Na Goya Yarona Ina Sallah Da Kashi A Pampers Ɗinsa,Yaya Hukuncin Sallata?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum. Malam Na goya yarona, to pampers ɗin jikinsa da fitsari ko kashi, shin zan iya sallah da shi a bayan ko sai na sauke shi?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam. Ƴar uwa abin da ya kamata ki riqa lura da shi shi ne, matuqar kashin nan ko fitsarin nan ya fito wajen pampers ɗin, to ki cire masa ki wanke masa, sannan ki goya shi ki yi sallar da shi.

    Amma matuqar kashin nan ko fitsarin bai fito wajen pampers ɗin ba, to hukuncinsa kamar hukuncin kashi da fitsarin da ke cikin mutum ne, wato kenan za ki iya goya shi ki yi sallah da shi, saboda akwai mushaqqa idan aka ce kowane lokaci sai kin aje yaron nan idan za ki yi sallah saboda matsalar pampers, wani lokacin ma idan kika aje shi wata qil idan ya sa rigima sallar ma ba za ta yiwu maki ba.

    Duba Fataawal Lajnatid Dá'ima (1/237). Almajmu'a ta biyu.

    Allah ne mafi sani.

    Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/DIcJIQrWyLP0oBOMSnDi5P

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.