𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Yaro ne ya yi
laifi sai ubansa ya doke shi sai shi kuma ya kai ƙarar uban, aka kawo masa
sammaci daga kotu. Sai ya komo gida yana kuka, ya ce wa matarsa (uwar yaron):
Idan ta sake ba yaron nan abinci, to a bakin aurenta igiya uku! Kuma sai da ya
maimaita mata har sau uku! Sai kuwa ta daina. Daga baya sai kakar yaron
(mahaifiyar mijin) ta ce, ta cigaba da ba yaron abinci. Sai ita kuwa ta ba shi.
Tambaya: Wai ina matsayin aurenta?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa
Barakaatuh.
Daga cikin nau’ukan sakin aure ta fuskar lafazin
aukar da shi akwai zartacce (munjiz), akwai kuma ratayayye (mu’allaq).
Zartaccen saki shi ne wanda mai faɗin sa ya yi aniyar aukar da shi a daidai
lokacin da ya faɗe shi,
kamar wanda ya ce wa matarsa: ‘Ke sakakkiya ce.’ Ko ya ce mata: ‘Na sake ki.’
Hukuncin wannan shi ne aukuwar sakin a daidai lokacin da ya aukar da shi.
Ratayayyen saki kuwa shi ne wanda mai fadin sa ya
rataya sakin ga aukuwar wani abu, kamar wanda ya ce: ‘Idan na shiga gida, ko
idan kika shiga gidan su wance to ke sakakkiya ce.’
Irin wannan sakin malamai sun kasa shi gida biyu:
1. Idan tun daga zuciyarsa nufin sakin ya yi a
lokacin aukuwar abin da ya rataya sakin a kansa, to sakin ya auku!
2. Idan kuma ba nufinsa aukar da sakin ba ne, shi
dai kawai razanar da matar yake son yi, ko yana son ya ɗora kansa ko ita kanta a kan aikata wani
abu, ko kuma ya hana kansa ko ita aikata wani abu, to a nan malamai ba su
zartar da sakinsa ba. Sai dai kaffarar rantsuwa ce kawai ta hau kansa.
(Tamaamul Minnah: 3/156)
Don haka, abin da ya rage sai an ji daga wannan
mutumin wanda matsalar da ke tsakaninsa da ɗansa ta janyo furta waccan kalmar ga
matarsa: Mecece manufarsa?
Allaah ya kiyaye.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/IqsWWSpUkwk6b8hWJ6vXOO
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.