Ticker

Mayar Da Haƙƙin Zalunci

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Na zalunci wani ne, yanzu kuma na gane kuskure na har ina son in mayar masa da haƙƙin nasa. Amma kuma idan na nuna masa hakan yana iya zama sanadin gaba a tsakaninmu. Yaya zan yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

Dayake kofar ɓarna ana son ƙanƙanta ta da rufe ta ko kulle ta ne a tsakanin musulmi, ya zama dole ka ɗauki dukkan matakan mayar masa da haƙƙinsa daidai wa daidai, kuma a cikin gaggawa ba tare da jinkiri ba.

Idan ba ka iya bayyanar masa har ya gane cewa kai ɗin ne ba, kana iya aika masa da saƙon ta hannun wanda bai san shi ba, kamar wani yaro madaidaici. Ko kuma ka ajiye masa a inda zai gani ya ɗauka shi da kansa, ba tare da wani ya gani ba shi ba.

Sannan ka haɗa saƙon da bayanin cewa: Haƙƙinsa ne da wani ya cuce shi da su a baya. Yanzu ya dawo masa da su ne yana mai tuba ga Allaah, kuma yana neman shi mai haƙƙin ya yafe masa.

Malamai sun yarda idan aka bi wannan hanyar kuma aka cigaba da roƙon Allaah gafara da yawaita ayyukan alkhairi a cikin tsawon rayuwa kafin zuwan mutuwa, hakan na iya zama sanadin samun alkhairi a lahira, in Shã Allãh.

Allaah ya ƙara mana taimako.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/EbkKRXdFzNu4F8aQZbZ1Vx

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments