MAI MARTABA SARKIN KARAYE YAYI ABIN AL'AJABI

    MAI MARTABA SARKIN KARAYE YAYI ABIN AL'AJABI

    MAI MARTABA SARKIN KARAYE YAYI ABIN AL'AJABI

    Ba kasafai akan hangi sarakuna a kasar Hausa sun je janaza ko ta'aziyya ba, hasali ma wanda akawa mutuwa ne kan je, kafa da kafa, zuwa fada domin yiwa sarkin garin su ta'aziyya. 

    Sai dai Mai Martaba Sarkin Karaye, Dr. Ibrahim Abubakar, yayi wani abu irin sa na farko a tarihin dani na taba ji ko gani;  daukar makara a kafadar sa domin yin rakiya ga wadda ta rasu. Hakika Sarki ya kyauta koda kuwa menene alakar sa da wadda ta rasu din.

    Wannan kyakkyawan misali da Mai Martaba Sarki yayi jarumta ce, wannan kyakkyawar mu'amula  ce, wannan kulawa ce, wannan saukin kai ne, wannan kauna ce ga wadanda ake mulka kuma wannan abin koyi ne. 

    Da fatan Allah ya sakawa Mai Martaba Sarki da alkhairi ya kara masa kusaci da talakawan sa, itama mai rasuwa Allah ya jikan ta, mu kuma ya kyauta namu karshen, amen.

    Kawu Sule Rano

    15-09-2021

    YADAWA Comr Baba Hamza

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.