Ticker

Idan Mace Ta Yi Ɓari Bayan Mutuwar Mijinta Da Wata Huɗu, Ta Kammala Iddarta

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Salam alaikum malam mace ce mijinta ya rasu tana da cikin wata huɗu sai tayi ɓari bayan rasuwar mijin da kwana 3 yaya takaba ɗin ta zai kasance?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikum assalam wa rahmatullhi

Mutukar cikin ya kai wata huɗu, to ta kammala iddarta.

A cikin suratul Dhalak aya ta (4), Allah ya bayyana cewa: iddar mace Mai ciki tana kasancewa idan ta haife cikinta.

... ۚ وَأُولَاتُ الْأَحْمَالِ أَجَلُهُنَّ أَنْ يَضَعْنَ حَمْلَهُنَّ ۚ ...

...Kuma ma'abũta cikinna ajalinsu, (shi ne) cewa su haifi cikinnansu.

Duk lokacin da ciki ya kai wata huɗu, dukkan hukunce-hukuncen haihuwa suna hawa kansa, a zancen da ya fi inganci. Hadisin Abdullahi Dan Mas'ud ya tabbatar da cewa ana busawa yaro rai idan ya cika kwana (120) a cikin mahaifiyarsa.

Allah ne Mafi sani.

✍️Amsawa: Dr Jamilu Yusuf Zarewa

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments