Ticker

Mijina Ba Wani Wadata Gareshi Ba, Amma Wai Zai Kara Aure

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Miji ne da matarshi yakasance kusan komi in zasuyi suna haɗa kuɗine suyi, kamar biyan haya, kuɗin makaranta, dasauransu dai, saboda mijin ba wani wadata gareshi sosai ba matar kusan tafishi wadatan ma, yanzu yanaso yaqara aure shin wannan matar tashi zata cigaba da hidimar nan ko kuwa zata daina tunda dama haqqinshi ne ganin bashi da halin yi sosai ne take taymakawa duk da Yanzun ma gaskiya ba wadatar gareshi ba amma auren dai yakeso yaqara gaskiya. Tambaya ta anan in shi da uwargidan suka cigaba yadda sukeyi ita kuma Amaryan yaje yana yimata hidima ita rashin adalci bai shigo ba?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Toh irin wannan yana daga cikin matsalarda take damun wasu daga cikin mazaje, sekaga mutum befi karfin matsalar gidanshiba shida 'Yar matarshi guda ɗaya amma kuma sekaji ya ce ze kara aure, kuma dayawa inka bincikama zaka samu bashi sukeci suna kara auren amma ni anan banga wani lefin matarba dan ta janye tallafinda take bashi tunda dama aiba ita Allah ya daurama nauyinba shi mijin nata shine wanda aka daura masa. Toh tunda baze iya saukewaba amma kuma yanada kuɗin kara aure toh ni bana goyon bayan ace ita matar ta cigaba da bashi tallafinda take bashi, tunda har ze iya karo aure kuma ya dauki nauyin amaryar toh itama kawai taje ta cigaba da tara dukiyarda Allah yabata amma ko takalmi kada ta yarda ta siya sedai tace shi ya siya mata domin idan tacigaba dayin abunda tasaba toh karshenta nangaba sedai komai tayiwa kanta, amma dayawan mutane kara aure a haqqinsu haramunne amma saboda jahilci da karancin tunani sekuma kaga sunkara dan kawai sunaso su tonama kansu asiri. Amma lallai ni ina ganin kawai ta janye wannan tallafinda take bashi ɗin shine yafi kyau. Inkuma yacigaba da kin bata haqqinta toh se tayi kararshi wajanda yadace dan tanemi haqqinta tunda yanzu tagane cewa bawai bashi da shi bane tunda har yana iya karo aure.

Allah Yasa mudace

Jameel Al-Hassan Haruna Kabo

{ABU ZULAIHAT}

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBqfaiPwf28l

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments