Ticker

Hukuncin Sana’ar Waka

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Ƙanina ne yake son ya zama mawaƙi, shin ko hakan ya halatta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Malamai sun kasa waƙa gida biyu ne: Akwai wacce ake haɗa ta da kayan kiɗa, akwai kuma wacce ba a haɗa ta da komai.

1. Waƙar da ake haɗa ta da kayan kiɗa, kamar ganga ko kalangu ko garaya ko molo ko kuntugi ko gurmi ko goge ko busa ko algaita ko ƙwarya ko tafi ko feɗuwa (fito) ko nishi da sauran makamantansu, malamai ba su goyi bayan halaccin yin wannan irin waƙar ba, sai a wurare biyu kawai:

(i) Ranar Idi ga yara ƙanana, kuma da kalmomin da ba su ci-karo da koyarwar kyakkyawan addinin musulunci ba.

(ii) Ranar tarewar aure, shi ma ga yaran mata ƙanana, da kalmomin da ba su ci-karo da koyarwar kyakkyawan addini ba.

Waɗannan wuraren sun halatta ne ga waɗanda aka ambata kawai saboda hadisai sahihai da suka zo da bayani a kan haka.

Amma idan aka saɓa wa waɗannan ƙaidojin, kamar aka ɗauke waƙar daga waɗannan wuraren aka mayar da su waɗansu wuraren na dabam, kamar lokutan bikin naɗin sarauta ko na saukar karatu, ko murnar cikan shekara, ko kama aiki, ko samun ƙarin girma da makamantansu, ko kuma aka sanya manyan maza ko mata ne masu yin waƙar ko kiɗan, ko kuma ya zama ana yin su ne a wurin bikin da ya zama a cikinsa akwai cakuɗa a tsakanin maza da mata baligai ko murahiƙai (waɗanda suka kusa balagar), da sauran irin waɗannan dai, to a wannan halin waƙar da kiɗan duk ba su halatta ba, sun zama fasiƙanci, kuma saɓon Allaah Maɗaukakin Sarki!

2. Idan kuwa waƙa ce kaɗai ba tare da an haɗa ta da komai na kayan kiɗan da ambatonsu ya gabata ba, to a nan sai an kalli wasu ƙaidoji kuma kafin a amince da halaccin ta:

(i) Ya zama kalmomin da ake amfani da su kyawawan kalmomi ne da ba su ci-karo da koyarwa kyakkyawan addini da ɗabi’a ba.

(ii) Ya zama wurin da ake yin waƙar ya dace da irin wuraren da aka riwaito magabata suna yi, kamar a cikin halin tafiya ko komowa daga aikin hajji ko jihadi da sauransu.

(iii) Ya zama babu cuɗanya ko cakuɗa a tsakanin maza da mata baligai ko murahiƙai a wurin da ake yin wannan waƙar.

(iv) Ya zama ba a haɗa wakar da motsa wata gaɓar jiki kamar kai ko hannuwa ko ƙaffafu a tare da waƙar ba.

(v) Ya zama waƙar ba ta ɗauke hankali, ta mantar da wani abin da ya fi ta muhimmanci a rayuwar duniya ko lahira ba.

Amma idan aka karya ko ɗaya daga cikin waɗannan ƙaidojin, kamar aka riƙa siffata ayyukan saɓo ana ƙawata su, kamar zina da tsiraici da giya da caca da sata da makamantan haka, ko aka riƙa munana ayyukan alheri ana ƙyamatarwa a kan su, kamar sallah da salati da azumi da sadaka da hajji da kyautata wa maƙwabta da zawarawa da marayu da makamantan haka, ko kuma ya zama ana yin waƙar a wurin da bai dace ba, kamar a wurin taron bikin cikar shekarar haihuwa ko ta ƙarin girma ko samun wani matsayi, ko ya zama ana yin ta a yanayi ko tare da siffar da ba ta dace ba, kamar a riƙa yin waƙar tare da rangaji ko kaɗa hannu ko kai ko ƙafa da sauransu, ko kuwa aka mayar da waƙar ta zama sanaa, har ta hana mai yi koyon wata sanaa ta halal, ko ma ta shagaltar da shi daga hardace Alqurani ko Sunnah ko Fiqhu da sauransu, to a wannan lokacin wannan waƙar ita ma ba ta halatta ba, in ji malamai.

Daga cikin irin waɗannan waƙoƙin marasa kyau akwai nauukan waƙoƙin da ake kira waƙoƙin addini. A asali waɗannan babu laifi idan aka yi su a inda suka dace, yadda suka dace, ba tare da an yawaita su ba, kuma ba a faɗi abin da ba daidai ba a cikinsu. Amma a lokacin da su ma ya zama ana sharara ƙarya a cikinsu, ta hanyar faɗa wa Allaah abin da bai faɗa ba, ko siffata Annabi Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da siffofin da suka wuce matsayinsa, ko kuma ɗaukaka matsayin waliyyai sama da matsayinsu na asali, a riƙa kai su matsayin Annabawa ko ma na Ubangiji (Tabaaraka Wa Taaala), a irin waɗannan halayen ya zama dole a bayyana haramcin irin waɗannan waƙoƙin fiye da waɗanda suka gabata, saboda jingina su da addini da aka yi.

Akwai riwayoyi sahihai da suka zo a kan haramcin waƙa da kiɗa, kamar wannan:

Manzon Allaah (Sallal Laahu ’Alaihi wa Alihi wa Sallam) ya ce:

Waɗansu mutane za su kasance a cikin al’ummata waɗanda za su halatta zina da alharini da giya da kayan kiɗa. Kuma waɗansu mutane za su sauka a gefen wani tsauni, ana yi musu goge ko garaya a cikinsu, sai mabaraci ya zo musu da buƙatarsa, su kuma sai su ce masa, ka bari sai gobe ka dawo. Sai kuwa a wayi gari Allaah ya hallaka su gaba ɗaya, an rugurguza tsaunin, su kuma an shafe waɗansu: An mayar da su birai da aladu!

Wannan yana daga cikin hadisai da malamai suka inganta a kan haramcin kayan kiɗa.

(Dubi: Littafin Tahreem Alaatit Tarbi na As-Shaikh Al-Albaaniy da Tanzeehus Sharee’ah an Ibaahatil Aghaaniyil Khalee’ah na Shaikh Ahmad Bn Yahya An-Najmiy).

Wannan hadisin ya nuna haramcin amfani da kayan kiɗa da busa irin na zamani ta hanyoyi da yawa kamar haka:

(i) Cewa da ya yi: ‘za su halatta’ ya nuna a asali wannan abin ba halal ba ne, wani abu ne daga cikin abubuwan da Allaah ya haramta amma su ne suka mayar da shi halal!

(ii) Haɗa shi da sauran abubuwan da kowa ya san haram ne a wuri ɗaya, watau: zina da giya da sanya alharini, ya nuna hukuncinsu iri ɗaya ne watau haramci.

(iii) Hallaka su da Allaah Ta’aala ya yi wannan ma ya nuna cewa sun aikata haram ne.

(iv) Haka kuma shafe su da aka yi zuwa ga siffofin birai da aladu, wannan ma ya nuna sun aikata haram ne.

Bayan mun ji wannan bayani a taƙaice, to wajibin abin da ke a kan ku game da wannan ƙanin naku shi ne ku yi janyo hankalinsa da yi masa nasiha a cikin hikima da kyakkyawan waazi cewa:

(i) Ya mayar da hankalinsa ga abin da ya fiye masa alkhairi a duniyarsa da barzahu da lahira, kamar ya yi ƙoƙarin hardace Alqurani, ya koyi hadisai sahihai na Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya hardace su, kuma ya kula da hardace littaffan ilimi.

(ii) Ya riƙa kulawa da darussansa na makarantar boko don ya koyo ilimin da zai ƙara masa basira da fahimta da wayewa a cikin rayuwar da yake ciki na duniya. Kar ya zauna cikin jahilcin da har wasu za su mayar da shi wawa, su riƙa amfani da shi domin biyan buƙatun kawunansu kawai.

(iii) Ya yi ƙoƙarin ƙwarewa a kan wata kyakkyawar sanaa ta halal, ba waƙa ko kiɗa ko rawa da makamantansu ba. Domin ta haka ne zai samu abin da zai rayu da shi na halal a cikin duniya, ya kare mutuncinsa da na iyalinsa da iyayensa da ’yan uwansa da danginsa da sauransu, kafin makomarsa lahira.

(iv) Ya gane cewa: Waƙa ba sanaar Annabawa da Manzannin Allaah (Alaihimus Salaatu Was Salaam) ba ce. Amma dai ita hanya ce kawai ta mabiya shaiɗan, wadda kuma da ita yake kawar da su daga Alqur’ani da fahimtarsa da yin aiki da shi. Shiyasa ya sanya ta zama abin amfani da yayatawa a cikin kusan dukkan tashoshin rediyo da talabijin da sauran kafafen sadarwa a yau.

(v) Ya sake dubawa ya gani: Lallai waƙa ba sanaar fitattun mutanen kirki ba ce. Ya binciki magabatan wannan alummar ya gani: Manyan malamai na-Allaah irin su Abu-Haneefah da Maalik da As-Shaafiiy da Ahmad da mabiyansu har zuwa yau (Rahmatul Laahi Alaihim) guda nawa ne suka rayu a kan waƙa? Kuma magabatansu daga cikin manyan Sahabbai daga cikin Al-Khulafaaur Raashiduun da Al-Asharatul Mubassharuuna Bil Jannah (Radiyal Laahu Anhum) guda nawa ne suka koyar da sanaar waƙa?!

Kai! Shi kansa Manzon Allaah Annabin Rahama (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ga abin da Allaah (Tabaaraka Wa Ta’aala) ya faɗa a kansa:

وَمَا عَلَّمۡنَـٰهُ ٱلشِّعۡرَ وَمَا یَنۢبَغِی لَهُۥۤۚ

Kuma ba mu koya masa waƙa ba, kuma ba ta ma kamace shi ba. (Suratul Yáá-Seen: 69)

Ko wannan kaɗai ya isa ya sa mai hankali ya nisanci mayar da waƙa ta zama sanaar da zai rayu a kanta, matukar dai mabiyi ne na gaskiya wanda kuma yake ƙaunar zama tare da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a lahira.

Allaah ya shiryar da mu gaba-ɗaya ga abin da yake so kuma yake yarda da shi.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments