TAMBAYA (13)❓
Assalamu Alaykum malam an tashi lpy dan Allah
malam inaso a daure a amsa min tabayoyina wllhy nasha tura tambaya amma ba taba
amsa min ba ngd
Tambaya ta farko malam nakai shekara hudu da aure
inada yarinya 1 amma malam bansan dadin aure ba hatta sha’awa ma ban santaba
sannan wani lokacin inajin zafi idan muna saduwa da mijina wani lokacin kuma
idan nayi mafarkin ana sadauwa dani nakanji dadin haka shine nakeso nasan mi
yake kawo hakan nagode
Tambaya ta biyu malam ina yawan yin mafarkin
macizai amma basa yimin komai kawai zan gansu dayawa ne Sosai sannan inayin
mafarkin anbata min guri da kashi nayi ta wankewa amma baya wankuwa sai
mafarkin kare yana bina nida yarinta amma kafin na farka ina illatar da Karen
dan dakyar yake motsawa dan Allah malam ka amsamin cikin ilimin da ubangiji
yayi maka Nagode
AMSA
Kamar yanda muka san cewar kowacce cuta tanada
magani kuma babu wani abu da zai gagari Allah SWT. A shawarce kije Islamic
chemist kiyi musu bayani in sha Allahu za a samu maganin da ya dace da
matsalarki. Sannan kuma fassarar mafarkin saduwa kamar yanda Imam Muhammad Ibn
Seerin (Dalibin Imam Malik, Allah ya jikansu baki daya) ya ce: Mafarkin mace
tana saduwa da namiji na nufin fadawa tarkon zunubi, idan mara lafiya yayi
mafarkin yana saduwa da mahaifiyarsa to mutuwarsa kenan saboda anan mahaifiyar
tana nufin kasar da aka halicceshi, haka kuma mafarkin saduwa na nufin bashi ko
kuma samun sauqin rayuwa, mafarkin saduwa da karuwa na nufin son duniya ko kuma
samun ribar kasuwanci, mafarkin saduwa da macen Aljannah (Hurul Ayn) na nufin
zurfin addini da tsarkin ruhi
Mafarkin kare na nufin mutum mai yawan aikata
zunubbai, ganin kare na nufin mace mai girman kai wadda take tareda mutane masu
duqufa akan sabon Allah. Fada da kare na nufin son duniya. A takaice dai
mafarkin kare yawanci abune mara kyau indai ba mafarkin dan karamin farin dan
kwikwiyoba wanda yakeda alaqa da haihuwar yaron da za a so kuma zai taso a
matsayin nagari
Mafarkin kashi yana nufin kudi, yin kashi akan
gado na nufin sakin aure, yin tafiya akan kashi na nufin wahala da kunci, kashi
a mafarki na nufin kudi, boyayyen sirri, tafiya, fada, waraka daga cuta,
mummunan tunani, waswasi, shaawa da yarda. Jin warin kashi a mafarki na nufin
bashi, aiki fiyeda kima, bari ga mai ciki. Ganin kashin mutum a mafarki na
nufin kusantar bala'i, bude kasuwance.
Mafarkin macizai na nufin gaba tsakanin maqota,
sirikai ko kuma yaya. Idan maciji ya hadiye mutum a mafarki na nufin mutum zai
samu wani shahararren muqami. Bakin maciji na nufin qaqqarfan maqiyi, farin
maciji na nufin rarraunan maqiyi. Kashe maciji na nufin yin aure. A takaice dai
yin mafarkin maciji ko gansheka na nufin kishi, hassada, yaudara, damfarar
mutane, saba alqawari da kuma tsananin qiyayya
SHARHI
Idan akwai hoto wanda ake ratayawa a bango a gidan
da kike (na mutum ko na dabba) to a cireshi ko kuma a juyashi saboda Annabi SAW
ya ce: "Mala'ikun rahama basa shiga gida wanda akwai kare ko kuma sura
(hoto)"
(Sahihul Bukhari 3543)
Sannan kuma ki dage da adhkar na safiya da maraice
saboda sharrin maqiya da mahassada
Sannan kuma a dage da addu'ar Allah ya kauda
sharrin da mafarkin ya kunsa domin kuwa an karbo daga Abu Hurairah RTA, Annabi
SAW ya ce: "Babu abin da yake canza qaddara sai addu'a"
Tirmidhi 3573
Subhanakallahumma wabi hamdika, ash-hadu anla
ilaha illa anta, astaghfiruka wa'atubi ilay
Amsawa:
✍️Usman
Danliti Mato Usmannoor_As-salafy)
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.