Ticker

    Loading......

KAKAN HASAN, ANNABI (SAW)

1.     Daren jiya baituka sun zo mani

Sun ce da alkalami ya ce sannunka.

 

2.     ‘Da gun Aminatu dan Abdullahi ga

Goyon Halimatu, duniya ta san ka.

 

3.     Dukkan mazaje sun gaza sai jinjina

Mata ko sun gaza haihuwar tamkarka.

 

4.     Kai ne kadai aka ce mu bi ba tambaya

Taku-da-taku ne alamar sonka.

 

5.     Sako da nauyi wa za a ba domin ya kai

Allah ya ce: kai ne kadai zan ba ka.

 

6.     Sako na addini da babu kamarsa yau

Haske, da yado, kowa ya na san barka.

 

7.     An tattaro duka annabawa, mursalai

An tambaya: shin kowane zai bi ka?


8. Amsarsu: tabbaci duk za mu bi

Haka sun ka ce, Allahu ne shaidanka. 

 

9.     Ka ida sakon, ka yada haske ba duhu

Mun shaida wannan, tabbatan mun dauka.

 

10.     Dukkan tafarki ko yawan mabiyansa yau

Ce mar ‘bata, in ba shi kan sunnarka.

 

11.  Dukkan ibada ko tulun adadinta kau

Banza ta ke, in zucci ba a son ka.

 

12.  In an yi kuri: “Ai akida ta mu ce”,

Karya a ke, sai dai a ce kakanka.

 

13.  Mun gode Allah wanda yash shiryar da mu

Hanya guda mikakkiyar nan taka.

 

14.  Da ma ya sa Ranar Kiyama mui gamo-

Da-katar a ce mun sam rabon cetonka.

 

15.  Ba mu kadai ba, duk muminina gaba daya

Ka hado mu duk sannan ka ce mana naka.

 

16.  Kowa ya zo don shan ruwan Alkausara

Ba zai yu ba, sai gun hannun albarka.


17. Ka sa ni gabanka in kirari mai yawa

Karshe ka ce mini: ya Ali ga naka.

 

18.  Tsira aminci da’iman mun roka maka

Kakan Hasan! Waye ya ce ya fi ka?

 

Dr. Aliyu U. Tilde

9 October 2022

Post a Comment

0 Comments