Hukuncin Mace Ta Fito Da Nononta Waje A Gaban Muharramanta Don Ta Shayar Da Jaririnta

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Shin ko ya halatta mace ta shayar da Ɗanta nono a gaban Muharramanta? Sannan ina ne ya ke iya zama tsiraicin mace a wajen muharramanta?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Dangane da hukuncin mace ta fito da nononta waje a gaban muharramanta don ta shayar da Ɗanta, an samu maganganu kamar guda uku na Malamai a game da saɓanin da suka yi dangane da cewa ina ne iyakar tsiraicin 'ya mace a gaban muharramanta kamar

    Ɗanta

    Babanta

    Ɗan-Mijinta

    Ɗan'uwanta

    Ɗan kaninta

    Ɗan yayanta

    1. Ƙauli na farko shi ne, abinda Mazhabin Malikiyya da kuma Hanabila suka tafi a kansa cewa tsiraicin mace a gaban muharramanta ya game dukkan jikinta ne amma banda fuskarta, hannayenta, kafafuwanta, da kuma gashin kanta. Amma ba ya halatta a gareta ta bayyanar da kirjinta ko nonuwanta a gabansu. Danhaka haramun ne muharraminta ya ga kirjinta ko nonuwanta, ko da kuwa mahaifinta ne shi, sannan kuma ko da ba da nufin sha'awa ko jin daɗi ya kallaba.

    2. Ƙauli na biyu kuma shi ne, Mazhabin Hanafiyya sun tafi a kan cewa tsiraicin mace a gaban muharramanta shi ne tsakanin cibiyarta zuwa guiwowinta da cikinta da kuma bayanta. Danhaka ya halatta ya ga dukkan sauran jikinta in banda waɗancan wuraren, amma sukace da sharaɗin ya kasance an aminta da cewa babu wata fitina da a ke zaton kallon zai iya haifarwa, sannan kuma ya zama ba kallo ba ne ze yi mata irin na sha'awa, idan kuwa kallon sha'awa ne ze yi mata ko kuma ita za ta ji sha'awa ko daɗi a dalilin hakan, to haramun ne ya ga ni.

    3. Ƙauli na uku shi ne abin da Mazhabin Shafi'iyya suka tafi a kan cewa tsiraicin Mace a gaban muharramanta shi ne tsakanin cibiyarta zuwa guiwowinta kaɗai, sukace ya halatta Muharraminta ya iya ganin fuskarta, hannayenta, kafafuwanta, gashin kanta, kirjinta, nonuwanta, cikinta, da kuma bayanta. Shin muharramin nan Ɗan'uwanta ne shaƙiƙi na jini ko kuma Ɗan'uwanta ne da suka sha nono tare, duk hukuncinsu ɗaya ne.

    To amma sai dai maganar da mafi yawan Malamai sukafi rinjayar da ita ita ce,  Ƙaulin da Mazhabin MALIKIYYA suka tafi a kansa na cewa dukkan jikin mace tsiraici ne, sai dai ya halatta muharramanta su iya ganinta a yanayin da a bisa al'ada a ke iya ganin wasu wurare sukan bayyana a jikin mace idan tana yin wasu aikace-aikace irin na cikin gida.

    Wato kamar zira'in hannayenta, wuyanta, gashin kanta, da kuma Ƙafafuwanta zuwa guiwarta.

    Amma dangane da hukuncin tsiraicin Mace a gaban 'yan'uwanta Mata ko da kuwa waɗannan matan 'yan'uwanta ne na jini, wasu daga cikin Malamai sukace tsiraicin mace a gaban 'yan'uwanta mata dai-dai yake da hukuncin tsiraicinta a gaban muharramanta, danhaka sukace ba ya halatta mace ta bayyana tsiraicinta kamar cinyoyinta da nonuwanta da cikinta zuwa cibiya a gaban wasu Matan, sai dai in da wata larura mai ƙarfi, amma sai dai wasu Malaman sun tafi ne a kan cewa hukuncin tsiraicin Mace a gaban 'yan'uwanta mata dai-dai yake da hukuncin tsiraicin namiji a gaban ɗan'uwansa namiji, wato daga cibiya zuwa guiwa, to haka suma Mata a tsakaninsu daga cibiya zuwa guiwa,

    Daga ƙarshe idan mukayi duba a kan maganganun da Malamai suka yi za muga cewa magana mafi inganci ita ce haramun ne Mace ta fito da nonuwanta fili a gaban muharramanta dan ta shayar da jariri. danhaka ya zama wajibi a kanta ta san duk yadda za ta yi ta suturce nonuwanta a lokacin da ta ke shayar da Ɗanta.

    шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ

               Mυѕтαρнα Uѕмαи

                  08032531505

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.