَبِى جَهْمٍ ، فَإِنَّهَا أَلْهَتْنِى آنِفًا عَنْ صَلاَتِى »
Ku kai wa Abu-Jahmin wannan rigar, ku karɓo min ambijaaniyar Abu-Jahmin, domin ta ɗauke min hankali ɗazun nan a cikin sallata. (Sahih
Al-Bukhaariy: 373)
(Ambijaaniyyah riga ce mai kauri mara alamu ko
hotuna).
A kan haka Al-Imaam An-Nawawiy (Rahimahul Laah) ya
ce:
واَمَّا الثَّوْبُ الَّذِى فِيهِ صُوَرٌ أَوْ صَلِيبٌ أَوْ مَا يُلْهِي فَتُكْرَهُ الصَّلَاةُ فِيهِ وَاِلَيْهِ وَعَلَيْهِ لِلْحَدِيثِ
Amma tufar da a jikinta akwai hoto ko gicciye
(cross) ko duk wani abin da ke ɗauke
hankali, to makaruhi ne a yi sallah a cikinta ko in tana gaba ko kuma a kan ta,
saboda wannan hadisin. (Al-Majmuu’u Sharhul Muhazzab: 3/180).
Shi kuma Al-Haafiz Ibn Hajr (Rahimahul Laah) ya
ce:
وَيُسْتَنْبَطُ مِنْهُ كَرَاهِيَةُ كُلِّ مَا يُشْغِلُ عَنِ الصَّلَاةِ مِنَ الْأَصْبَاغِ وَالنُّقُوشِ وَنَحْوِهَا
Daga wannan hadisin ne aka zaƙulo karhancin duk wani
abin da ke ɗauke
hankali a cikin sallah kamar launuka da zane-zane da makamantansu. (Fat-hul
Baariy: 1/483).
A kan hadisin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa
Alihi Wa Sallam) ya yi sallah alhali labule mai hotuna yana a gabansa, kuma ya
umurci A’ishah (Radiyal Laahu Anhaa) da ta kawar da shi (labulen) saboda
hotunan jikinsa sun riƙa gitto masa a cikin sallarsa, sai Ibn Hajr
(Rahimahul Laah) ya ce:
وَهَذَا تَشْرِيعٌ وَإِذَا كَانَتِ الصُّوَرُ تُلْهِي الْمُصَلِّي وَهِيَ مُقَابِلُهُ فَأَوْلَى إذِاَ كَانَ لَابِسَهَا
Wannan ita ce shari’ar haka kuma idan hotunan suna
ɗauke hankalin mai sallah
a halin suna a gabansa, to ina kuma idan yana sanye da su ne?! (Irshaadus
Saariy: 8/484)
Daga waɗannan bayanan ya fito fili cewa ɗaga kai da kallon hoton mai wucewa a cikin
bangon tiles bai halatta ba, makaruhi ne.
Amma abin da ya kamata, idan ba a iya kawar da
hoton, kamar ta hanyar rufe shi ko lulluɓe shi, sai ya nisanci ɗaga kansa domin kallon hoton. Ya kula da
yin aiki da abin da malamai suka nuna, watau ya sunkuyar da kansa zuwa ƙasa
kawai. Saboda hadisin A’ishah (Radiyal Laahu Anhaa) cewa
« دَخَلَ رَسُولُ اللَّهِ - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - الْكَعْبَةَ مَا خَلَفَ بَصَرُهُ مَوْضِعَ سُجُودِهِ حَتَّى خَرَجَ مِنْهَا »
Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam) ya shiga Ka’abah, kuma idanunsa ba su kauce daga wurin sujadarsa ba har
ya fita daga cikinta. (Al-Mustadrak: 1/652).
Wal Laahu A’lam.
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.