Hukuncin Ɓoye Kayan Kasuwanci Har Zuwa Lokacin Tsadarsa

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum. Shin ya halatta mutum ya sayi kaya lokacin da take araha idan ya yi tsada ya fitar ya saida dan ya samu riba?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam. Mutum ya Saye kaya ya ɓoye shi sai bayan wani lokaci ya yi tsada ya fito da shi don ya gallazawa al'umma, wannan shi ne malamai suke kira IHTIKAR, KO BAI'UL MUHTAKIR, wannan aiki haramun ne babu ko shakka, Sahabin Annabi mai suna Ma'amar ya ruwaito hadisi cewa: Annabi ya ce: "Duk wanda ya yi ihtikari (ɓoye kaya har sai ya yi tsada) mai saɓo ne". A wani lafazin kuma ya ce: "Babu mai yin ihtikari sai mai saɓo".

    Duba Muslim 1605.

    Lallai bai halasta mutum ya saye kayan abinci da makamantansu da nufin ɓoye shi har zuwa lokacin da mutane suke tsananin buqatarsa, sannan ya fito da shi ya gallaza ma jama'a ba.

    Amma wanda ya sayi kaya ko ya yi noma sai a lokacin kayan ya yawaita a kasuwa ta yadda ko ya fitar da kayan ba zai sami riba ba, sai ya bari har zuwa lokacin da farashi zai ɗan matsa gaba, to wannan babu laifi matuqar ba zai cutar da kowa ba.

    Duba Alminhaaj: Sharhun Nawawiy Ala Muslim 6/42.

    Allah ne mafi sani.

    Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.`         

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.