Mahaifina Ya Hanani Aure Wai Sai Na Gama Karatu

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum. Malam Ni budurwa ce, kuma na samu wanda nake so na aura, Amma mahaifina yaqi yarda yana so na gama karatuna na samu aiki kafin nayi aure  Bansan yadda zanyi ba.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullah.

Yana daga cikin amanonin da Allah ya dora wa mahaifa cewa su aurar da 'ya'yansu mata yayin da suka iso shekarun auren, mutukar sun samu mazajen da suka dace dasu.

Rashin bin wannan umurnin, babban saɓo ne, kuma cin amanar 'ya'yan ne. Allah ya ce:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لَا تَخُونُوا اللَّهَ وَالرَّسُولَ وَتَخُونُوا أَمَانَاتِكُمْ وَأَنْتُمْ تَعْلَمُونَ ٧٢۝

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada kuci amanar Allah da ManzonSa, kuma ku ha'inci amãnõninku, alhãli kuwa kunã sane. (Suratul Anfal Aya ta 27)

Kuma Allah ya faɗa acikin Suratun Nur ayah ta 32 ya ce:

وَأَنْكِحُوا الْأَيَامَىٰ مِنْكُمْ وَالصَّالِحِينَ مِنْ عِبَادِكُمْ وَإِمَائِكُمْ ۚ إِنْ يَكُونُوا فُقَرَاءَ يُغْنِهِمُ اللَّهُ مِنْ فَضْلِهِ ۗ وَاللَّهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ ٢٣۝

Kuma ku aurar da gwaurãye daga gare ku (wato 'ya'yanku marassa aure) da sãlihai daga bãyinku, da kuyanginku. Idan sun kasance matalauta Allah zai wadãtar da su daga falalarSa. Kuma Allah Mawadãci ne, Masani. (Suratun-Nur aya ta 32)

Kuma Manzon Allah ya ce "Idan wani yazo muku wanda kuka yarda da tarbiyyarsa da rikon addininsa, to aurar masa (da 'ya'yanku ko Qannenku). Idan har baku aikata haka ba, to fitina zata kasance a doron Qasa da kuma ɓarna mai girma".

Don haka irin abin da wasu iyayen sukeyi wajen hana 'ya'yansu mata yin aure da wuri, tare da dora musu burin wai dole sai sun kammala karatun Jami'ah kuma sun samu aikin gwamnati kafin suyi aure. Irin wannan ra'ayin ya saɓawa tsantsar tarbiyyah irin ta addinin musulunci, kuma tabbas yana zama sanadiyyar afkuwar ɓarna kala-kala acikin al'ummah. Kasancewar yanayin yadda Allah ya gina halittar ɗan Adam, ya gina sha'awa mai karfi ajikin mata wacce yawanci tana motsawa ne tun daga lokacin da alamomin balaga suka fara bayyana ajikin 'ya mace.

Shawarar da zan baki anan ita ce, idan mahaifin naki ya ksance mai saukin hali ba wanda zai iya saurararki kije wajensa ku tattauna ki gaya masa ra'ayinki, kuma ki bayyana masa cewa zaki iy Qarasa karatunki koda bayan anyi auren. ko kuma ki gaya wa mahaifiyarki ta sanar dashi.

Idan kuma babu wannan damar, to kije ki samu wani daga cikin kakanninki wanda zai wakilceki ya samu mahaifin naki suyi maganar. Ko kuma ki samu abokin mahaifinki ko kuma wani daga cikin 'yan uwansa na kusa.

Kafin nan kuma kici gaba da hakuri kuma ki yawaita addu'a  da neman zaɓin Allah acikin dukkan lamuranki. Allah zai kalli niyyarki ya baki mafita mafi alkhairi.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/EbkKRXdFzNu4F8aQZbZ1Vx

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments