Ticker

Hukuncin Miƙewan Ɗalibai Don Gai Da Malamai

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, Malam ina muku sannu da ƙoƙari, malam ina da tambaya cikin rubutunku da kuka yi game da Martanin Mauludi , kun kawo wani hadithi:

مَنْ أَحَبَّ أَنْ يَتَمَثَّلَ لَهُ النَّاسُ قِيَاماً فَلْيَتَبَوَّأْ مَقْعَدَهُ مِنَ النَّارِ

 Duk wanda ke son mutane su miƙe masa a tsaye, to ya nemi mazauninsa a cikin Wuta.

Malam, na kasance malamar makartar boko, idan ɗalibai za su gaishe ni sai sun yi tsaye, to kenan na shiga cikin wanan hadithin ????

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

W alkm slm w rhmt laah.

1. Da farko ba za a ce kin shiga cikin Hadisin ba kai-tsaye, domin ai hadisin cewa ya yi: 'Duk wanda yake so...'

Don haka, idan dai ba kina so, ko kina sha'awar miƙewar yaran ba ne, ba za a ce kin shiga cikin Hadisin ba, in shaa'al laah.

2. Amma duk da haka, abin da ya wajaba gare ki da sauran malamai irinki shi ne: Ku hana ɗalibanku miƙewar, domin koya musu kyakkyawar ɗabi'a tun suna ƙanana, kuma da toshe kafar yaɗuwar sharri a cikin al'umma. Haka maruwaicin hadisin ya yi:

3. Asalin Hadisin, Sahabi Mai Daraja ne Mu'awiyah Bn Abi-Sufyaan (Radiyal Laahu Anhu) ya shiga wani ɗaki wanda a cikinsa ya tarar da Abdullaah Bn Az-Zubair da Abdullaah Bn Amir. Sai Ibn Amir ya miƙe domin shi, shi kuwa Ibn Az-Zubair ya tabbata a zaune, bai miƙe masa ba.

Daga nan ne sai Mu'awiyah ya ce:

 اجْلِسْ يَا ابْنَ عَامِرٍ! فَإِنّي سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ (صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَآلِهِ وَسَلَّمَ) يَقُولُ...

 Zauna, Ibn Amir! Domin na ji Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) yana cewa: ...

Sai ya ambaci Hadisin.

4. A kan haka ne As-Shaikh Al-Albaaniy (Rahimahul Laah) a cikin (Silsilah Saheehah: 1/696) inda yake fitar da fiƙhun hadisin ya ce:

Wannan hadisin ya nuna mana abubuwa guda biyu:

1. Haram ne ga wanda ya shigo wuri ya yi sha'awar mutanen da ya tarar su miƙe ma sa.

 2. Wanda ya shigo kuma aka miƙe masa, sai lallai ya ƙyamaci hakan ga mutanen da suka yi masa hakan (watau ya hana su), duk kuwa da kasancewar ba ya son miƙewar. Wannan a babin: Umarni da kyakkyawa da Hana mummunan aiki ne, kuma domin toshe dukkan ƙofar sharri... Haka maruwaicin Hadisin Mu'awiyah (Radiyal Laahu Anhu) shi da kansa ya nuna mana...

5. Amma abin da waɗansu suka yi na kafa hujja da misalin Hadisin da ya ce:

 قُومُوا إِلَى سَيِّدِكُمْ

 Ku miƙe zuwa ga shugabanku

Malaman Sunnah sun ce: Wannan ba hujja ce mai ƙarfi ba, saboda dalilai kamar haka:

A larabci: 'Ƙaama Lahu' ya sha bamban da ' Ƙaama Ilaihi.'

A lokacin da na-farko ke nuna ya miƙe ne, kuma ya tsaya a matsayinsa don girmama shi, na-biyun nuni yake ga cewa, ya miƙe ne tsaye kuma ya taka zuwa gare shi domin taimaka masa, ko don wani abu dai, misali.

Shi ya sa wannan hadisin da suka jawo ya zo da ƙarin bayani a ƙarshensa mai nuna manufarsa, Watau cewa:

 فَأَنْزِلُوهُ

 Ku sauke shi

Malaman Hadisi da Tarihi sun san cewa wannan maganar ta auku ne a lokacin da aka kira Sahabi Sa'ad (Radiyal Laahu Anhu) da ba shi da lafiya don ya yanke hukunci a kan Yahudawa. Da ya zo a kan abin hawarsa shi ne Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya faɗa wa Lansarawa:

 قُومُوا إِلَى سَيِّدِكُمْ ، فَأَنْزِلُوهُ

 Ku tashi ga shugabanku, ku sauke shi.

Wannan ya nuna ashe ba maganar tsayawa a wuri guda don girmamawa Hadisin yake yi, irin yadda ake yi wa shugabanni a yau ba.

A taƙaice dai, ba daidai ba ne a riƙa miƙewa tsaye don girmama wani mutum, saboda wannan Hadisin Sahihi.

Amma kuma kowane mutum yana aiki da abin da ya sani na Ilimi ne, da gwargwadon ikonsa da kuma yanayi ko halin da yake ciki.

Allaah Ta'aala ya ce:

 فَاتَّقُوا اللهَ مَااسْتَطَعْتُمْ

 Ku bi Allaah da taƙawa da gwargwadon iyawarku.

Wal Laahu A'lam

Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy

 Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments