𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Mene ne hukuncin sallar Wanda ya
karanta surah a raka'a biyun karshe?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam. Wanda ya qara karatun surah a
raka'a ta uku da ta huɗu a
sallah mai raka'a huɗu,
babu komai a kansa, saboda hadisin Abu Sa'id Alkhudriy da yake cewa: Lallai
Annabi ﷺ ya
kasance yana karanta gwargwadon aya talatin a kowace raka'a daga cikin raka'o'i
biyu na farkon Sallar Azuhur, a raka'o'i biyun qarshe kuwa yana karanta
gwargwadon aya goma sha-biyar a kowace raka'a. A La'asar kuwa yana karanta
gwargwadon aya goma sha-biyar a raka'o'i biyun farko, a raka'o'i biyun qarshe
kuma yana karanta gwargwadon aya bakwai.
Duba Muslim 452.
Kenan wannan hadisin ya nuna cewa Annabi ﷺ yakan karanta surah a wasu lokutan a
raka'o'i biyun qarshe na Azuhur da La'asar, sai dai Annabi ﷺ a wasu lokutan ne yake yin hakan, wato ba
a duk sallar Azuhur da La'asar ba ne yake yi, saboda hadisin Abu Qatada da
Bukhariy da Muslin suka ruwaito da ke cewa: "Lallai Annabi ﷺ ya kasance yana karanta Fatiha da surah a
raka'o'i biyun farko na Azuhur da La'asar, wani lokacin yakan jiyar da mu aya ɗaya, sannan kuma yana karanta Fatiha ne
kawai a raka'o'i biyun qarshe".
Bukhariy 759. Muslim 451.
Kenan kuma shi wannan hadisin ya nuna cewa Annabi ﷺ ba ya karanta surah a raka'o'i biyun
qarshe. Saboda haka ne malamai suka tafka saɓani a kan hadisin da ya kamata a yi amfani
da shi a game da wannan matsalar, sai wasu malaman suka rinjayar da hadisi na
biyu, saboda kasancewarsa Bukhari da Muslim suka ruwaito, wasu kuma suka ce za
a iya haɗa duka
hadisan a yi amfani da su ba tare da cin karo da juna ba.
Maganar da ta fi zama daidai ita ce za a iya haɗa hadisan a yi aiki da su duka ba tare da
sun saɓa wa
juna ba, yadda abin yake kuwa shi ne, wani lokacin Annabi ﷺ yakan yi Fatiha da surah har a raka'o'i
biyu na qarshen Azuhur da La'asar kamar yadda hadisin Muslim ya bayyana, wani
lokacin kuma ba ya yi kamar yadda hadisi na biyu da Bukhariy da Muslim ɗin suka ruwaito ya bayyana, amma rashin yi
ɗin ne a gaba a bisa
fahimtar jumhur na Malamai.
Amma a fahimtar malaman da ba sa aiki da wancan
hadisi na Muslim da ya ce Annabi ﷺ yana
karatun surah a raka'o'i biyun qarshe, su suna
da fahimtar cewa duk wanda ya yi karatun surah a raka'o'i biyun qarshe
zai yi sujjada ba'adiyya, saboda a fahimtarsu ya yi qari ne a cikin sallah.
Allah ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/CQ9TMXMrWDx1y7sYye2znU
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.