Hukuncin Wanke Gaɓoɓin Alwala Sau Ɗai-Ɗai Ko Sau Biyu-Biyu

    𝐓𝐀𝐌𝐁A𝐘𝐀

    Assalamu alaikum mallam, Ina da tambaya, shin yin Alwala sau biyu biyu ya halasta?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam.

    1. Tabbas ya halasta mutum ya wanke gaɓoɓin alwala sau ɗai-ɗai, kamar yadda Abdullahi ɗan Abbas ya ruwaito cewa Annabi ya yi. Bukhari 157.

    2. Kuma ya halasta a wanke sau biyu-biyu, kamar yadda Abdullahi ɗan Zaidu ya ruwaito cewa Annabi ya yi hakan. Bukhari 158.

    3. Sannan kuma ya halasta a wanke sau uku-uku, kamar yadda mafi yawan hadisan da aka ruwaito game da siffar alwalar Annabi suka nuna yana yi. Bukhari 159.

    Wannan ya nuna cewa Manzon Allah yana caccanjawa ne domin nuna halasci, wani lokacin ya wanke sau ɗai-ɗai, wani lokacin sau biyu-biyu, wani lokacin kuma sau uku-uku.

    Duk wanda aka yi alwala da ita alwala ta inganta, saboda wanki na farko shi ne wajibi, abin da ake so a tabbatar ruwa ya game ko'ina, sai dai kuma wanke gaɓoɓin alwala sau uku-uku ya fi kamala fiye da sau ɗai-ɗai ko sau biyu-biyu, saboda shi ne abin da aka fi yawan ruwaitowa daga siffar alwalar Manzon Allah .

    Allah ne mafi sani.

    Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/G5NSbo2TyHMD6bcoEfds5E

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.