𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum mlm tambayata ita ce, mlm idan
miji ya sadu da matarsa kuma tana shayarwa yaronta ya tashi a bacci to mlm sai
tayi wanka ta bashi nono ko zata iya bashi haka, sannan kuma wani lokacin idan
tana bashi nonon mijin yana amfani da gabanta ta baya hakan babu mtsala. Allah
ya sakawa mlm da alkhairi.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh
Al-imamul A'imma Maliku Ibn Anas Yace, Bai Kamata
ga Mace ta shayar da danta Nono Alhalin Akwai Janaba a Jikinta ba. Sabida
Wannan yaron zai sha Wannan Nonon Nata tare da Shaiɗani. Shaiɗani yana Kusantar Mutumin da yake da
Janaba a Jikinsa. Wanda kuma idan Shaiɗan ya sha Wani Abu Ko ya Ci Wani Abu tare da
Mutum, Zai cutar da shi. Musamman Yaro. Shiyasa Manzon Allah ﷺ ya ce idan ɗayanku zai Ci Abinci yayi Bismillah a
farkon Farawarsa, idan ya manta Baiyi Bismillah a Farkon Laumarsa ba, to ko da
a ta Karshe ne ya yi Bismillah. Sakamakon Rashin Yin Bismillah, yana Ci da Shaiɗani. Idan Yayi Bismillahi. Wannan Shaiɗanin zai Amayar da Abinda ya ci tare da
Wannan Mutumin da Baiyi Bismillah a karon farko wajen cin Abincinsa ba. Ko dai
yaron nan ya Haɗu da
wata Jinya, ko kuma ya dabi'antu da Dabi'u irin Na Kangarewar Shaiɗani da Sauransu.
Sabida haka Kenan sai dai tayi Wanka Ko tayi
Alwala kafin ta shayar da wannan yaron.
Zama Da
Janaba haka Kawai ba shi da Amfani. Amma dai ba Lefi bane a shari'ah Mutum ya
dan Zauna da Janaba kafin ya samu yayi Wanka na ɗan Wani Lokaci. Sabida wani Lokaci Manzon
Allah ﷺ Ya Haɗu da Abdurrahman Ibn Sakarin Addausiy
Al-yamaniy, shi ne Abihuraira a wata hanya. Sai Abu Huraira bai zo ya gaisa da
Manzon Allah ﷺ ba.
Ashe ya tafi ne yayi Wanka wanda a wannan Lokacin Akwai Janaba a jikinsa. Sai
da ya dawo sai manzon Allah ﷺ ya ce
ina ka shiga ya Abuhuraira? Sai Abuhuraira Yace, Akwai Janaba ne a Jikina, shi
ne na kyamaci Gaisawa da kai ina Cikin halin janaba. Sai manzon Allah ﷺ ya ce SUBHANALLAH AI MUMINI BA YA ZAMA
NAJASA.
Duk da Cewar Manzon Allah ﷺ ba ya gaisawa da Mutane, ba ya Maida
Sallama kuma ba ya yiwa kowa sallah idan da janaba a jikinsa. Har sai yayi
Wanka. Sannann Kuma Yana Cewa, Mala'iku ba sa Shiga Gidan da ya ke da Mai
Janaba a Jikinsa.
Allah Shi ne Masani.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/IQUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.