Ticker

Miyar Shuwaka


Miyar Shuwaka

Miyar Shuwaka

Miyar Shuwaka

Fitattun Kayan Haɗi

* Shuwaka

* Wake

* Nama/Kifi

* Kayan Miya

* Manja

* Gyaɗa

* Kayan Ɗanɗano

* Kayan Ƙamshi

* Kanwa

* Kalwa (idan mutum yana so) 

Lura: Waɗannan fitattu ne kawai daga cikin kayan haɗin. Ana iya samun sauye-sauye (daɗi ko ragi), wanda hakan ya danganta ga salo da ra'ayin mai girki.


Mataki na farko :- Za ki wanke wakenki kamar gwangwani biyu, wanki kamar alala, ki cire dusar. 


Mataki na biyu :- Ki ɗora tukunya a kan wuta, ki saka manja ko man gyaɗa.


Mataki na uku:- Ki saka jajjagen kayan miya (Attarugu, tattasai, tumatur, albasa, tafarnuwa). 


Mataki na huɗu :- Ki soya sama - sama. 


Mataki na biyar :- Ki saka ruwa daidai yadda kike son miyar. 


Mataki na shida :- Ki saka spices naki, da kayan ɗanɗano (maggi) da gishiri, thyme, curry, citta, daddawa (kalwa) 


Mataki na bakwai :- Ki dauko wannan waken da kika wanke ki saka a ciki. 


Mataki na takwas :- Ki rufe ki bari yana dahuwa a hankali a hankali. 


Mataki na tara :- Ita kuma shuwaka bayan kin cira, za ki cire dogon tsinken da ke tsakiyansa manya kawai. 


Mataki na goma:- Za ki saka a baho bayan kin gama cirewa.


Mataki na sha ɗaya:- Ki zuba masa kanwa dakakke ko wanda aka jiƙa ya kwana, da gishiri daidai. 


Mataki na sha biyu:- Za ki saka ruwa daidai ki dinga murjewa da hanunki kamar dai yadda ake wanki😅, haka za ki ta yi. (Idan kina yi za ki ga yana kumfa, idan ya yi kumfa sosai za ki canja ruwa ki sake saka wani ruwa da kanwa ki ci gaba da wankewa). 


Mataki na sha uku:- A haka za ki ga ya dena kumfa alamar ya fita ke nan, za ki iya taɓawa ki ji babu ɗacin. 


Mataki na sha huɗu :- Daga nan sai ki matse sosai. 


Mataki na sha biyar:- Sai mu koma miyarmu, ki duba waken za ki ga ya dahu sosai ya faffashe, sai ki taɓa ɗanɗanon idan komai ya yi. 


Mataki na sha shida :- Daga nan sai ki zuba gyaɗa da kika daka. 


Mataki na sha bakwai:- Sai ki saka shuwakan nan da aka wanke. 


Mataki na sha takwas :- Ki ƙauraya ya haɗe sosai, sai ki kawo kifi da aka soya ki zuba a ciki ki haɗe sosai ki rufe. 


Mataki na sha tara :- Daga nan za a bari ya dahu a hankali har sai shuwakan ya yi laushi yadda kike so. Za a ji yana ƙamshi sosai ya fitar da mai. 


Mataki na ishirin:- Daga nan sai a kashe wuta an kammala, za a iya ci da ko wani irin tuwo da ake so, yana da lafiya sosai a jiki, sannan yana da daɗi sosai. 


(Son samu amma ki fara wanke shuwaka kafin ki fara haɗa miyarki, sabida yana cin lokaci, kar miyarki ta dahu ba ki kammala wanke shi ba). 

A ci daɗi lafiya.

Miyar Shuwaka

Miyar Shuwaka

Daga:

Ummu Amatulqahhar Kitchen 
(Humaira'u)



Post a Comment

0 Comments