Mukaddima - Daga Tahamisin Wakakken Ka’idojin Rubutun Hausa

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa


Muƙaddima

Hanns Vischer, shi ne mutum na farko da ya fara shata ƙaidojin rubutun Hausar boko a farfajiyar ƙasar Hausa ta hanyar rubuta littafin da ya kira Rules for Hausa Spelling. Ya aiwatar da wannan gagarumin aiki ne a lokacin da yke riƙe da muƙamin daraktan ilmi a Nijeriya Ta Arewa. An buga littafin a shekarar 1911 a maɗaba’ar Gwamnati dake Zangeru (Government Printing Office, Zangeru).

Tsarin abjadin Vischer yana ƙunshe da haruffa 28 ne. Ya cire haruffa kamar: c, da q, da v da kum x. Ya yi bayani a kan baƙaƙe da wasulla tare da auren wasali kamar ai, da au” da wakilin suna da zagi da yadda ake samar da jam’i da lokutan aikatau.

Ya kuma bayyana cewa, kalmomin da Hausa ta aro daga harshen Larabci za a rubuta su kamar yadda ake furta su da Hausa. Sunayen Larabci kuma za a rubuta su tamkar yadda suke. Yayin da kalmomin Ingilishi, sai a fasara su zuwa Hausa. Ya kawo tsarin kalmomin da suka kamata a haɗe da waɗanda suka kamata a raba. Ya yi amfani da “ch” a madadin “c”. Ya kasa bambanta “y” da “’y”. Ya yi amfani da ɗigagga a ƙarƙashin hamzatattun baƙaƙe tamkar yadda Robinson ya yi wato , a madadin ɓɗƙ. Ya sa ɗauri a inda babu ɗauri. Misali: barra a madadin bara.

ƙaidarsa harfain r na ƙarshen kalmar nasaba da haddasau suna sajewa da harafin farko na kalmar da ke biye da shi. Misali: rigad da a madadin “rigar da” ko “fitad da” a madadin “fitar da”. Ya yi amfani da karan ɗori a sashen farko na tagwan kalmar da ake sarrafawa. Misali: ɗan-uwa da ‘yan-uwa. Ya haɗe kalmomin da ake maimaitawa a madadin ya sa karan ɗori. Misali: ‘Saƙesaƙe a madadin saƙe-saƙe.

Shi kuma Bargery sai ya kyautata ƙaidojin rubutun ta hanyar aiwatar da wasu gyare-gyare da yake hangen sun dace da harshen Hausa kamar haka:

“Ya yi watsi da harafin “ch” ya yi amfani da “c”, ya kuma yi amfani da harafin “sh” da “ts” a fagen ɗauri kuwa sai ya amfani da “ssh” da “tts” a madadin “shsh” da “tsts”. Ya yi amfani da waƙafi a gaban hamzatattun baƙaƙe a madadin ɗigagga da ake sawa a ƙarƙashin baƙaƙe. Misali: b, d, k.

Bayan shimfiɗa sahihin harsashen ginin ƙaidojin rubutun Hausar boko a farfajiyar ƙsar Hausa, Turawan mulkin mallaka sun yi ƙoƙarin kafa wasu hukumomi a cikin gida da ƙasashen waje domin kyautata ƙaidojin tare da haɓaka su. A ƙasar Turai an danƙa alhaki ne ga hukumar ƙasa da ƙsa ta nazarin harsuna da aladun Afirka (International Institute of African Languages and Cultures). Jagoran wannan hukumar shi ne farfesa Westernman wanda ya yi namijin ƙoƙarin shata wata ƙaida ta gaba ɗaya da ta shafi rubuta harsunan Afirka ciki kuwa har da harshen Hausa.

Gwamnatin Jihar Arewa ita ma ba a bar ta a baya ba, domin ta yi ƙoƙarin kafa wani kwamiti a shekarar 1932 domin samar da tabbatacciyar ƙaidar rubuta hamzatattun baƙaƙe a maimakon yi masu digagga a ƙasansu. Dr. R. M. East, wanda yake daya daga cikin yan kwamitin, shugaban ofishin fasara kuma ministan ilmi, ya tafi birnin Berlin don ya tattauna da shugaban cibiyar nazarin harsuna da al’adun afirka, game da hamzatattun harufa. A yayin wannan ziyarar ne suka cimma matsayar amfani da ƙugiya a kan haruffa kamar: b domin samar da sautin ɓ”, da harafin “d” domin samar da sautin “ɗ” da kuma harafin “k” domin samar da sautin “ƙ.

Dawowarsa ke da wuya, sai ya sanar da Gwamnatin sakamakon ziyararsa, aka aminta tare da buga alamomin sautukan a Mujallar Gwamnatin Nijeriya lamba ta 396 ta ranar 24 ga watan Maris, 1938.

R. C. Abraham, shi ne mutum na farko da ya soma amfani da waɗannan ƙaidojin alamun sautukan a ƙamusunsa mai suna Dictionary of the Hausa Language wanda London University Press, suka buga a shekarar 1946.

A cikin shekarar 1955, Gwamnatin Nijeriya ta Arewa ta kafa Hukumar Harshen Hausa domin sake daidaita ƙaidojin rubuta harshen Hausa da hafuffan Romawa (boko), an kira wannan hukumar da suna: Hausa Language Board. Hukumar ta tace kalmomin da harshen Hausa ya aro daga harsunan Larabci da Ingilishi. Ta kuma tabbatar da littafin ƙaidojin rubutun Hausa mai suna: Rules For Hausa Spelling tare da yi masa wasu gyare-gyare da suka danganci raba kalmomi da haɗe su.

Sakamakon haka ne R. M. East ya rubuta ɗan littafi ƙarami mai suna: “Hanyar Rubuta Hausa”, wanda kamfanin ɗab’i na Gaskiya da ke Zariya ya buga sai da ba a rubuta shekarar da aka buga littafin ba.

Bayan shuɗewar Turawan mulkin mallaka, an samu wasu masana daga cikin Hausawa da suka takamuhimmiyar rawa wajen ƙara daidaita ƙa’idojin rubutun Hausar boko tare da inganta shi. Sakamakon yunƙurin nasu ne ya wanzar da samuwar wallafe-wallafen littattafan ƙidojin rubutun harshen Hausa. Misali a cikin shekarar 1979, Tsangayar Ilmi ta Jamiar Ahmadu Bello da ke Zariya ta wallafa littafin ƙaidojin rubutun Hausa da aka kira: Karatu da Rubutu a Hausa: Jagoran Ƙaidojin Rubuta Hausa (A Guide To Hausa Orthography) wanda kamfanin ɗab’i na Thomas Nelso Nigeria Limited suka buga. Ba a sake samun wani littafi game da ƙaidar rubutu ba sai a shekarar 1990, lokacin da Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza ya wallafa littafi mai suna: “Nahawun Rubutu: Jagoran Ƙaidojin Rubutun Hausa. Shaihin Malamin nai tsaya nan kawai ba, domin a cikin shekarar 2002, ya wallafa wani littafi da ya raɗa wa suna: “Rubutun Hausa: Yadda Yake da Yadda Ake Yinsa”. Bayan shekaru uku sai Farfesa Bello Sa’idu ya biyo bayansa, a inda ya rubuta littafi mai take: “Ƙaidojin Rubutun Hausa: Jagora ga Marubuta, wanda aka buga a shekarar 2005. Daga nan kuma sai aka samu wani littafi mai suna: “Rubutun Hausa da Ƙaidojinsa, wanda Yakubu Musa Muhammad ya rubuta, maɗaba’ar Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta buga a shekarar 2009.

Duk kusan tsawo shekaru fiye da ɗari (100) da aka yi na gwagwarmayar daidaita ƙaidojin rubutun Hausa, ba a samu wani masani da ya yi azamar zayyana su a cikin sigar waƙa ba, sai a cikin shekarar 2004, aka samu bayyanar littafin da Shaihun Malami Aliyu Muhammadu Bunza ya rubuta mai take: Waƙaƙƙen Ƙaidojin Rubutun Hausa” ɗauke baitoci 751. Waƙar ta kasance ƙwar biyu ce kowane baiti.

Fasahar rubuta waƙa wata baiwa ce da Allah ke ba duk wanda ya so, wato ana haihuwar ɗan Adam da ita don haka sai a ga mutum yana aiwatar da waƙa a duk lokacin da ya ga dama. Haka yawan nazarin waƙoƙi kan yi tasiri ga mutum har ya ƙware tare da ƙara gogewa a fagen ƙiƙirar tare da rubuta su. 

Wani zubin kuma, naƙaltar waƙa da salailan yadda ake tsara waƙoƙi yakan wanzu ne ga mutum ta hanyar koyo sakamakon yawan karance-karancen waƙoƙi da muamula da marubuta waƙoƙi. Ba zato ba tsammani sai mutum ya tsinci kansa a fagen rubuta waƙa tasa ta kansa ko ya kasance mai yi wa waƙa tahamisi. Saboda haka, ba abin mamaki ba ne idan Malam Haruna Umar Maikwari da Abu-Ubaida Sani aka ga un yi wa waƙa tahamisi, musamman idan aka yi laakari da yadda suka shaƙu da marubucin waƙar ta asali. Hasali ma Hausawa na cewa; “Barewa ba ta haihuwa ɗanta ya yi rairahe””. A wani ƙaulin sukan ce: zama da maɗaukin kanwa shi ke sa farin kai”. Babu ko tamtama zaman su da Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza da yadda suka shaƙu da shi ya yi tasiri ƙwarai da gaske wajen aiwatar da wannan tahamisin. Babu shakka sun yi namijin ƙoƙari musamman idan aka yi laakari da yadda suka tsara ƙaramin amsa-amon kowane baiti kamar yadda ya kasance a baitocin waƙar ta asali, tare da fayyace wasu ƙa’idoji da misalai. Allah ya saka masu da kyakkyawan sakamako a nan duniya da gobe ƙiyama. Ya kuma ba malamai da ɗaliban Hausa damar amfana da wannan aiki, amin.

Dr. Adamu Rabi’u Bakura
Department of Languages and Cultures
Federal University, Gusau
Zamfara State, Nigeria

Get a copy:

Haruna Umar Maikwari
Call or WhatsApp: 07031280554

Abu-Ubaida Sani
WhatsApp: +2348133529736
Email: abuubaidasani5@gmail.com



Post a Comment

0 Comments