𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
An ruwaito narkon azaba mai girma ga wanda baya
wankan janaba kamar yadda Allah ya nemi musulmi suyi aduk lokacin da janaba ta
same su, yazo acikin mu'ujamul dabarani al'ausad, daka Anas Yardar Allah taƙara tabbata a gareshi ya ce: Manzan Allah
salallahu Alaihi wasallam ya ce: (Abubuwa uku duk wanda ya kiyayesu toshi
waliyyin Allah ne ma'ana masoyin Allah ne, duk wanda ya tozartasu toshi makiyin
Allah ne nagaske, Sallah, da azumi, dakuma janaba).
Azzarƙani
acikin sharhin muwadda ya ce:[ Abunda ake nufi da kasancewar wanda ya tauyesu
makiyin Allah ne, shi ne Allah zai masa sakamako akai, zai tabar dashi ya
wulakan tashi, ya kaskantashi, idan afuwar Allah bata riske shiba yatuba, idan
ya tozarta tasu yana mai kore wajab cinsu, to shi kafirine, sai kiyayyar
takasance ababinta.
Wanda baya wankan janaba tahanyar mafarki ko zina
ko jima'i da matarsa, idan yana hakanne yana mai inkarin wajabcin wankan to ya
kafirta, shaikul islam ibnu taimiyya yace acikin lttafinsa jawabi ingantacce ga
wanda yacanza addinin Annabi isah.
Lallai munsani acikin musulunci salloli biyar
wajibine akan kowanne musulmi, haka tsarki daka hadasi da kuma janaba shima
wajibine, mutum ba zaiyi sallah ba sai dasu tare da iko, ba zaiyi taimama ba
idan yana da iko, duk wanda yayi inkarin wannan kafirine a ittifaƙin musulmi.
Malam shankiki ya ce: acikin littafinsa AZWA'UL
BAYAN Malamai sun haɗu akan
cewa wanda yabar sallah yana mai kore wajabcinta kafirine, kuma za'a kasheshi
amatsayin kafiri matukar bai tuba ba, abune afili barin bunda sallah bata
yiwuwa saida shi kamar barin sallar ne, haka kore wajabcinsa kamar kore tane,
Amma idan yabar wankan janaba bai kore wajabcinsa ba, kuma bai jahilci hakan
ba, toshi mai Saɓo ne
kuma ya cancanci ukuba, malamai sunyi saɓani akan kafircinsa, antambayi shaikul islam ibnu
taimiyyah Rahimahullah kamar yanda yazo amajmu'ul fatawa, shin wankan janaba
wajibine ko bawajibi bane? shin kuma yahalatta sallah da janaba batare da
ansake ba,?
Sai ya amsa dacewa: ( wankan janaba wajibine bai
halatta ga wani yayi sallah yana da janaba ko hadasi ba har sai yayi tsarki,
duk wanda yai sallah batare da tsarki ba ashari'a yana mai halatta hakan to ya
zama kafiri, wanda kuma bai halatta hakan ba anyi saɓani akan kafircinsa, zai fuskanci hukunci
mai tsanani, saidai in zai iya wanka da ruwa zaiyi wankan, inkuma bazai iya
amfani da ruwa ba yana tsoran cutuwa inyai amfani daruwan saboda wata cuta
dayake da ita ko tsoran sanyi sai yayi taimama yayi sallah ba ramuwa akansa, amafi
bayyanar zantukan malamai.
Wallahu ta'ala a'ala wa'alam
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/GUƙ2GCCzlcdL6nknƙLYYox
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.