Ticker

Mijina Baya Bani Hakkina Na Auratayya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, Ina so a taimaka min da shawara kuma da addu'oi da zan dunga yi. Mijina yanzu sai ya kwashi wata biyu bai kalli inda nake ba, ina nufin bai bani hakkina na aure ba. Kuma lafiyan shi lau bawata lallura ke damun shi ba. Har ya kaiga idan nayi mai magana sai yace wai gajiya ke damunsa. Na rasa inda zan saka kaina, saboda abin na mutukar damuna. Don Allah ina son wannan zauren mai albarka da ta taimakanin da abinda zanyi don magance wannan matsalar. Nagode.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikum Salam... 'Yar uwa mun karanta wasikarki acikin alhini da jimamin irin wannan yanayin da kike ciki..

Rashin samun hakkin ki na saduwar aure ba karamin bala'i bane agareki. Domin kuwa zai iya jefa ki acikin Haɗarin Zina (Allah ya Ƙara tsareki).

Sannan kuma zai chutar da lafiyarki. Domin kuwa duk lokacin da mace bata samun gamsuwa awajen Jima'i ko kuma ta rasa samun jima'in ma kwata-kwata, to maniyyinta yakan zo ya taru ne acikin Mararta. Sannan yakan haifar mata da wasu manyan matsaloli kamar ciwon mara, ciwon ciki mai tsanani, zazzabi mai zafi alokacin al'ada etc. Harma wasu lokutan da ciwukan da ba a san irinsu ba.

Muhimman shawarwarin da zan baki anan sune kamar haka:

1. Da farko dai shi addinin nan namu na musulunci bai bar komai ba sai da ya warware mana dalla-dalla. Hatta ire iren waɗannan matsaloli. Allah yana cewa acikin Suratun-Nur aya ta 35:

وَإِنْ خِفْتُمْ شِقَاقَ بَيْنِهِمَا فَابْعَثُوا حَكَمًا مِنْ أَهْلِهِ وَحَكَمًا مِنْ أَهْلِهَا إِنْ يُرِيدَا إِصْلَاحًا يُوَفِّقِ اللَّهُ بَيْنَهُمَا ۗ إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلِيمًا خَبِيرًا

"AMMA IDAN KUNA TSORON CUTARWA ATSAKANINSU (MA'AURATA)TO KU TATTARO MASU HUKUNCI DAGA CIKIN DANGIN-SA (Shi mijin) DA KUMA MASU HUKUNCI DAGA CIKIN DANGINTA (ita matar). IDAN SUKE NUFI (Acikin zukatansu) TO ALLAH ZAIDAIDAITA TSAKANINSU"

Saboda haka kinga anan kina da damar ɗaukar matakin sanar da waliyyanki halin da kike ciki. KAR KIJI KUNYA!! DOMIN KUWA ALLAH BA YA KEWAYE MA FAƊIN GASKIYA.

Yanzu idan Shaiɗan ya rinjayeki akan wannan halin da kike ciki, Kina jin mijin naki zai ji kunyar tallata ki aduniya??? (ke ma kin san ba zai ji ba).

Don haka ki sanar da waliyyanki, su kuma su sanar da waliyyansa cewar akwai wani zama da za'ayi. Idan sunzo sai akira shi maigidan naki atambayeshi: Shin gaskiya ne abinda wance take fada?? Idan ya amsa (watakil zai iya musantawa saboda kunya) sai a tambayeshi SHIN LAFIYARKA KALAU KUWA?? Idan bashi da lafiya ne sai a jinkirta masa tsawon shekara 1 yaje ya nemi magani. Idan ya warke shikenan. Idan kuma bai warke ba to ya halatta araba auren.

Idan kuma lafiyarsa kalau to sai atambayeshi dalilin da yasa yake yi miki haka.. Idan wani laifi kika yi masa, to sai abashi hakuri. Idan kuma babu wani laifi, kawai Ƙaunarki ko sha'awarki ne ba ya yi, to sai abashi Zaɓi nan take..

2. Ki cigaba da tsayawa akan tafarkin Ubangijinki tare da cikakken tsoron Allah da biyayya agareshi. Ki sani Ubangijinki zai iya jarrabarki da wannan bala'in domin ya gwada imaninki (ba wai don be sani ba).

Don haka ki kawar da kai daga duk wasu shawarwari irin na mugayen Ƙawaye.. Da sauran waɗanda ba zasu gaya miki alheri ba.

3. Ki dage da yawan ibada da nafilfilicikin dare. Ki yawaita karanta Alƙur'ani da yin tawassuli dashi domin neman yayewar wannan matsalar.

Kar ki manta da yawaita Salatun Nabiyyi domin magani ne sadidan ga kowacce damuwa.

Kar ki manta da addu'ar Annabi Yunus (as):

لاَّ إِلَـهَ إِلاَّ أَنتَ سُبْحَـنَكَ إِنِّى كُنتُ مِنَ الظَّـلِمِينَ

"LA ILAHA ILLA ANTA SUBHANAKA INNIY KUNTU MINAZ ZALIMEEN"

(Annabi yace maganin bakin ciki ce da damuwa. Kuma Allah yana amsarta da gaggawa..

4. Ki kula da tsafta da kwalliya da duk wani abinda zai ja hankalinsa. duk da dai watakila ko yana da wata matar ne bayan ke wacce take debe masa kewa, amma ya kamata yayi adalci. Domin kuwa yin adalci wajibi ne.

Mu maza ya kamata mu sanya Ƙarin jin tsoron Allah azuciyarmu. Domin kuwa irin wannan ba karamin chutarwa bane. Ka samu mata mai tsoron Allah, kana chutar da ita ahakkinta na auratayya, bayan kuwa Allah ya wajabta maka yin adalci agareta. Idan ka san ba zaka iya ba, ai gara ka sawwake. Domin kuwa Allah sai ya tambayeka akan kiwon da ya baka.

Allah ta'ala yasa mudace.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments