Hukuncin Mafarkin Saduwa

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Wanda ya yi mafarkin saduwa kuma har ya ji yanayin fitar maniyyi amma da ya farka sai bai ga maniyyi a jikinsa ba, sai tufarsa ce kawai ta jiƙe, to wai ko zai yi wankan janaba?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

    Abin da Malamai suka ce shi ne, Janaba tana samuwa ga mutum ne idan ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan ya auku:

    1. Fitar maniyyi daga gare shi ta hanyar babbar sha’awar jima’i ko a barci ta hanyar mafarki, ko kuma a farke ta hanyar tunani ko kallo ko shafan jiki ko wasanni.

    2. Ɓacewar kan alauran namiji (hashafa) a cikin na-mace kamar a lokacin saduwa ko wasan banza, ko da kuwa ba su yi maniyyi ba.

    3. Fitar maniyyi ta hanyar yin wasa da al’aura ko ta amfani da wani inji ko wata na’ura da turawa suka ƙera musamman domin haka, kamar budurwar roba.

    Duk wanda hakan ya same shi kuwa wankan janaba ne ya wajaba a kansa amma ba alwala ba, saboda maganar Ubangiji Tabaaraka Wa Ta’aala cewa:

    وَإِن كُنتُمۡ جُنُبࣰا فَٱطَّهَّرُوا۟ۚ

    Kuma idan kun kasance masu janaba, to sai ku yi wanka. (Surah Al-Maa’idah: 6)

    Sannan kuma Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya bayar da fatawa ga wanda yake yawaita wanka saboda fitar maziyyi cewa:

    « لاَ تَفْعَلْ ، إِذَا رَأَيْتَ الْمَذْىَ فَاغْسِلْ ذَكَرَكَ وَتَوَضَّأْ وُضُوءَكَ لِلصَّلاَةِ ، فَإِذَا فَضَخْتَ الْمَاءَ فَاغْتَسِلْ »

    Kar ka yi haka. Idan dai ka ga maziyyi to sai ka wanke al’aurarka kuma ka yi alwala irin alwalarka ta sallah. Idan kuma ka fitar da maniyyi mai tunkuɗowa da ƙarfi, to sai ka yi wanka. (Sahih Abi-Daawud: 206).

    Wannan da ya farka ya ga tufarsa a jike, shi ma janaba ta same shi, don haka sai ya yi wanka. Wanda Yayi Mafarki Amma Ya Tashi Bega Komai ba wato bai fitar da maniyyi ba, To Malamai Sukace Babu Komai Akansa, Bazeyi Wanka Ba.

    Allaah ya ƙara mana fahimta.

    WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.