Hukuncin Matar Da Aka Saketa Tana Cikin Haila

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum Mallam. Mace ce mijinta ya saketa tana haila. Dan Allah jini nawa zatayi ta kare iddah. Nagode.z

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

    Akwai saɓanin Malamai game da sakin da aka yishi alhali matar tana cikin jinin haila. Kasancewarsa saki ne irin na bidi'ah. Wasu 'yan kaɗan daga cikin malamai sunce sakin bai afku ba.

    Amma magana mafi karfi itace wacce mafiya rinjayen malaman musulunci suke kai. Ita ce cewarsu sakin ya afku, wato ya yiwu. Duk da cewar saki ne na bidi'ah. Acikin malaman dake kan wannan fahimtar akwai Maluman Fiqhu na Mazhabobin nan huɗu wato Imam Malik, Abu Hanifah, Imam Shafi'iy da Imamu Ahmad (Allah ya rahamshesu).

    Game da siffar yadda zatayi kirgen iddarta kuwa, shima akwai saɓanin Malamai tun daga zamanin sahabban Annabi . Wasu sun ce ana yin kirgen ne bisa adadin jini,  wasu kuma suka ce bisa adadin tsarkin da aka samu abayan zuwan jinin.

    To amma idan kika ɗauki fatawar Maluman da suka ce ana yin kirgen ne bisa adadin tsarkin da aka samu bayan jini, to zaki fara kirgen ne bayan kammala wannan jinin da kike ciki.

    WALLAHU A'ALAM.

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒��𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/JoWs3feDfdyGE9yBsa1RSC

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.