Hukuncin Yin Wa’azi Kafin Zuwan Liman A Ranar Jumma'a (Pre-Khutbah)

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum. A kan wa’azi ko tunatarwa a ranar jumma’a kafin zuwan liman, shin ko akwai wani hadisin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ko wani atharin malaman salaf a kan haka da ya tabbata?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

    Abin da na sani dai shi ne:

    Al-Imaam Al-Bukhaariy (910) ya riwaito hadisi da isnadinsa har zuwa ga Sahabi mai daraja Salmaan Al-Faarisiy (Radiyal Laahu Anhu), daga Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

    « مَنِ اغْتَسَلَ يَوْمَ الْجُمُعَةِ ، وَتَطَهَّرَ بِمَا اسْتَطَاعَ مِنْ طُهْرٍ ، ثُمَّ ادَّهَنَ أَوْ مَسَّ مِنْ طِيبٍ ، ثُمَّ رَاحَ فَلَمْ يُفَرِّقْ بَيْنَ اثْنَيْنِ ، فَصَلَّى مَا كُتِبَ لَهُ ، ثُمَّ إِذَا خَرَجَ الإِمَامُ أَنْصَتَ ، غُفِرَ لَهُ مَا بَيْنَهُ وَبَيْنَ الْجُمُعَةِ الأُخْرَى »

    Duk wanda ya yi wanka a ranar Jumma’a, kuma ya tsarkake jikinsa da gwargwadon abin da ya samu iko na tsarki, sannan ya shafa mai ko ya shafa turare, sannan ya taka zuwa masallaci, kuma bai rarrabe a tsakanin waɗansu mutane biyu ba, sai kuma ya sallaci nafilolin da aka ƙaddara masa, sannan a lokacin da liman ya fito sai ya yi shiru (ya saurare shi), to an gafarta masa abin da yake a tsakaninsa da ɗaya Jumma’ar.

    Wannan ya nuna cewa: Duk lokacin da mutum ya shiga masallaci a ranar Jumma’a abin da aka ɗora masa shi ne, ya yi ta yin nafiloli da gwargwadon yadda ya ga dama kawai, ba tare da iyakancewa ba. Haka Al-Allaamah Ibn Al-Qayyim (Rahimahul Laah) ya faɗa:

    فَنَدَبَهُ إِلَى صَلَاةِ مَا كُتِبَ لَهُ ، وَلَمْ يَمْنَعْهُ عَنْهَا إِلَّا فِي وَقْتِ خُرُوجِ الْإِمَامِ

    Sai ya ladabtar da shi (mai shiga masallaci don sallar Jumma’a) ga yin sallar nafilar da aka ƙaddara masa, kuma bai hana shi cigaba da hakan ba sai a lokacin da liman ya fito.

    Wannan kuwa shi ne abin da Khalifah Umar Bn Al-Khattaab (Radiyal Laahu Anhu) ya faɗa, kuma Al-Imaam Ahmad (Rahimahul Laah) ya bi shi a kansa, cewa:

    خُرُوجُ الْإِمَامِ يَمْنَعُ الصَّلَاةَ ، وَخُطْبَتُهُ تَمْنَعُ الْكَلَامَ

    Fitowar liman ke hana sallar nafila, kuma huɗubarsa ke hana magana. (Zaadul Ma’aad: 1/346)

    Wannan nafila ce da ba a yi mata iyaka da wani adadi iyakantacce ba. Shiyasa riwayoyi daga ayyukan magabata a kan haka suka sha bamban: Ibn Umar (Radiyal Laahu Anhumaa) raka’o’i goma sha-biyu yakan yi kafin fitowar liman, Ibn Abbaas (Radiyal Laahu Anhumaa) kuma raka’o’i takwas, Ibn Mas’uud (Radiyal Laahu Anhu) kuwa raka’o’i huɗu. Ya tabbata daga Ummul-Mu’mineen Safiyyah (Radiyal Laahu Anhaa) ita ma ta yi raka’o’i huɗu kafin fitowar liman, sannan ta yi raka’o’i biyu na Jumma’a tare da liman. (Al-Ajwibatun Naafi’ah, shafi: 35)

    Wannan shi ne abin da ya tabbata a cikin Sunnah tun daga zamanin farko, kuma ba mu samu wata riwaya ingantacciya da ta nuna cewa a zamanin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), ko a cikin zamunan khalifofinsa shiryayyun nan matabbata a kan shiriya (Radiyal Laahu Anhum) an samu wani ya miƙe domin faɗakarwa ko tunatarwa a masallacin Jumma’a kafin fitowar liman ba.

    Sannan kuma dayake muryar mai wa’azin zai zama mai ɗauke hankalin mai sallah ne a wannan lokacin. Shiyasa Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya hana ɗaga murya a tsakanin masu yin karatun sallah a cikin masallaci, kamar yadda Al-Imaam Abu-Daawud (1334) ya riwaito kuma Al-Albaaniy ya sahhaha shi:

    « أَلاَ إِنَّ كُلَّكُمْ مُنَاجٍ رَبَّهُ فَلاَ يُؤْذِيَنَّ بَعْضُكُمْ بَعْضًا وَلاَ يَرْفَعْ بَعْضُكُمْ عَلَى بَعْضٍ فِى الْقِرَاءَةِ ». أَوْ قَالَ : « فِى الصَّلاَةِ ».

    Jama’a! Kowannenku fa yana ganawa da Ubangijinsa ne. Don haka kar wani sashenku ya cutar da sashe, kar wani sashe ya ɗaga muryarsa da karatu a kan sashe. Ko kuma ya ce: A cikin sallah. (Sahih Abi-Daawud: 1203)

    Don haka, abin da ya fi daidai a fahimtarmu shi ne: Kar wani ya tashi a cikin masallacin Jumma’a domin yin wa’azi ko tunatarwa kafin zuwan liman, sai dai ko in wani abu ne muhimmi da ya bijiro a wani lokaci guda kawai. Amma bai kamata a ɗauke shi kamar yadda yawancin mutane a yau suka ɗauke shi a matsayin wata ƙaida ko Sunnah daga cikin Sunnonin Jummaa ba. Wannan kan iya zama ɗaya daga cikin bidi’o’i abin ƙyama.

    Allaah ya kare mu daga dukkan bidi’a, kuma ya gafarta mana dukkan kura-kuranmu.

    WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.