Hukuncin Yin Karatun Alqur'ani Ba Da Harshen Larabci Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, Allah ya qara basira, Allah ya saka da gidan aljanna firdausi. Tambayata ita ce Allah ya gafarta malam misali mutum bai haddace Alqur’an ba, sai yana so ya sauke a watan Ramadan, Allah ya gafarta malam idan ya zo surar da bai iya ba kuma ya iya karanta Hausa, shin zai iya karasawa da Hausa kuma yana da ladan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa’alaikumus Salam. Ba ya halasta a yi karatun Alqur'ani da wani harshe da ba Larabci ba, ko da mutum yana iya kyautata karatun ko ba ya iya kyautatawa, ko da a cikin sallah ne ko a wajen sallah, idan mutum ya yi sallah da karatun Ajamanci sallarsa ba ta inganta ba, wannan shi ne maz'habinmu, kuma shi ne maz'habin Malik da Ahmad da Dáwud da Abubakar bin Munzhir inji Imamun Nawawiy.

Duba Attibyan Fiy Ádábi Hamalatil Qur'an 96.

Kuma wannan ita ce fahimtar jumhur ɗin malaman Musulunci, cewa bai halasta a karanta Alqur'ani da Ajamanci ba, saboda Allah Ta'ála ya saukar da Alqur'ani ne a matsayin Balaraben littafi, kamar yadda aya ta 2 da ke suratu YUSUF ta bayyana:

إِنَّا أَنْزَلْنَاهُ قُرْآنًا عَرَبِيًّا لَعَلَّكُمْ تَعْقِلُونَ

Lalle ne Mũ, Mun saukar da shi, yanã abin karantãwa na Lãrabci; tsammãninkũ, kunã hankalta.

Saboda haka ƴar uwa yin hakan bai halasta ba, kuma ma ai ba a ce dole ne sai mutum ya sauke gaba ɗaya Alqur'ani a watan Ramadan ba, musamman ga wanda bai iya karanta Alqur'ani dukkansa ba, babban abin da ake so shi ne mutum ya qara qoqari wajen karanta Alqur'ani a watan, ko da kuwa sura ɗaya tal mutum ya iya sai ya yi ta maimaita abin da ya iya ɗin, tare da koyon sauran surorin da bai iya ba a Larabce a gaban malaman Alqur'ani, domin shi Alqur’ani ba kamar littafin koyi da kanka ba ne, wato (Teach your self), dole a bagan malaman da suka san shi suka iya shi ake koyonsa.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments