Hukuncin Wanda Ya Saci Kuɗin Ubangidansa

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Aslam Malam Barka Da Rana Allah Ya Temaka Amin. Dan Allah Malam Ga Tambaya Ta Atemakeni Dan Allah. Abokina Ne Yana Da Me Gida Suna Aiki Tare Sai Ya Incehi Ya Dauka Masa Kuɗi Malam Me Gidan Nasa Ya Rasu Malam Shi Kuma Yanaso Ya Dawo Da Wannan Kuɗin Malam Yaya Zeyi Ya Dawo Da Wan Nan Kuɗin ?.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

    Abin da zai yi shine ya fara tuba tukunna zuwa ga Allah (SWT) domin cin amanar nan da yayi,  babban laifi ne a musulunci. Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya lissafa irin wannan laifin acikin jerin alamomin munafuki.

    Acikin wani hadisin kuma ya ce "YARO (MAI KULA DA DUKIYAR UBANGIDANSA) SHIMA MAKIYAYI NE KUMA za a TAMBAYESHI GAME DA KIWON DA AKA BASHI".

    Abu na biyu kuma ya samo daidai misalin abin da ya sata ɗin nan, yaje ya bama iyalan wannan ubangidan nasa, sannan kuma yaci gaba da yin addu'ar neman gafara ga Ubangidan nasa.

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/G5NSbo2TyHMD6bcoEfds5E

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.