𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Meye hukuncin mutumin da yayi sallah, sai bayan ya
gama sannan ya fahimci cewa wannan sallah da yayi ba Alqibla ya fuskanta ba?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Yana daga cikin sharadin sallah mutum ya fuskanci
Alqibla matukar ba wata matsala aka samu ba wadda zata hanashi hakan, inhar ko
mutum yaki fuskantar Alqibla alhalin yana da dama toh sallarsa batacciya ce,
sabida Allah ya ce:
قَدْ نَرَىٰ تَقَلُّبَ وَجْهِكَ فِي السَّمَاءِ ۖ فَلَنُوَلِّيَنَّكَ قِبْلَةً تَرْضَاهَا ۚ فَوَلِّ وَجْهَكَ شَطْرَ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ ۚ وَحَيْثُ مَا كُنْتُمْ فَوَلُّوا وُجُوهَكُمْ شَطْرَهُ ۗ وَإِنَّ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ لَيَعْلَمُونَ أَنَّهُ الْحَقُّ مِنْ رَبِّهِمْ ۗ وَمَا اللَّهُ بِغَافِلٍ عَمَّا يَعْمَلُونَ
Lalle ne, Muna ganin jujjũyãwar fuskarka a cikin
sama. To, lalle ne, Mu jũyar da kai ga Alƙibla wadda kake yardã da ita. Sai ka jũyar da fuskarka wajen Masallãci Tsararre, kuma inda duk kuka kasance,
to, ku jũyar da
fuskõkinku jiharsa. Kuma
lalle ne waɗanda
aka bai wa Littãfi, haƙĩƙa su,
sunã sanin lalle ne, shĩ ne gaskiya, daga Ubangijinka. Kuma Allah
bai zama Mai gafala ba daga abin da suke aikatãwa. (Baqara 144).
Da umarnin da annabi (Sallallahu alaihi wasallam)
yayi ya ce “Sannan ka fuskanci alQibla kayi kabbara) Bukhari 6667.
Maluman sun tafi akan cewa wanda yayi sallah ba
zuwa ga Alqibla ba da gangan ko a halin mantuwa zai sake, sabida bai cika sharadinta
ba.
An tambayi maluman ‘Lajnatudda’imah’ kan hukuncin
matafiyi da ya isa gari, yayi sallah ba zuwa ga alqibla ba, kuma bai tambaya
ba, baiyi bincike ba, suka bada amsar cewa zai sake wannan sallar, sabida
rashin bincike da baiyi ba, ko kokari wurin gano alqiblar, (Lajnatudda’imah
Majmu’ah ta biyu 5/294).
Dan haka, ya wajaba akan wanda yayi sallah ba zuwa
ga Alqibla ba yana mai mantuwa ya sake sallansa, amma in ya rasa gane Alqibla
sabida rashin wanda zai tambaya, ko kuma wasu dalilai, toh mafi yawan Malamai
suna akan bazai sake ba. kuma hakan shine daidai…….
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/CfDLSdXaGD00Wpxdfy2ofp
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.